"Ƴan Bindiga Sun Shiga Uku": Abin da Tinubu Ya Faɗa kan Matsalar Tsaro a Katsina

"Ƴan Bindiga Sun Shiga Uku": Abin da Tinubu Ya Faɗa kan Matsalar Tsaro a Katsina

  • Mai girma shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci dakarun sojojin Najeriya su zage damtse, su gama da ƴan ta'addan da suka addabi jama'a
  • Bola Tinubu ya yi wannan roƙo ne da ya kai wa dakarun sojin 17 Brigade da ke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Katsina
  • Ya ce matsalar tsaron da ƙasar nan ke fama da ita jarabawa ce kuma yana da ƙwarin gwuiwar sojoji sun shirya dawo da zaman lafiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Katsina - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bukaci dakarun sojojin Najeriya da su ƙara zage damtse wajen kawo ƙarshen ta’addanci, ‘yan bindiga da ‘yan tawaye da ke addabar al'umma.

Shugaba Tinubu ya yi wannan kira ne a ranar Juma’a yayin da ya kai ziyara ga dakarun 17 Brigade na Sojojin Najeriya da ke Katsina.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samo mafita ga gwamnonin Najeriya kan masu sukarsu

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya buƙaci sojoji su kawo karshen matsalar tsaro Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ziyarci sojojin ne a wani ɓangare na ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar Katsina daga ranar Juma'a, 2 ga watan Mayu, 2025.

Gwamna Dikko Raɗɗa da mafi yawan gwamnonin Arewa na cikin tawagar da ta tarbi shugaban ƙasar.

Tinubu ya bukaci sojoji su zage damtse

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa lokaci ya yi da za a kawo ƙarshen duk wani nau'i na ta'addanci, ayyukan ƴan bindiga, garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.

Ya buƙaci dakarun sojojin su tashi tsaye, su yi amfani da gogewarsu wajen tabbatar da tsaron al'umma da dukiyoyinsu.

Shugaban ya bayyana cewa lamarin tsaro da ƙasar ke fuskanta babbar jarabawa ce a tarihin ƙasar, yana mai bukatar sojoji su zage damtse wajen kare ƙasar da dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda Rarara ya cashe da sabuwar waƙa a liyafar da aka shiryawa Tinubu a Katsina

Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya ce lokaci ya yi da zaman lafiya zai dawo a Najeriya Hoto: Ibrahim Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Abin da Tinubu ya ce kan matsalar tsaro

“Sojojinmu, ku sani wannan lokaci ne na jarabawa a tarihinmu. Barazana irin ta ta’addanci da ‘yan bindiga sun shafe tsawon lokaci suna damun mu.
"Yanzu lokaci ya yi da za mu ce ya ishe su. Ƴan Najeriya sun amince da mu, sun ganin ni da ku zami iya kawo ƙarshen matsalolin tsaro mu kwato kowane ɓangare na ƙasar nan."
“Ina so ku amsa mani da ƙarfi: Shin kun shirya? Shin kuna da kwarin guiwar kawo ƙarshen wannan matsala ta tsaro gaba ɗayanta?"
"Ina so muryar saƙonku ta karade dazuka da duwatsu, ku shaida wa makiyan Najeriya cewa lokaci ya kure musu.”

- In ji Shugaba Tinubu.

Gwamnati za ta iya dawo da tsaro a Najeriya?

A wani labarin, kun ji cewa Tsohon ministan tsaro, Janar T. Y. Danjuma (mai ritaya) ya ce gwamnati kaɗai ba za ta iya warware matsalar tsaron Najeriya ba.

Kara karanta wannan

"Karyarku ta sha Karya," Tinubu ya ɗauki zafi kan masu yunkurin tarwatsa Najeriya

Ya jaddada muhimmancin shiri don kare kai, yana mai cewa hakan wajibi ne duba da yadda rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a faɗin ƙasar nan.

Ɗanjuma ya ce yawaitar kashe-kashen jama'a a jihohin Benuwe, Filato da wasu sassan ƙasar nan, sun sake tabbatar da kiran da ya yi tun da daɗewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: