Sanata Ndume Ya Yi Fallasa, Ya Fadi Korafin Jiga Jigan APC kan Tinubu

Sanata Ndume Ya Yi Fallasa, Ya Fadi Korafin Jiga Jigan APC kan Tinubu

  • Sanata Ali Ndume na jam'iyyar APC ya nuna rashin gamsuwarsa kan salon mulkin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewa Tinubu ya watsar da manyan jiga-jigan APC
  • Sanatan ya nuna damuwa kan cewa na kusa da Tinubu na sukar duk wanda ya fito ya faɗi gaskiya kan gwamnatinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu, Ali Ndume, ya bayyana damuwar da wasu manyan jiga-jigan APC ke da ita kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa yawancin manyan jiga-jigan jam’iyya APC na jin cewa an mayar da su saniyar ware a ƙarƙashin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Sanata Ndume ya soki Tinubu
Sanata Ndume ya ce ya watsar da jiga-jigan APC Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Senator Mohammed Ali Ndume
Asali: Facebook

Sanata Ndume ya faɗi hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin ‘Politics Today’ na tashar Channels Television a ranar Juma’a, 12 ga watan Afirilun 2025.

Kara karanta wannan

Sanata Ndume na shirin ficewa daga APC ya haɗe da El Rufai a SDP? Ya yi bayani da bakinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ali Ndume ya faɗi ƙorafin ƴan APC kan Tinubu

Ali Ndume ya bayyana takaicinsa kan abin da ya kira rashin ɓa da dama ga manyan ƴan jam'iyya domin su yi tattaunawa tsakaninsu da shugaban ƙasa

Sanata Ali Ndume ya ba da misali da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufai wanda ya fice daga jam'iyyar APC zuwa SDP.

“Kimanin shekaru biyu da kafuwar wannan gwamnati, mutane da dama na jin kamar an yi watsi da su. Kamar El-Rufai, ya bayar da hujja cewa APC ta watsar da shi, haka nan da dama daga cikin sauran jiga-jigan jam’iyyar."

- Sanata Ali Ndume

Ali Ndume
Sanata Ndume ya soki Bola Tinubu Hoto: Senator Mohammed Ali Ndume
Asali: Twitter

Sanata Ndume ya ƙara nuna damuwa kan yadda gwamnatin Tinubu ke nuna halin ko-in-kula da ƙorafe-ƙorafen da masu biyayya ga jam’iyyar ke yi, yana mai cewa:

“Mutane da dama ba su da wata hanyar samun kusanci da gwamnati. Na taɓa faɗa a baya, amma babu wani abu da ya yi game da hakan."

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa," Sanata Ndume ya yi magana kan haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027

"Maimakon su saurari saƙon, sai su fito a jaridu suna zagin wanda ya kawo saƙon, maimakon su duba gaskiyar abin da ake faɗa."

Idan ba a manta ba dai Sanata Ndume a wata hira da aka yi da shi a ranar Litinin ya zargi shugaban ƙasa da nuna bangaranci wajen naɗa muƙamai.

Jawabin Ndume ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan batun haɗin kai, daidaito a cikin jam’iyyar APC, da kuma hanyoyin tafiyar da gwamnati ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu.

Ndume ya magantu kan shirin komawa SDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a majalisar dattawa, Ali Ndume, ya yi magana kan yiwuwar ficewa daga jam'iyyar APC zuwa SDP.

Sanata Ali Ndume ya bayyana cewa ko kaɗan ba shi da shirin barin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya zuwa wata jam'iyya.

Ali Ndume ya nuna cewa zai ci gaba da zama a jam'iyyar APC duk kuwa da yawan sukar gwamnatin Bola Tinubu da yake yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng