Boko Haram: Sanata Ndume Ya Fadi Barnar da 'Yan Ta'adda Suka Yi a Borno
- Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume ya gayawa duniya irin ɓarnar da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi a jihar
- Ali Ndume ya bayyana cewa a cikin watanni shida ƴan Boko Haram sun kai hare-hare guda 252 kan jama'a a jihar Borno
- Sanatan ya buƙaci gwaamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen samar da kayan aiki ga jami'an tsaro domin shawo kan matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya bayyana irin ɓarnar da ƴan ta'addan Boko Haram suka yi a Borno.
Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa mayaƙan Boko Haram sun ƙwace ƙananan hukumomi uku a jihar Borno sakamakon sake dawowar hare-haren da suke kaiwa a yankin Arewa maso Gabas.

Asali: UGC
Ndume ya bayyana ɓarnar da Boko Haram ta yi a Borno
Jaridar Daily Trust ta ce Sanata Ndume ya bayyana hakan yayin wata hira da ƴan jarida a Abuja a ƙarshen mako.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa al’ummar jihar Borno sun fuskanci hare-hare guda 252 tun daga watan Nuwamba zuwa yanzu.
Sanatan ya bayyana cewa a cikin wannan lokaci, sojoji 100 da fararen hula sama da 200 ne suka mutu, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda kashe-kashen Boko Haram ke sake dawowa duk da ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen shawo kan matsalar.
Ndume ya ce sake dawowar rikicin a jihar Borno ne ya sa Sanatoci uku na jihar, Gwamna Babagana Zulum da wasu ƴan majalisar wakilai suka gana da shugabannin tsaro domin nemo mafita kan hare-haren ƴan ta'addan.
Sanata Ali Ndume ya koka kan Boko Haram
“Mun damu matuƙa domin daga watan Nuwamban bara zuwa yanzu, an kai hare-hare 252 a jihar Borno. A cikin watanni shida, sama da sojoji 100 aka kashe. Sama da fararen hula 200 suka rasa rayukansu."
“Duk da cewa rundunar sojojin Najeriya na bakin ƙoƙarinta, sun kashe sama da ƴan ta’adda 800 a jihar Borno. Boko Haram da ISWAP sun fiye da mutum 500 a tsakaninsu saboda faɗan da suke yi da juna."
"Yanzu haka da nake magana da ku, ƙananan hukumomi guda uku, Gudumbari, Marte da Abadama a hannun Boko Haram suke. Wannan shi ne maganar gaskiya."
- Sanata Ali Ndume
Sanata Ndume ya ba Tinubu shawara

Asali: Twitter
Sanata Ndume ya kuma buƙaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-ɓaci kan harkar tsaro.
Ali Ndume ya buƙaci gwamnatin tarayya da ka da ta bari ƴan ta’addan su sake kwace yankunan da aka ƙwato a jihar Borno, tare da buƙatar a samar wa sojoji isassun kayan aiki domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Zulum ya caccaki minista kan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi kalamai masu zafi kan ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris.
Gwamna Zulum ya bayyana cewa ministan bai san abin da yake faruwa a ƙasar nan ba, bayan ya yi wasu kalamai kan matsalar rashin tsaro a Borno.
Zulum ya buƙaci ministan da ya maida hankali kan aikinsa maimakon yin magana kan abubuwan da bai da masaniya a kansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng