Boko Haram: Gwamna Zulum Ya Yi Wa Ministan Tinubu Martani Mai Zafi
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya taɓo batun kalaman sa ministan yaɗa labarai ya yi kan matsalar tsaro a jihar
- Farfesa Babagana Umara Zulum ya bayyana ministan bai san abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan ba
- Zulum ya nuna cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da haɗa kai da hukumomin tsaro domin shawo kan matsalar ƴan ta'addan Boko Haram
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya yi martani ga ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, kan matsalar Boko Haram.
Gwamna Zulum ya mayar da martanin ne bayan wani rahoto ya nuna cewa Mohammed Idris, ya yi watsi da damuwar da ya bayyana kwanan nan dangane da matsalar tsaro a jihar.

Asali: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ce Gwamna Zulum ya mayar da martanin ne yayin wata hira da manema labarai.

Kara karanta wannan
'Ka gwada zuwa Borno ka gani': Jigon APC ya kalubalanci ministan Tinubu kan Boko Haram
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A baya, Gwamna Zulum ya bayyana cewa Boko Haram ta sake farfaɗo da hare-hare da garkuwa da mutane a jihar, kuma babu isasshen martani daga jami’an tsaro.
Sai dai kuma wani rahoto ya bayyana cewa ministan ya yi watsi da zancen Gwamnan. Zargin da ministan ya fito ya ƙaryata, inda ya bayyana rahoton a matsayin ƙarya da sauya masa kalamansa.
Wane martani Gwamna Zulum ya yi?
Gwamna Zulum a yayin hira da ƴan jaridar, ya ce ministan yaɗa labarai bai san me ke faruwa a ƙasar nan ba.
“Ba na son yin cacar baki da ministan yaɗa labarai. Ina ganin bai fahimci me ke faruwa a cikin ƙasar nan ba. Bai san yadda abubuwa ke gudana ba."
“Abin da muka tattauna a zaman majalisar tsaro ba abu ba ne mara kyau ba. Mun dai bayyana damuwa ne kan yadda ayyukan Boko Haram ke sake dawowa a jihar Borno."

Kara karanta wannan
"Zan ba gwamna mamaki," Sanata Nwoko ya yi ƙarin haske kan jihar da ake shirin ƙirƙirowa
"Kuma akwai buƙatar gwamnatin jihar Borno, sojoji da sauran hukumomin tsaro su haɗa kai don daƙile wannan barazana. Ina ganin wannan faɗakarwa ce mai kyau. Babu wani abu da muka ce fiye da haka."
- Farfesa Babagana Umara Zulum
Zulum ya faɗi ƙoƙarin da yake kan rashin tsaro

Asali: Facebook
Gwamna Zulum ya ƙara da cewa:
"Abu mafi muhimmanci, ina tabbatar muku da cewa mun je Abuja, mun gana da manyan hafsoshin tsaro, musamman CDS, hafsan sojojin ƙasa, hafsan sojojin ruwa da kuma hafsan sojojin sama."
“Mun samu tabbaci daga gare su cewa za su yi duk mai yiwuwa domin shawo kan halin da ake ciki."
"Muna matuƙar jin daɗin irin martanin da muka samu daga shugabannin tsaro, kuma gwamnatin jihar Borno za ta ci gaba da haɗa kai da rundunar sojojin Najeriya da kuma gwamnatin tarayya domin rage barazanar ƴan ta’addan."
Sanatan Borno ya caccaki ministan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Borno ta Tsakiya, Kaka Shehu Lawan, ya yi wa ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris, kan rashin tsaro a Borno.

Kara karanta wannan
"Na yi wa Allah alƙawari," Gwamna Alia ya yi magana da aka fara raɗe raɗin zai bar APC
Sanata Kaka ya bayyana cewa kalaman da ministan ya yi kan Gwamna Babagana Umara Zulum cin mutunci ne da rashin girmamawa a gare shi.
Ya ƙalubalanci ministan da ya ziyarci birnin Maiduguri domin ya ji da kunnensa daga wajen masu kula da harkokin tsaro kan abubuwan da ke faruwa.
Asali: Legit.ng