Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna, an Samu Nasara kan Miyagu

Dakarun Sojoji Sun Yi Wa 'Yan Bindiga Kwanton Bauna, an Samu Nasara kan Miyagu

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan miyagun ƴan bindiga a jihar Taraba da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Sojojin sun samu nasarar ne bayan sun yi wa ƴan bindigan kwanton a ƙaramar hukumar Ussa ta jihar
  • A yayin artabun da aka yi, an kashe ɗan bindiga ɗaya yayin da sauran suka ranta a na kare zuwa cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun runduna ta shida ta sojojin Najeriya sun hallaka wani ɗan bindiga a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun kuma ƙwato makami da babur a yayin wani samame na musamman da suka gudanar a ƙaramar hukumar Ussa da ke jihar Taraba.

Sojoji sun fatattaki 'yan bindiga a Taraba
Dakarun sojoji sun hallaka dan bindiga a Taraba Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankim Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a c

Sojoji sun ragargaji ƴan bindiga

Majiyoyin sirri sun bayyana cewa farmakin wanda aka gudanar a ƙarƙashin Operation Lafiyan Jama’a, ya biyo bayan sahihin bayanan sirri da suka nuna motsin wasu ƴan ta’adda a yankin Fikyu na ƙaramar hukumar Ussa.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan ISWAP sun farmaki sansanin sojoji, an samu asarar rayuka

Majiyoyin sun bayyana cewa dakarun sun samu nasarar yin kwanton ɓaunan ne a daren Asabar da misalin ƙarfe 9:00 na dare a ƙauyen Gafar.

“A cikin wannan farmakin, dakarun sun ƙaddamar da kwanton ɓauna a wasu wuraren da aka gano ƴan bindiga ke bi a wannan yanki."
"Da misalin ƙarfe 9:00 na dare, dakarun sun hango wasu ƴan bindiga suna matsowa kusa da ƙauyen Gafar da yiwuwar shirin kai hari."

- Wata majiya

Majiyar ta ƙara da cewa dakarun sun yi gaggawar buɗe wuta a kan ƴan ta’addan nan take, inda suka kashe ɗaya daga cikinsu yayin da sauran suka tsere cikin daji.

Dakarun sojoji sun ƙwato kayayyaki

Bayan haka, dakarun sun ci gaba da sintiri a yankin, inda suka samu nasarar ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da kuma wani babur da aka sace daga wani mutumin garin da suka kai wa hari a baya.

Dukkan kayan da aka ƙwato suna hannun dakarun domin ci gaba da bincike da ɗaukar matakan doka.

Sojoji sun kashe dan bindiga a Taraba
Dakarun sojoji sun kwato babur a hannun 'yan bindiga a Taraba Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewar majiyoyin tsaro, wannan aiki ya kasance wani ɓangare na ƙoƙarin da rundunar ke yi domin daƙile hare-haren ƴan bindiga da kuma kare rayukan jama’a a jihar Taraba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai munanan hare hare a Sokoto, an samu asarar rayuka

Rundunar ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da gudanar da irin waɗannan ayyuka don tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu ƙauyuka guda uku na ƙananan hukumomin Gwadabawa da Sabon Birni.

A yayin hare-haren da ƴan bindigan suka kai a ƙauyukan, sun hallaka mutane 11 waɗanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Ƴan bindigan dai sun yi gungu ne kan babura lokacin da suka kai hare-hare a ƙauyukan cikin dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng