Masarautar Zazzau Ta Yi Rashi, Danmajen Arewa Ya Yi Bankwana da Duniya
- Masarautar Zazzau da ke jihar Kaduna ta bayyana rasuwar Danmajen Arewa, Injiniya Hayyatu Mustapha, daya daga cikin fitattun masu sarautar birnin
- Sanarwar da masarautar ta fitar a shafinta na Facebook ta tabbatar da cewa marigayin ya rasu ne a yammacin Asabar, 12 ga Afrilu, 2025
- Haka kuma sanarwar ta ce za a gudanar da sallar jana’izar Injiniya Hayyatu Mustapha a ranar Lahadi, 13 ga Afrilu, a unguwar Mangawaron Babajo
- Ana sa ran sallar jana’izar za ta fara ne da karfe 2:30 na rana a kofar gidan Asusu, inda ake rokon Allah ya jikansa da rahama
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Zaria, Kaduna - Masarautar Zazzau a jihar Kaduna ta sanar da rasuwar daya daga cikin manyan masu sarauta a birnin.
An tabbatar da rasuwar Danmajen Arewan Zazzau, Injiniya Hayyatu Mustapha a ranar Asabar 12 ga watan Afrilun 2025.

Kara karanta wannan
Yan sanda sun yi ƙarin haske bayan kama wasu mafarauta 4 daga Kano da makamai a Edo

Source: Facebook
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa shafin Zazzau Emirate ya wallafa a manhajar Facebook da safiyar yau Lahadi 13 ga watan Afrilun 2025.
Sarkin Yakin Zazzau ya riga mu gidan gaskiya
A farkon watan Janairun 2025, Masarautar Zazzau ta yi rashin Sarkin yaki wanda aka shiga alhini sosai duba da girman marigayin a fada.
Alhaji Rilwanu Yahaya Pate, Sarkin Yakin Zazzau, ya rasu a ranar Alhamis, 30 Janairu, 2025 ana tsaka da taro a wani asibiti.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi jana'izar marigayin a gidansa dake Rimin Doko, Unguwar Kaura, a Birnin Zaria, tare da gudanar da sallah a misalin karfe 5:00.
Majiyar Legit Hausa ta tabbatar da cewa ai Martaba Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli ya fito domin a sallaci marigayin.

Source: Facebook
An sanar da lokacin sallar jana'izar marigayin
Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne a yammacin jiya Asabar 12 ga watan Afrilun 2025 da muke ciki.
Har ila yau, sanarwar ta tabbatar da cewa za a yi sallar jana'zar marigayin a yau Lahadi 13 ga watan Afrilun 2025.
Sanarwar ta ce:
"Bisa yardar Allah za a gabatar da jana'izar marigayi Danmajen Arewan Zazzau, Injniya Hayyatu Mustapha.
"Za a gabatar sallar jana'izarsa a yau Lahadi 13 ga watan Afrilun 2025 a Mangawaron Babajo da ke kofar gidan Asusu.
"Sallar za ta gudana ne da misalin karfe 2:30 na rana, da fatan Allah ya jikansa da ramaharsa, Ameen."
Shugaban gudanarwa a Izalah ya rasu
Kun ji cewa an shiga jimami a jihar Adamawa bayan rasuwar Alhaji Muhammad Aliyu Kaka, daya daga cikin manyan shugabannin Izalah na reshen Jos.
Kungiyar JIBWIS reshen jihar Gombe ce ta tabbatar da rasuwar shugaban a wani rubutu da ta wallafa a shafin Facebook a daren ranar Asabar.
Marigayin ya rike mukamin shugaban gudanarwa na JIBWIS a Adamawa kafin rasuwarsa, kuma yana da karbuwa sosai a tsakanin mabiyansa.
Rahotanni sun tabbatar an gudanar da sallar jana'izarsa a masallacin Izalah na Gate 2 da misalin karfe 11:00 na safe, kamar yadda sanarwa ta bayyana.
Asali: Legit.ng
