Bayan Sallar Juma'a, Wani Abu da Ake Zaton 'Bam' ne Ya Tarwatse a Shagon Ɗaukar Hoto

Bayan Sallar Juma'a, Wani Abu da Ake Zaton 'Bam' ne Ya Tarwatse a Shagon Ɗaukar Hoto

  • Wani abu da ake zargin bam ne ya tarwatse a shagon ɗaukar hoto da yammacin ranar Juma'a, 11 ga watan Afrilu, 2025 a jihar Legas
  • An ruwaito cewa akalla mutane biyar ne suka jikkata ciki har da mace bayan wuta ta kama a shagon sakamakon fashewar
  • Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa jami'an sashen kwance bam sun kewaye wurin kuma sun fara bincike kan abin da ya faru

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Rahotanni daga jihar Legas na cewa mutane da dama sun jikkata yayin da wani abin fashewa ya tarwatse da yammacin Juma’a a wani shagon daukar hoto da ke titin Kodesoh, yankin Ikeja.

Shaidun gani da ido sun ce fashewar ta afku ne bayan wani ma’aikacin shagon ya bude wani kunshin saƙo sa aka kawo, wanda suke shakku a kansa.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Jihar Legas.
Mutum 5 sun jikkata da wani abu ya fashe a shagon ɗaukar hoto a Legad Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Leadership ta tattaro cewa tuni jami'an agaji da suka haɗa da ƴan sanda, jami'an sashen kwance bam, da jami'an hukumar LASTMA suka kewaye wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda abin fashewar ya tashi a shago

Wani ganau mai suna Lucky Okoro ya bayyana cewa:

"Lamarin ya faru da kusan karfe shida na yamma ne, ina dab da shiga shagon sai abin fashewar ya tashi. Na sa kafa na kan gangaren shiga shagon kenan, fashewar ta cilla ni baya.
"Ban tsaya komai ba, na tsere daga wurin amma dai mum hangi wuta ta kama wata mata da wani namiji da ke cikin shagon."

Mutane nawa fashewar ta yi wa illa?

Jaridar The Cable ta tattaro cewa akalla mutane biyar ne suka samu raunuka kuma tuni aka garzaya da su asibitin koyarwa na jami'ar jihar Legas (LASUTH) domin kula da lafiyarsu.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da cewa jami’an sashem kwance bam sun killace wurin domin gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

An fara mantawa: Lauya ya taso da maganar kisan Hausawa a Edo da tambayoyi 10

"Masu bincike daga sashen kwance bam (EOD) na rundunar ƴan sanda sun tsabtace wurin don tabbatar da lafiyar mazauna yankin tare da bincike mai zurfi don gano ainihin musabbabin fashewar," inji Hundeyin.
Yan sanda.
Kwamishinan yan sandan Legas ya kai ziyara shagon da lamarin ya faru Hoto: @PoliceNG
Asali: Getty Images

Kwamishinan ƴan sanda ya ziyarci wurin

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Legas, CP Olohundare Jimoh, ya isa wurin da lamarin ya faru don ganin halin da ake ciki da idanunsa.

Ya kuma tabbatar wa jama’a cewa rundunar ƴan sanda na kan lamarin, za ta gano abin da ya haddasa fashewar.

Kakakin ƴan sandan ya kara da cewa:

"CP ya bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum tare da tabbatar da cewa babu dalilin firgita."

A halin yanzu ƴan sanda sun sun fara bincike don gano musabbabin fashewar, yayin da ake ci gaba da kula da wadanda suka jikkata a asibiti.

Ƴan sanda sun fara bincike kan harin ofishin LP

Kara karanta wannan

Gwamnan Filato ya fayyace komai, an ji yawan garuruwan da 'yan ta'adda suka mamaye

A wani labarin, kun ji cewa wasu tsageru sun kai hari ofishin jam'iyyar LP na jihar Legas, sun tafka ɓarna tare da sace kayayyaki.

An tattaro cewa kimanin mutum 300 suka farma ofishin da safiyar Litinin, suka tafka satar mai yawa kuma suka tsere kafin zuwan ‘yan sanda.

Sai dai rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa an fara bincike domin gano wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel