"Ana Shan Wuya": Jigo a PDP Ya Fadi Yaudarar da Ake Yi Wa Shugaba Tinubu
- Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya yi magana kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu
- Dele Momodu ya bayyana cewa ƴan Najeriya na shan wahala a ƙarƙashin mulkin mai girma Shugaba Tinubu
- Jigon na PDP ya nuna cewa Tinubu na iya ɗaukar cewa sauya sheƙar da ƴan siyasa ke yi zuwa APC, alamu ne na cewa yana yin daidai a mulkinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya bayyana cewa ƴan Najeriya har yanzu na ci gaba da wahala a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Dele Momodu ya bayyana cewa Tinubu na iya fahimtar abubuwa a baibaye kan sauya sheƙar da ƴan siyasa ke yi zuwa jam'iyyar APC.

Source: Facebook
Dele Momodu ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Soni Irabor Live na tashar News Central Tv a ranar Asabar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya yi karatun ta natsu, ya gano matsalar da ya kamata a magance a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me jigon PDP ya ce kan Tinubu?
Jigon na PDP ya bayyana cewa ƴan Najeriya na shan wahala a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Tinubu.
"Amma duk inda ka juya a Najeriya, mutane na kuka. Ban taɓa ganin irin wannan matakin baƙin ciki da ƙuncin rayuwa ba. Ina fatan shugaban ƙasa yana karɓar sukar da ake yi masa da zuciya ɗaya."
“Ina fatan ana gaya masa halin da ake ciki a ƙasar nan, domin babu yadda zai iya jin ko sanin abin da ke faruwa idan ba a faɗa masa ba. Shi wanda abin ya shafa ne kaɗai ke jin daɗi ko zafinsa."
- Dele Momodu
Ya bayyana shakku kan ko shugaban ƙasa na da cikakken sani game da matsalolin da jama’a ke fuskanta, inda ya ce yawan sauya sheƙa daga jam’iyyun adawa zuwa APC na iya ba shugaban ƙasa ra’ayin cewa abubuwa na tafiya daidai.
"Ba na tsammanin shugaban ƙasa yana da cikakken fahimta kan abubuwan da ke faruwa. Domin idan ka ga gwamnoni da dama na sauya sheƙa zuwa jam’iyyarka, ba za ka ɗauka cewa kai ne mafi girma a tarihin Najeriya ba?
“Ba za ka iya ganin laifin mutum ba idan yana jin hakan."
- Dele Momodu

Source: Facebook
Dele Momodu ya koka kan sauya sheƙa
Dele Momodu ya yi ƙorafin cewa an jefar da kundin tsarin mulkin Najeriya, inda ya ce ya kamata ƴan siyasa da ke yawan sauya jam’iyya su shirya rasa muƙamansu.
"Ka sani cewa mun jefar da kundin tsarin mulkinmu tun da daɗewa cikin Tekun Atlantika. An watsar da shi, kuma hakan abin takaici ne."
“Kundin tsarin mulki ya bayyana cewa idan wani da aka zaɓa a ƙarƙashin wata jam’iyya ya yanke shawarar sauya sheƙa, to dole ne ya ajiye muƙamin da yake kai."
- Dele Momodu
Tinubu ya magantu kan rashin tsaro
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yarda cewa ƙasar nan na fama da ƙalubalen rashin tsaro.
Tinubu ya bayyana cewa dole ne a magance matsalar rashin tsaro idan ana son a jawo masu zuba hannun jari zuwa ƙasar nan.
Shugaban ƙasan ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ganin cewa ta kawo ƙarshen masu tayar da ƙayar baya a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng

