Bayan Atiku da El Rufa'i, Ganduje Ya Dura Gidan Buhari da Jiga Jigan APC

Bayan Atiku da El Rufa'i, Ganduje Ya Dura Gidan Buhari da Jiga Jigan APC

  • Shugaban APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya jagoranci tawagar jiga-jigan jam’iyyar zuwa gidan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Ziyarar ta biyo bayan zuwan shugabannin jam’iyyun adawa PDP da SDP da suka hada da Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa'i
  • Kafin haka, Abdullahi Ganduje da wasu manyan jam’iyyar sun kai wa Gwamna Dikko Umaru Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa a jihar Katsina

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Tawagar jiga-jigan APC ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ta kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Ziyarar ta zo ne bayan shugabannin jam’iyyun adawa na PDP da SDP sun ziyarci Muhammadu Buhari a garin Kaduna.

Buhari
Tawagar APC ta ziyarci Buhari a Kaduna. Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Legit ta gano yadda shugabannin APC suka ziyarci Buhari ne a cikin wani sako da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Atiku, El Rufai, Malami da sauran manyan ƴan adawa da suka ziyarci Buhari a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kafin nan kuma, tawagar APC ta sauka a jihar Katsina inda ta kai gaisuwar ta’aziyya ga Gwamnan jihar, Malam Dikko Umaru Radda, bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u.

Ganduje da 'yan APC sun ziyarci Buhari

Shugaban APC na ƙasa, Ganduje, ya jagoranci tawagar manyan 'yan jam’iyyar zuwa Kaduna domin gaisawa da tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Ziyarar na nufin ƙarfafa haɗin kai da ɗorewar kusanci tsakanin shugabanin jam’iyya da tsohon shugaban, wanda har yanzu yana da tasiri a harkokin jam’iyyar da siyasa a Najeriya.

Ziyarar ta nuna cewa APC na ƙoƙarin tabbatar da cewa Buhari yana da cikakken kulawa da haɗin kai da shugabannin jam’iyya bayan saukarsa daga mulki.

A 'yan kwanakin nan, manyan 'yan siyasa na kai ziyara zuwa gidan Muhammadu Buhari da ke Kaduna, wanda hakan ke jawo martani iri iri a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Atiku da El Rufa'i raddi mai zafi a gidan Buhari kan zaben 2027

Buhari
Atiku da 'yan adawa sun ziyarci Buhari ranar Juma'a. Hoto: PAul O Ibe
Asali: Twitter

Tawagar APC ta ziyarci Dikko Radda a Katsina

Tun kafin ziyartar Kaduna, Ganduje da sauran manyan jam’iyyar APC sun sauka a jihar Katsina domin kai gaisuwar ta’aziyya ga Gwamna Radda bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Safara’u.

A cewar Ganduje:

“Mun zo ne domin nuna alhini a madadin jam’iyya bisa wannan babban rashi, kuma mun riga mun yi addu’o’i a ƙasa mai tsarki domin samun rahamar Allah gareta.”

Mataimakin Gwamnan Katsina, Faruk Lawal Jobe, wanda ya karɓi bakuncin tawagar a madadin Gwamna, ya gode wa jam’iyyar bisa ziyarar ta’aziyya.

Ya jaddada cewa zuwan shugabannin APC ya ƙara musu ƙwarin gwiwa, tare da yi musu fatan alheri a tafiyarsu.

Sheikh Pantami ya ziyarci Buhari a Kaduna

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarci Shugaba Muhammadu Buhari a gidan shi na Kaduna a ranar Juma'a, 11 ga Afrilu.

Kara karanta wannan

El Rufai ya yi magana, ya faɗi dalilin zuwan Atiku da manyan jiga jigai wurin Buhari

Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarci Buhari ne tare da tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami domin mika gaisuwar sallah ga tsohon shugaban kasar.

Tsohon ministan ya bayyana yadda Muhammadu Buhari ya masa raha da cewa ya murmure yayin da suka yi hira a kebance.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng