Dakatar da Fubara: Mata Sun Cika Tituna a Rivers Suna Zanga Zanga

Dakatar da Fubara: Mata Sun Cika Tituna a Rivers Suna Zanga Zanga

  • Wasu mata a Jihar Rivers sun gudanar da zanga-zangar lumana domin goyon bayan dokar ta-baci da Bola Tinubu ya ayyana a jihar a watan Maris
  • Wannan ne karon farko da aka samu gangamin goyon bayan wannan mataki, inda matan suka soki Simi Fubara tare da neman a tabbatar da zaman lafiya
  • Rahotanni sun nuna cewa matan sun bayyana cewa tun bayan ayyana dokar ta-baci, jihar ta samu sauƙin rashin tsaro da rage ayyukan ‘yan ta’adda

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Wasu mata daga sassa daban-daban na Jihar Rivers sun fito kwansu da kwarkwatansu ranar Litinin a babban birnin jihar, Port Harcourt, suna zanga zanga.

Matan suna zanga zanga ne domin nuna goyon bayansu ga dokar ta-baci da gwamnatin tarayya ta ayyana a jihar tun ranar 18 ga watan Maris, 2025.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun sake tabargaza a Filato, sun kashe mutane kusan 50

Fubara
Mata sun goyi bayan dakatar da Fubara yayin zanga zanga a Rivers. Hoto: Hoto: @PH_Socials
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta wallafa cewa wannan ne karon farko da aka samu irin gangamin domin goyon bayan dakatar da Fubara a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar tare da dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, mataimakiyarsa Farfesa Ngozi Odu da kuma majalisar dokokin jihar.

Daga bisani, an naɗa tsohon shugaban rundunar sojan ruwa, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), a matsayin mai kula da harkokin jihar.

Mata sun fito zanga zanga a jihar Rivers

Matan sun yi zanga-zangar lumana, sanye da tufafi farare, kuma suka riƙe alluna masu ɗauke da rubuce-rubuce kamar: “Mun yarda da dokar ta-baci,” “Ba mu goyon bayan Fubara,” da sauransu.

Gangamin ya biyo bayan wata zanga-zanga da wasu mata masu biyayya ga Gwamna Fubara suka gudanar a baya ƙarƙashin ƙungiyar RWUS.

Ɗaya daga cikin masu shirya zanga-zangar, kuma tsohuwar mataimakiyar shugabar ƙaramar hukumar Etche, Hon. Gladys Nweke ta yi hira da 'yan jarida.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Tinubu ya kunyata masoya, ya hana fara yi masa Kamfen a dukkan jihohi

Hon. Gladys Nweke ta bayyana cewa zanga-zangar tasu na goyon bayan zaman lafiya ne da nufin marawa gwamnatin tarayya baya kan sanya dokar ta baci a jihar.

Mata su ce an samu zaman lafiya a Rivers

Da take magana da manema labarai, Gladys Nweke ta ce zaman lafiya ya samu a jihar tun bayan matakin da Bola Tinubu ya dauka.

“Abin da muke yi a nan shi ne zanga-zangar goyon baya ga dokar ta-baci da aka ayyana a Jihar Rivers.
“Tun da aka ayyana dokar ta-baci a jihar, mun samu zaman lafiya. Ba mu ƙara jin labarin kashe-kashe ko ayyukan ‘yan daba ba kamar da.”

Rahoton Channels TV ya nuna cewa sun nemi al’ummar jihar da su ci gaba da mara wa gwamnatin tarayya baya domin tabbatar da zaman lafiya da cigaban Jihar Rivers.

Fubara
Mata masu zanga zanga sun goyi bayan datakar da Fubara a Rivers. Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Instagram

Tompolo ya ce za a dawo da Simi Fubara

Kara karanta wannan

Bayan Atiku ya gana da Buhari, an karfafawa Uba Sani, Tinubu guiwa a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa abokin ministan Abuja da aka fi sani da Tompolo ya ce ana shirin mayar da gwamna Simi Fubara.

Legit ta rahoto cewa Tompolo ya yi maganar ne a wani taro da aka shirya domin cikarsa shekaru 54 a duniya.

Baya ga haka, ya bayyana cewa ba zai yarda da duk wani abu da ake tunanin zai kawo koma baya ga 'yan asalin yankin Neja Delta ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng