Ruwan Sama Ya Yi Gyara a Kebbi, Daruruwan Gidaje Sun Ruguje

Ruwan Sama Ya Yi Gyara a Kebbi, Daruruwan Gidaje Sun Ruguje

  • Gidaje da dama sun ruguje bayan an samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi
  • Ruwan wanda yake haɗe da iska mai ƙarfin gaske da ya auku a ranar Talata, ya yi sanadiyyar lalata gidaje aƙalla guda 240
  • Gwamna Nasir Idris ya yi alƙawarin ba da agajin gaggawa domin ragewa mutanen da lamarin ya shafa raɗadin da suke ciki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya tare da iska mai ƙarfin gaske sun lalata gidaje a jihar Kebbi.

Ruwan saman da aka yi a ranar Talata, ya yi sanadiyyar rushewar aƙalla gidaje 240 a ƙauyen Garin Kestu, da ke cikin mazaɓar Atuwo a ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi.

Ruwan sama ya yi gyara a Kebbi
Ruwan sama ya lalata gidaje a Kebbi Hoto: @NasiridrisKG
Asali: Facebook

An tabbatar da rugujewar gidaje a Kebbi

Mai Magana da yawun gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Ahmed Idris, shi ne ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gama magana, ya faɗi matsayarsa kan ficewa daga LP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan iftila’i ya jefa al’ummar yankin cikin babban tashin hankali da asarar dukiya mai yawan gaske.

A cewar mai magana da yawun gwamnan, ruwan saman wanda ke haɗe da iska mai ƙarfin gaske ya rusa gidaje 240 tare da lalata dukiyoyi da darajarsu ta kai miliyoyin Naira.

Ya nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki saboda ba a samu asarar rai ba a dalilin ruwan saman.

Gwamnatin Kebbi za ta tallafawa jama'a

Gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, ta bakin shugaban ƙaramar hukumar Shanga, Alhaji Audu Dan Audu, ya jajanta wa waɗanda abin ya shafa.

Dr. Nasir Idris ya bayyana cewa gwamnati za ta gaggauta kawo agaji domin rage musu raɗaɗin wannan iftila’i.

“Gwamna ya umarce ni da na ziyarci al’ummar da abin ya shafa domin tantance irin ɓarnar da aka yi wa gidajensu da dukiyoyinsu."

"Haka kuma ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta kawo taimakon gaggawa cikin lokaci, wanda ya haɗa da kayan gini, abinci da sauran kayan agaji domin rage musu asarar da suka yi."

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya tsage gaskiya, ya fadi fargabarsa kan 'yan Boko Haram

- Alhaji Ahmed Idris

Ruwan sama ya yi gyara a Kebbi
Gidaje sun ruguje sakamakon ruwan sama a Kebbi Hoto: @NasiridrisKG
Asali: Twitter

Gwamnan jihar Kebbi ya yi nasiha

Gwamnan ya kuma buƙaci al’umma da su karɓi wannan iftila'i da zuciya ɗaya, su yarda cewa kaddara ce daga Allah, wanda ke da ikon kawo komai a lokacin da ya so.

Al’umma sun bayyana mamakinsu bisa irin yadda aka samu ruwan sama a wannan lokaci, duba da cewa ba a saba samun ruwa mai ƙarfi a farkon lokacin damina ba a jihar Kebbi.

Sai dai duk da haka, ruwan ya kawo sauƙi ga jama’a kan tsananin zafin da aka daɗe ana fama da shi

A halin yanzu, ana sa ran cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace don tallafa wa waɗanda suka rasa matsugunnansu.

Ruwan sama ya ruguza gidaje a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa ruwan sama kamar da bakin ƙwarya ya yi gyara a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu ya fadi hanyar kawo karshen kisan gilla a jihar Filato

Ruwan saman ya yi sanadiyyar lalata rumbunan abinci da gidaje aƙalla guda 70 a ƙaramar hukumar Langtang ta jihar Plateau.

Mutanen da lamarin ya ritsa da su sun miƙa ƙoƙon bararsu ga gwamnatin jihar kan ta kawo musu ɗauki cikin gaggawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng