Faɗin Gaskiya Ya Yi Rana: Gwamma Ya Naɗa Mata 2 Masu Ɗauke HIV a Muƙamai na Musamman

Faɗin Gaskiya Ya Yi Rana: Gwamma Ya Naɗa Mata 2 Masu Ɗauke HIV a Muƙamai na Musamman

  • Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya naɗa wasu mata biyu a muƙamai na musamnan saboda faɗin gaskiya kan cutar HIV da suke ɗauke da ita
  • Agbu Kefas ya bayyana hakan ne a lokacin da uwar gidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyara jihar Taraba
  • Ya roki matar shugaban kasa da ta lallaɓa mijinta ya kara turo tallafin kuɗi Taraba, yana mai tabbatar da cewa zai yi aikin da ya dace da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Taraba - Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya naɗa wasu mata biyu da suka fito bainar jama'a suka bayyana cewa suna ɗauke da cutar ƙanjamau watau HIV

Agbu Kefas ya ce gwamnatinsa za ta bai wa matan su biyu aiki na musamman bayan sun tabbatar da cewa suna farin ciki duk da suna ɗauke da cutar tsawon shekaru 10.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu za ta ɗauki sababbin ma'aikata a faɗin Najeriya, an fitar da sanarwa

Gwamna Kefas na Taraba
Gwamnan Taraba ya nada mata 2 masu HIV a muƙamai na musamman Hoto: Agbu Kefas
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta tattaro cewa gwamnan ya naɗa matan a muƙamai na musamnan domin jinjina masu bisa iya faɗin gaskiya a cikin jama'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar Tinubu ta kai ziyara Taraba

Agbu Kefas ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, yayin ziyarar aiki ta kwanaki biyu da matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta kai garin Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Sanata Oluremi Tinubu ta kai ziyarar ne domin kaddamar da rabon kayan aikin jinya ga Ma’aikatan jinya 10,000 a yankin Arewa maso Gabas.

Matar shugaban ƙasar ta kuma tallata shirin yaki da cututtuka uku ciki har da cutar kanjamau watau HIV da ciwon hanta a tsakanin mata masu haihuwa.

Yadda matan suka burge Gwamna Kefas

A wajen taron, wasu mata biyu daga cikin daruruwan da suka halarta suka yanke shawarar bayyana irin kalubalen da suka fuskanta tsawon shekaru suna rayuwa da cutar HIV.

Mata biyun sun bayyana yadda suka sha wahala saboda kaskanci da wariya daga al’umma, daga maza har da mata, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: Hedkwatar tsaro ta fito da bayanin yadda aka ceto Janar Tsiga

Da yake jawabi, Gwamna Kefas ya bukaci matar shugaban kasa da ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya kara turo da kudaden tallafi zuwa Taraba.

Gwamnan ya kuma tabbatar wa uwar gidan shugaban ƙasa cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da kuɗin yadda ya kamata.

Gwamna Kefas.
Mata 2 masu HIV sun samu muƙami a gwamnatin Taraba Hoto: Agbu Kefas
Asali: Facebook

Wane mukamai gwamnan ya naɗa matan?

Ya kuma sanar da cewa, daga wannan rana, za a nada wadannan mata biyu a matsayin Masu Ba Da Shawara Na Musamman a ofishin matar gwamna, inda ya ce:

"Bayan wannna taron, ku je ofishin matar gwamna domin karbar takardun nadin ku. Wannan nadin ba wai kawai sakamako ne na gaskiyar da kuka bayyana ba, karramawa ce bisa jarumtarku.”

Gwamna Kefas ya kara da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da duk wani tallafi da Taraba ta samu wajen gina rayuwar al’umma, musamman mabukata.

Gwamnan Taraba na shirin gyara ilimi

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Taraba, Agbu Kefas, ya bayyana aniyarsa ta aiwatar da gyaran ilimi da zai ba 'yan jihar damar samun ingantaccen ilimi mai rahusa.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

Ya ce ilimi shi ne tushen ci gaban gwamnatinsa, kuma hakan ya sa ya ayyana ilimi kyauta da tilasta shi a matakin firamare da sakandare.

Agbu Kefas ya yi wannan bayani ne a wurin taron bikin yaye dalibai a Kwalejin Ilimi ta Zing da aka gudanar a ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262