Obasanjo Ya Tabo Batun Talauci a Najeriya, Ya Fadi inda Matsalar Take

Obasanjo Ya Tabo Batun Talauci a Najeriya, Ya Fadi inda Matsalar Take

  • Tsohon shugaban ƙasa a mulkin soja da farar hula, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan talaucin da ya addabi ƴan Najeriya
  • Obasanjo ya bayyana cewa bai kamata ƴan Najeriya su kasance cikin talauci ba duba da irin ɗumbin albarkatun da ƙasar take da su ba
  • Dattijon ya nuna cewa matsalar talaucin da ake fama da ita ta ta'allaƙa ne da yadda ake tafiyar da tulin albarkatun ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Abia - Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa babu dalilin da ya sa ƴan Najeriya za su kasance cikin talauci.

Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa bai kamata ƴan Najeriya su zauna cikin talauci ba duba da irin albarkatu da arziƙin da Allah ya horewa ƙasar.

Olusegun Obasanjo
Obasanjo ya ce bai kamata a yi talauci a Najeriya ba Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Obasanjo ya bayyana hakan ne a taron wata liyafa da gwamnatin jihar Abia ta shirya a daren ranar Juma’a, a gidan gwamnati da ke Umuahia, domin girmamawa gare shi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa," Sanata Ndume ya yi magana kan haɗakar Atiku, Obi da El Rufai a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce Najeriya ƙasa ce mai yalwar albarkatu, amma matsalar ta ta’allaka ne kan yadda ake tafiyar da waɗannan albarkatu cikin sakaci da rashin gaskiya.

"Ƴan Najeriya ba su da wani dalilin kasancewa cikin talauci, domin Allah ya ba mu duk abin da muke buƙata."
"Idan mu na tafiyar da abin da Allah ya ba mu cikin sakaci, to ba zamu ɗorawa Allah laifi ba, mu da kanmu ne muke da laifi."

- Olusegun Obasanjo

Obasanjo ya yabi gwamnan Abia

Tsohon shugaban ƙasar ya yaba da ƙoƙarin Gwamna Alex Otti na jihar Abia wajen canza tsarin mulki da inganta rayuwar al’umma, yana mai jaddada cewa ana yabawa salon mulkinsa a faɗin ƙasar.

Ya tabbatar da cewa gwamnan na yin tasiri wajen tafiyar da mulki a jiharsa, kuma ya buƙaci ya ci gaba da ƙoƙari da jajircewa don jin daɗin jama’a.

"Idan da muna da gwamnonin da suka kai 18 waɗanda ke gudanar da shugabanci nagari kamar yadda ake gani a Abia, da mun gina ƙasa mai ƙarfi kuma mai cike da ci gaba."

Kara karanta wannan

Duk da hare haren Boko Haram, gwamnati za ta shigar da tubabbun 'yan ta'adda cikin al'umma

Ya sake jaddada damuwarsa game da halin da ƴan Najeriya ke ciki da kuma ingancin shugabancin da suke samu daga shugabanni.

"A gare ni, ko ka gan ni ka ƙi gaishe ni, ko na gaida ka ka ƙi amsawa, abin da ya fi damuna shi ne ganin al’ummar wannan ƙasa suna samun abin da ya dace da su, wanda shi ne shugabanci nagari."

- Olusegun Obasanjo

Gwamna Otti ya nuna godiyarsa ga Obasanjo

Alex Otti
Gwamna Alex Otti ya godewa Obasanjo Hoto: @alexcotti
Asali: Twitter

A jawabinsa, Gwamna Alex Otti ya gode wa tsohon shugaban ƙasan bisa goyon bayan da ya ba shi tun kafin ya samu nasarar zama gwamna.

"A matsayina na shugaba, nasarar da aka samu a yau ba ta zo da sauƙi ba. Akwai ƙalubale da dama da na fuskanta a cikin shekaru da dama da nake fafutuka a siyasa, amma hangen nesa da juriya ne suka sa aka kai ga nasara."

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fara sauye-sauye da dama musamman a ɓangaren ilimi, don tabbatar da cewa kowane ɗan jihar Abia yana da damar samun ilimi mai inganci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta ɗauki sababbin ma'aikata a faɗin Najeriya, an fitar da sanarwa

Shi ma ya ba da ta shi gudunmawar

Kabir Hussaini ya shaidawa Legit Hausa kalaman da tsohon shugaban ƙasan ya yi gaskiya, amma shi ma ya ba da irin ta shi gudunmawar.

"Abin mamaki ne Obasanjo ya zo yana irin waɗannan kalaman domin shi ma yana daga cikin shugabannin da suka yi watanda da dukiyar ƙasar nan."
"Tabbas gaskiya ya faɗa bai kamata a ce ana talauci a Najeriya ba, amma shi ma ya taimaka wajen halin da mutane suka samu kansu a cikin ƙasar nan na fatara."

- Kabir Hussaini

Obasanjo ya koka da sarakunan yau

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya nuna damuwa kan irin sarakunan da ake naɗawa.

Obasanjo ya bayyana cewa ana naɗa ƴan ta'adda da mutane marasa tarbiyya a matsayin sarakunan da za su jagoranci al'umma.

Obasanjo ya bayyana cewa hakan ba ƙaramar illa yake yi ba ga sarautun gargajiya masu daɗaɗɗen tarihi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel