'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, Sun Tafka Barna Mai Yawa

'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, Sun Tafka Barna Mai Yawa

  • Ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyukam jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Miyagun ƴan bindigan sun farmaki ƙauyen Tabkin Maza inda suka hallaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutane masu yawa
  • Tsagerun sun kuma kai wani harin a ƙaramar hukumar Tsafe inda suka ƙona gidajen mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai munanan hare-haren ta'addanci a wasu ƙauyuka biyu da ke jihar Zamfara.

Ƴan bindigan a yayin hare-haren da sukai kai a lokuta daban-daban, sun hallaka mutum ɗaya tare da yin awon gaba da wasu mutane masu yawa.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun bude wuta kan jami'an tsaro, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara

Majiyoyin sirri sun bayyana cewa harin farko da ƴan bindigan suka kai ya auku ne a ranar Juma'a, 11 ga watan Afirilu, 2025, da misalin ƙarfe 11:00 na dare.

Ƴan bindigan a yayin harin sun kutsa cikin ƙauyen Tabkin Maza da ke yankin Nassarawa a ƙaramar hukumar Bakura.

Miyagun ƴan bindigan sun harbe wani mutum har lahira kafin su yi awon gaba da wasu mutane da ba a bayyana yawansu ba.

Jami’an ƴan sanda sun garzaya zuwa wurin da lamarin ya faru, kuma an miƙa gawar mamacin ga ƴan uwansa domin yi masa jana’iza.

Harin na biyu ya faru ne a ranar 12 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 6:40 na yamma, a lokacin da ƴan bindigan suka kai hari a ƙauyen Tsageru da ke ƙaramar hukumar Tsafe.

A yayin harin, sun harbi mutum ɗaya inda suka raunata shi, sannan suka ƙona gidaje da dama.

Kara karanta wannan

Ana jimamin kisan kusan mutum 50, an sake sabon ta'addanci a Plateau

An garzaya da mutumin da ƴan bindigan suka ji wa rauni zuwa asibiti domin kula da lafiyarsa.

Dakarun sojoji
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Sojoji sun ɗauki mataki

A matsayin martani ga waɗannan hare-hare, dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yamma da ke sansani a Tsafe sun ƙara zafafa sintirinsu da ayyukan bincike domin cafke waɗanda suka kai harin.

Ƴan bindiga dai sun daɗe suna cin karensu babu babbaka a jihar Zamfara, inda suka kai hare-hare kan bayin Allah.

Ƴan bindiga sun farmaki jami'an NSCDC

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari kan jami'an tsaro na hukumar NSCDC a jihar Bayelsa.

Ƴan bindigan sun farmaki jami'an tsaron ne a ƙaramar hukumar Southern Ijaw ta jihar, yayin da suke dawowa daga wani samame da suka kai.

Harin da ƴan bindigan suka kai ya jawo wani jami'in NSCDC ya rasa ransa yayin da aka raunata wasu jami'ai bayan an yi musayar wuta.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun samu gagarumar nasara kan 'yan bindiga a Katsina

Yankin da ƴan bindigan suka farmaki jami'an tsaron dai ya yi ƙaurin suna wajen haƙar mai ba bisa ƙa'ida ba da ayyukan masu fasa bututun mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng