'Yan Bindiga Sun Bude Wuta kan Jami'an Tsaro, an Samu Asarar Rayuka
- Wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai farmaki kan jami'an tsaro na hukumar NSCDC a jihar Bayelsa
- Ƴan bindigan sun farmaki jami'an tsaron ne a ranar Juma'a inda suka hallaka mutum ɗaya tare da lalata wasu da dama
- Kakakin hukumar NSCDC a jihar Bayelsa ya tabbatar da aukuwar lamarin, wanda ya auku a ƙauyen Igbomotoru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Wasu da ake zargin ƴan bindiga ne sun kai hari kan tawagar sintiri ta hukumar tsaron NSCDC a ƙauyen Igbomotoru, cikin ƙaramar hukumar Southern Ijaw ta jihar Bayelsa.
Ƴan bindigan waɗanda suka kai harin a ranar Juma'a, sun kashe wani jami’in hukumar da har yanzu ba a tantance sunansa ba.

Asali: Twitter
Wani mazaunin yankin ya tabbatarwa da jaridar Daily Trust aukuwar lamarin kai harin da ƴan bindiga suka yi a kan jami'an tsaron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka farmaki jami'an NSCDC
Ya bayyana cewa tawagar ta NSCDC tana kan hanyar dawowa ne daga wani samame da suka kai kan wuraren haƙar mai ba bisa ƙa'ida ba a yankin lokacin da harin ya auku.
Yankin Igbomotoru ya yi ƙaurin suna wajen haƙar mai ba bisa ƙa'ida ba saboda kasancewarsa wajen da ke da yawan rafuka.
Wasu majiyoyi sun bayyana harin a matsayin wani shiri na tsanaki da wasu ƴan bindiga suka yi, inda suka buɗe wuta kan jirgin ruwa na sintirin NSCDC a kusa da Koluama, wanda aka daɗe ana saninsa a matsayin cibiyar satar mai.
Ana kyautata zaton harin yana da nasaba da masu lalata bututun mai, waɗanda suka yi amfani da muggan makamai don korar jami’an tsaro.
An ce jami’in da aka kashe, an harbe shi ne a lokacin musayar wuta, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa, yayin da sauran jami’an da suka jikkata ake ba su kulawa a wani asibiti da ke birnin Yenagoa.
Me hukumar NSCDC ta ce kan harin?

Asali: Twitter
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun NSCDC na jihar Bayelsa, Solomon Ogbere, a ranar Lahadi, ya bayyana cewa har yanzu bai samu cikakken rahoto kan abin da ya faru ba.
"Eh da gaske ne mun samu rahoton faruwar lamarin, amma har yanzu ina jiran OC ya bani cikakken bayani. Amma abin da kuka faɗa akwai gaskiya a cikinsa, sai dai ba zan iya faɗin komai yanzu ba saboda ban samu cikakkun bayanai ba."
"Amma Insha Allahu gobe (Litinin) zan faɗi komai kan abinda ya faru, adadin waɗanda suka rasa rayuka da sauran bayanai."
"To amma dai wani abu makamancin haka ya faru, sai dai har yanzu ban samu cikakken rahoto a kansa ba."
- Solomon Ogbere
Ƴan bindiga sin farmaki ɗaliban jami'a
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu yan bondiga sun kai hari kan ɗaliban jami'ar tarayya ta Birnin Kebbi (FUBK).
Ƴan bindigan waɗanda ba a san ko su waye ba sun kai harin ne a wani gidan haya da ke wajen harabar jami'ar.
A yayin harin, ƴan bindigan sun yi awon gaba da wani ɗalibi mai suna Stephen Madubiya zuwa cikin daji.
Asali: Legit.ng