Dangote Ya Sauke Farashin Fetur bayan Dawo Sayar Masa Mai da Naira

Dangote Ya Sauke Farashin Fetur bayan Dawo Sayar Masa Mai da Naira

  • Matatar Dangote ta sanar da sauke farashin fetur bayan sun tattauna da gwamnatin tarayya kan sayar masa da mai da Naira
  • Tuni dai manyan dilolin mai suka fara daukan fetur daga matatar Dangote da ke Legas bayan cimma yarjejeniyar da ya yi da gwamnati
  • Dama dai tun da gwamnatin Najeriya ta sanar da cigaba da sayar masa da danyen mai da Naira aka fara hasashen samun saukin kudin fetur

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Rahotanni na nuni da cewa matatar Dangote ta rage kudin litar man fetur zuwa N865 daga N888.

Sabon farashin ya nuna cewa an samu saukin N15 idan aka kwatanta da yadda matatar ta sayar da litar mai a ranar Laraba da ta wuce.

Dangote
Matatar Dangote ta rage kudin litar fetur. Hoto: Dangote Industries.
Asali: UGC

Punch ta wallafa cewa a safiyar Alhamis, 10 ga watan Afrilu 2025, matatar Dangote ta sanar da rage kudin.

Kara karanta wannan

An buga asara a Kano da mummunar gobara ta tashi a kasuwar Gandun Albasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yarjejeniyar sayar da mai da Naira

A ranar Laraba, majalisar zartarwa ta ƙasa ta bayar da umarnin cigaba da aiwatar da yarjejeniyar sayar da danyen mai da Naira wa matatu masu sarrafa mai na cikin gida.

Hakan ya fito ne a wani bayani da ma’aikatar kuɗi ta fitar, inda ta bayyana cewa tsarin ba na ɗan lokaci ba ne.

Ta ce tsari ne da gwamnati ke so ta kafa domin cigaba da sarrafa danyen man fetur da aka hako a Najeriya.

Bayan taron da Ministan Kuɗi ya gudanar da wakilan kamfanin Dangote a ranar Talata, an bayyana cewa gwamnati za ta ci gaba da goyon bayan tsarin don rage shigo da mai daga waje.

Sauran gidajen mai za su rage farashi

Rahotanni sun ce manyan gidajen mai kamar kamfanin MRS, Ardova Plc, Heyden da wasu, waɗanda ke da yarjejeniya da kamfanin Dangote, na shirin rage farashin man fetur.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke mutane sama da 100 da suka kai farmaki cikin dare a Abuja

Rahoton Channels TV ya nuna cewa gidajen man suna sayar da litar mai a kusan N925 zuwa N910 domin daidaita da farashin matatar Dangote ta kara a baya.

Dama duk lokacin da matatar Dangote ta rage farashin mai ana samun sauki daga gidajen man da suke hulda da matatar.

Dangote
Dangote ya sauke farashin mai. Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Talaka zai ci rabar saukin farashin?

Samun saukin farashin na zuwa a wani lokaci da ‘yan Najeriya ke fama da tsananin hauhawar farashi da matsananciyar wahala.

Wani mai aikin acaba a jihar Gombe, Muhammad Ibrahim ya ce samun saukin zai taimaka ta bangarori da dama.

'Duk da cewa ba kowane gidan mai ake samun saukin ba, amma dai ba a raina sauki komin kadan din shi.
"Muna fata kamar yadda aka sanar a jaridu, za muga sauyi a gidajen mai."

Farashin danyen mai ya karye a duniya

A wani rahoton, kun ji cewa farashin danyen mai ya karye a kasuwar duniya yayin da Amurka ke lafta haraji wa kasashe.

Kara karanta wannan

Gaba da gabanta: Umarnin da kotu ta ba shugaban riko a Rivers bayan saba mata

Rahotanni sun nuna cewa wannan ne fadin farashin mai mafi muni da aka samu tun shekarar 2021.

An bayyana cewa saukar farashin zai iya yin tasiri wajen rage farashin man fetur a Najeriya, wanda hakan zai iya shafar farashin kayayyaki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng