An Samu Bayanai bayan Zargin Kwangilar Makarantu da Ɗan Bello Ya Yi ga Bala Lau
- Mai kamfanin Fal-Damno a Taraba, Alhaji Ali Bukar Lau ya bayyana cewa kamfaninsa ne ya yi aikin kwangilar da ake zargin Bala Lau da shi
- Alhaji Lau ya ce ya kafa kamfanin Fal-Damno tun shekarar 1998, kuma babu wata alaka tsakanin Sheikh Lau da wannan kamfani ko aikin kwangilar
- Ya bayyana takaicinsa kan yadda ake bata sunan mutane ba tare da bincike ba, yana tunanin daukar matakin shari’a kan wannan zargi da ke yawo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sardauna, Taraba - Wani mamallakin kamfanin Fal-Damno ya yi magana kan zargin da ake yiwa Sheikh Bala Lau na kwangila.
Mutumin mai suna Alhaji Ali Bukar Lau ya ce kamfanin da ake magana na shi ne ba na Sheikh Abdullahi Bala Lau ba.

Asali: Facebook
Bala Lau: An samu bayanai kan zargin Ɗan Bello

Kara karanta wannan
Bayan fara tambayoyi, Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo da aka hallaka Hausawa
Wannan na kunshe a cikin wani bidiyo da shafin Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin faifan bidiyon, Ali Bukar Lau ya ce abin takaici ne yadda aka tsara karyar ba tare da bincike ba.
Ya ce:
"Assalamu Alaikum, ni dai sunana Alhaji Ali Bukar Lau da ke zama a Jalingo, wannan magana da ake na kwangila kamfanina ne, lallai mu muka yi aikin, kuma Fal-Damno na wane ni Alhali Ali Bukar Lau.
"Sannan na yi rijistar kamfanin Fal-Damno a 1998 wanda yanzu ya kai shekaru 27 kenan, tun wancan lokacin na ke amfani da shi har zuwa yau."
Ya ce abin mamaki ne zargin inda ya tabbatar da cewa sun yi aikin har kuma sun kammala ba tare da matsala ba.
A cewarsa:
"Hakika ni na yi wannan aiki a kan iyaka kuma mun yi aiki har mun gama, muna da takardu na kamfani da na kammala aiki.
"Wanann shaida ce da za ta nuna wannan kamfani ba na Sheikh Bala Lau ba ne, ni ne mai kamfani.

Asali: Facebook
Menene gaskiyar mallakar kamfani na Bala Lau?
Alhaji Bukar Lau ya ce Sheikh Bala Lau ba shi da alaka kwata-kwata da kamfanin Fal-Damno kamar yadda ake fada.
Ya kara da cewa:
"A fahimta na, mun shiga wani irin yanayi duk lokacin da mutum ya kai wani matsayi sai ka ga ana ta haddada da shi.
"Ka ga yanzu wannan kunya za a ji, naga bidiyo an ce kamfanin Bala Lau ne, na yi mamakin wannan abu har ga Allah.
"Idan har za su yi irin wannan abu ya kamata su yi bincike saboda wannan kamfani dai ba na Bala Lau ba ne.
"Ba daidai ba ne mutane ma su daraja irin malamai a zo ana bata musu suna, ina jan hankalin yara irinsu Ɗan Bello masu ƙananan shekaru da za su iya yiwa ƙasa amfani su guji irin haka."
Mai kamfanin ya ce har yanzu yana ta tunanin wani mataki zai ɗauka saboda an bata musu suna.
Izalah za ta maka Dan Bello a kotu
Kun ji cewa Kungiyar Izala ta ce za ta gurfanar da Dan Bello a kotu kan zarge-zargen da ya yi wa shugabanta, Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Kungiyar ta musanta cewa ta karɓi kuɗi daga gwamnatin tarayya domin gina ajujuwa, tana mai cewa ayyukan wasu ‘yan majalisa ne.
Izala ta ce Dan Bello ya yi sharrin da ke da nufin ɓata sunan shugabanta da ƙungiyar, don haka za ta bi hakkinta ta hanyar shari’a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng