Kungiyar Izalah Ta Yi Rashi da Shugabanta Ya Yi Bankwana da Duniya a Adamawa

Kungiyar Izalah Ta Yi Rashi da Shugabanta Ya Yi Bankwana da Duniya a Adamawa

  • An shiga jimami a jihar Adamawa bayan rasuwar Alhaji Muhammad Aliyu Kaka, daya daga cikin manyan shugabannin Izalah na reshen Jos
  • Kungiyar JIBWIS reshen jihar Gombe ce ta tabbatar da rasuwar shugaban a wani rubutu da ta wallafa a shafin Facebook a daren ranar Asabar
  • Marigayin ya rike mukamin shugaban gudanarwa na JIBWIS a Adamawa kafin rasuwarsa, kuma yana da karbuwa sosai a tsakanin mabiyansa
  • Rahotanni sun tabbatar da za a gudanar da sallar jana'izarsa a masallacin Izalah na Gate 2 da misalin karfe 11:00 na safe, kamar yadda sanarwa ta bayyana

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - An shiga jimami a jihar Adamawa bayan rashin daya daga cikin shugabannin kungiyar Izalah.

An sanar da rasuwar shugabvan gudanarwa na kungiyar JIBWIS da ke da hedikwata a Jos, Alhaji Muhammad Aliyu Kaka.

Kara karanta wannan

Buhari ya yi wa Sheikh Pantami wasa da dariya da ya ziyarce shi a Kaduna

Kungiyar Izalah ta yi rashi a Adamawa
Shugaban gudanarwa a ƙungiyar Izalah ya rasu a Adamawa. Hoto: JIBWIS Gombe State.
Asali: Facebook

Shafin kungiyar reshen jihar Gombe ne ya tabbatar da rasuwar marigayin a Facebook a daren ranar Asabar 12 ga watan Afrilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Izalah ta maye gurbin marigayi Jingir

A wani labarin da Legit Hausa ta kawo cewa kungiyar Izalah ta nada wasu mukamai ciki har da wanda zai mayen gurbin marigayi Sheikh Sa'id Hassan Jingir.

Majalisar Malaman Izala ta tabbatar da Sheikh Dalhatu Abubakar Hakimi a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai na ƙasa II.

Shugaban majalisar, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ya kafa kwamiti domin cike gibin da marigayi Sheikh Saidu Hassan Jingir ya bari.

Kungiyar ta fitar da bayani kan kwamitocin fatawa, zakka da kuma harkokin matasa domin inganta tafiyar addinin Musulunci a faɗin Najeriya.

Izala ta yi babban rashin shugaba a jihar Adamawa
Kungiyar Izalah ta sanar da rasuwar shugaban gudanarwarta a Adamawa. Hoto: JIBWIS Nigeria.
Asali: Facebook

An fadi lokacin sallar jana'izar marigayi, Kaka

Sanarwar ta ce marigayin kafin rasuwarsa shi ke rike da mukamin gudanarwa na kungiyar reshen jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufa'i, Pantami da manyan 'yan adawa sun gana da Buhari a Kaduna

Har ila yau, an tabbatar da cewa za a yi sallar jana'izar marigayin da misalin karfe 11:00 na safe a masallacin Juma'a na kungiyar da ke 'Gate 2'.

Sanarwar ta ce:

"Innalilillahi wa innailaihiraji’un'
"Allah ya yi wa shugaban gudanarwa na kungiyar JIBWIS mai hedikwata a Jos reshen jihar Adamawa, Alhaji Muhammad Aliyu Kaka.
"Allah ya gafarta masa kura-kuransa, ya karbi ayyukan alherinsa, Ubangiji ya jikansa da rahama.
"Za a yi sallar jana’iza ranar Asabar da karfe 11:00 na safe idan Allah ya yarda a masallacin Izalah na Gate 2."

Mutane da dama sun yi jimamin rasuwar marigayin inda suka kwatanta shi a matsayin jajirtaccen dattijo da ya ba da gudunmawa.

'Dan majalisa ya rasu a jihar Zamfara

Kun ji cewa dan majalisar da ke wakiltar Kaura Namoda ta Kudu a jihar Zamfara, Hon. Aminu Ibrahim Kasuwar Daji ya riga mu gidan gaskiya.

Sanata Yau Sahabi daga Zamfara ya nuna alhini kan rasuwar dan majalisar dokokin jihar inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai biyayya da jajircewa.

A cewar Sanata Sahabi, Aminu Kasuwar Daji mutum ne da tawali’u da gaskiya suka mamaye rayuwarsa, inda hakan ya zama abin koyi ga mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.