Gwamna Dauda Ya Tsage Gaskiya kan Halin da Ya Tarar da Zamfara bayan Matawalle
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya koka kan tarin matsalolin da ya gada wajen magabacinsa, Bello Matawalle
- Dauda Lawal ya bayyana cewa N4m kawai aka bar masa a asusun jihar, sai kuma tarin basussuka na biliyoyin naira
- Gwamnan ya nuna cewa hakan ne ya sanya ya duƙufa wajen aiki tuƙuru domin warware matsalolin da ya tarar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana matsaloli da ci gaban da gwamnatinsa ta fuskanta tun bayan da ya hau kan karagar mulki.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ya gaji ɗumbin basussuka daga wajen gwamnatin Bello Matawalle.

Asali: Twitter
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da tashar Arise TV a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dauda Lawal ya ce ya gaji matsaloli a Zamfara
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa lokacin da ya karɓi mulki daga tsohon gwamna Bello Matawalle, jihar Zamfara tana cikin matsaloli ta kowanne fanni.
Ya bayyana cewa rashin tsaro ya yi katutu, tsarin ilimi ya rushe, ɓangaren kiwon lafiya mara kyau, da kuma ɗumbin basussuka da aka biyo jihar.
“Lokacin da na karɓi mulki a matsayin gwamna, jihar Zamfara tana cikin wani yanayi mai matuƙar muni a kowanne ɓangare na rayuwa, matsalar tsaro ta kai ƙololuwa, ilmi ya yi ƙasa, kiwon lafiya ya taɓarɓare."
“Babu ko ɗigon ruwa guda a jihar Zamfara na tsawon watanni biyar kafin na hau mulki, amma mun samu damar warware wannan matsala cikin kwana uku kacal."
"Gaskiya bashin da aka bari ba abin yarda ba ne, amma a matsayin shugaba, dole ne na nemo mafita domin gyara lamarin,”
- Dauda Lawal
Gwamna Dauda ya faɗi basussukan da ya gada
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana irin basussukan kuɗi da ya gada lokacin da ya hau mulki, da kuma yadda ya biya albashin ma’aikata da fansho da sauran basussuka.

Asali: Facebook
"Lokacin da na hau mulki, ba komai a cikin baitul-mali na jihar. Na gaji bashi mai yawa, Naira miliyan huɗu ne kacal na tarar."
"Dukkan bayanan suna nan, bashin albashin ma’aikata na tsawon watanni huɗu da rabi, bashin ɓangaren shari’a na naira biliyan 1.6, WAEC Naira biliyan 1.6, NECO Naira biliyan 1.4, da sauran ƙalubale masu yawa."
"Abu na farko da na fara yi shi ne biyan bashin albashi. Na nemi yarjejeniya da WAEC da NECO domin yaranmu su samu su zauna jarrabawa, kuma ba kawai jarrabawar ba, har da samun shaidar kammala karatu da suka rubuta a baya amma suka kasa karɓa saboda rashin biyan kuɗi."
"Lokacin da na hau mulki, albashin ma’aikacin gwamnati a jihar Zamfara N7,000 ne kacal, N7,000 a faɗin jihar, matakin jiha da ƙananan hukumomi. Dole ne na gaggauta ƙara shi zuwa mafi ƙarancin albashi na N30,000.”
“Ba haka kawai ba, tun daga shekarar 2011, ba a biyan tsofaffin ma’aikata fanshonsu ba, har bashin ya kai Naira biliyan 16.5, wanda Alhamdulillah na samu na biya su baki ɗaya a watan da ya gabata."
"Duk wani ma’aikaci daga 2011, an biya masa fansho, kuma yanzu muna biyan albashi mafi ƙaranci na N70,000.”
- Gwamna Dauda Lawal
Matawalle ya yi wa ƴan APC kyauta
A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya gwangwaje mambobin jam'iyyar APC a jihar Zamfara.
Tsohon gwamnan na jihar Zamfara ya raba shanu ga mambobin na APC domin su yi bukukuwan ƙaramar Sallah cikin walwala.
Bello Matawalle ya bayyana cewa rabon shanun da ya yi, na daga cikon abin da ya saba yi domin kyautatawa al'umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng