Hakeem Baba Ahmed Ya Dura kan Buhari bayan Ajiye Mukami a Gwamnatin Tinubu

Hakeem Baba Ahmed Ya Dura kan Buhari bayan Ajiye Mukami a Gwamnatin Tinubu

  • Tsohon mai ba mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, shawara kan siyasa, Hakeem Baba-Ahmed ya soki Muhammadu Buhari
  • Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa tsohon shugaban ƙasan ya fi damuwa da kujerarsa fiye da sauke nauyin da aka ɗora masa
  • A wata hira da aka yi da shi, dattijon ya nuna gwamnatin Muhammadu Buhari ita ce mafi muni da aka taɓa yi a tarihin ƙasar nan
  • Tsohon mai ba da shawarar ya bayyana cewa sun koma sukar Buhari a fili ne bayan sun ba shi shawarwari a sirrance bai ɗauka ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hakeem Baba-Ahmed, tsohon mai ba mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, shawara kan harkokin siyasa, ya caccaki Muhammadu Buhari.

Hakeem Baba-Ahmed ya ce tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya fi mayar da hankali kan kujerarsa fiye da gudanar da mulki da gaskiya.

Kara karanta wannan

Buhari da tsofaffin ministoci na shirin ficewa daga APC kafin 2027? Gwamna Sule ya yi magana

Hakeem Baba-Ahmed ya soki Muhammadu Buhari
Hakeem Baba Ahmed ya caccaki gwamnatin Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari, Hakeem Baba-Ahmed
Source: Facebook

Tsohon mai ba Kashim Shettima shawarar ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Politics Today' na Channels Tv a ranar Alhamis, 1 ga watan Mayun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Hakeem Baba-Ahmed ya ce kan Buhari?

Hakeem Baba-Ahmed mai shekaru kimanin 70ya bayyana cewa mulkin Buhari shi ne mafi muni da ya gani a tarihin Najeriya.

“Buhari bai wakilci Arewa ba. Mun ga Buhari a matsayin mafi dacewa a lokacin, ba don cewa ɗan Arewa ba ne ba, amma saboda a lokacin ya fi Goodluck Jonathan."
“Mun yi zaton zai yi tsauri wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, kuma zai haɗa kan ƙasa, saboda Jonathan bai ɗauki Boko Haram da muhimmanci ba. Amma daga ƙarshe sai ya zama akasin haka."

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem ya ce Buhari bai ɗaukar shawara

A yayin da ake tambayarsa ko mulkin Buhari ne mafi muni a tarihin Najeriya, Baba-Ahmed ya amsa da cewa haka batun yake.

Kara karanta wannan

Hakeem Baba Ahmed ya fadi abin da ya sani kan alakar Tinubu da Shettima a Villa

Hakeem Baba-Ahmed
Hakeem Baba Ahmed ya yi kalamai masu kaushi kan Buhari Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: UGC
“Ban ga wata gwamnati da ta fi ta Buhari muni ba, daga kwarewata, ina da shekaru 70. Ban ga gwamnati da ta gaza wajen shugabanci, ta fi nuna rashin kulawa ga talakawa, ko ta kasa wajen maida hankali kan abin da ta sanya a gaba."
“Na kasance cikin masu goyon bayansa a lokacin yaƙin neman zaɓe. Na jagoranci jam’iyyarsa a jihata na tsawon shekara huɗu."
"Amma cikin watanni bayan hawansa mulki, sai muka fahimci cewa ya fi damuwa da zama shugaban ƙasa fiye da gudanar da mulki."
“Mun fara da ba shi shawara a sirrance, daga bisani muka koma yin suka a fili lokacin da ya bayyana a fili cewa ba zai saurara ba.”

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem Baba-Ahmed ya magantu kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba mataimakin shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

"Akwai matsala," Hakeem Baba Ahmed ya ƙara fallasa abin da ya gani a Gwamnatin Tinubu

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa ko kaɗan bai yi nadamar karɓar muƙanin da ya yi ba a gwamnatin Shugaba Tinubu.

Sai dai, duk da hakan ya bayyana cewa bisa yadda gwamnatin Tinubu ta ke tafiyar da al'amuranta, ba zai ƙara yin aiki a ƙarƙashinta ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng