Shehu Sani Ya Yi wa Buhari Raddi kan Maganar 'Satar' Kudin Gwamnati

Shehu Sani Ya Yi wa Buhari Raddi kan Maganar 'Satar' Kudin Gwamnati

  • Muhammadu Buhari ya ce ya bar mulki ba tare da tara dukiyar da ba shi da ita kafin hawa karaga, yana nufin bai saci kuɗin gwamnati ba
  • Shehu Sani ya ce Allah ne kawai ya san gaskiyar maganar Buhari, amma ya fi dacewa a duba halin da talakawa suka shiga bayan mulkinsa
  • Ya kuma bayyana cewa abin da ya fi jan hankali shi ne ko jama’ar da suka wahala domin ganin Buhari ya hau mulki sun amfana da mulkinsa ko a’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai saci kuɗin gwamnati ba lokacin da yake mulki.

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi ikirarin cewa dukiyarsa ba ta ƙaru ba tun daga lokacin da ya hau mulki har zuwa saukarsa.

Kara karanta wannan

'Mun yi kuskure,' Gwamnatin Tinubu ta ba da hakuri kan maganar nada mukamai

Shehu Sani
Shehu Sani ya nuna shakka kan cewa Buhari bai saci kudin gwamnati ba. Hoto: Bashir Ahmad|Shehu Sani
Asali: Facebook

Furuci ya jawo ce-ce-ku-ce daga wasu ‘yan Najeriya har ya kai ga Shehu Sani ya masa martani a wani sako da ya wallafa a Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Shehu Sani ya ce irin halin da talakawa suka shiga bayan shekaru takwas na mulkinsa ne abin lura ba wai ko ya tara kudi ba.

Shehu Sani: Allah ne ya san gaskiyar zancen Buhari

Shehu Sani ya yi martanin da ke nuna shakku kan maganar da Buhari ya yi na cewa bai tara kudin gwamnati ba.

A cewarsa:

“Wani tsohon shugaban ƙasa yana alfahari da cewe dukiyarsa ba ta karu ba a lokacin da ya fara mulki har zuwa karshe.
"Allah ne ya san gaskiyar maganar, sai kuma iyalansa da 'yan uwansa."

Ya ce abin da ya fi kamata mutane su duba shi ne halin da masu zaɓe suka shiga bayan wahalar da suka sha da sadaukarwar da suka yi kafin samun nasarar Buhari a 2015.

Kara karanta wannan

Buhari ya fadi adadin dukiyarsa kafin zama shugaban ƙasa da bayan barin mulki

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa:

“Ina da tabbacin babu wani ɗan siyasa da talakawa suka tara masa kuɗi da dukiyoyinsu, suka rasa rayuka domin ganin ya hau mulki kamar Buhari.
"Amma tambaya ita ce: shin bayan ya hau mulki, talakawan sun samu sauƙi ne?”
Shehu Sani
Shehu Sani ya yi raddi wa Buhari kan maganar satar kudin gwamnati. Hoto: @ShehuSani
Asali: UGC

Maganar badakalar CBN a lokacin Buhari

Shehu Sani ya jaddada cewa ba wai kawai maganar tsabtace kai da rayuwa mai sauƙi ke da muhimmanci ba, illa a kalli abubuwan da suka faru a hukumomin gwamnati a lokacinsa.

A cewar Shehu Sani, ya kamata a yi dubi ga abubuwan da suka faru a lokacin Buhari musamman babban bankin Najeriya (CBN).

Hukumar EFCC ta kama tsohon bankin CBN da ya yi aiki a lokacin Buhari bisa zarge zargen cin hanci da rashawa.

Gyaran gida: Buhari ya yabawa Shugaba Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi godiya wa gwamnatin Bola Tinubu kan gyara masa gida.

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

Buhari ya yaba da kokarin gwamnatin Bola Tinubu ne yayin da gwamnonin APC suka kai masa ziyara a gidansa da ya koma a Kaduna.

Tun bayan kammala mulki a 2023, shugaba Buhari ya tare a gidansa da ke Daura kafin a gyara masa gidansa na Kaduna ya koma can.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng