'Kun Raina Sarki': An Bukaci Ƴan Sanda Su Nemi Afuwar Sanusi II saboda Kiransa 'Alhaji'

'Kun Raina Sarki': An Bukaci Ƴan Sanda Su Nemi Afuwar Sanusi II saboda Kiransa 'Alhaji'

  • Wata Kungiya ta bukaci ’yan sanda su nemi afuwa saboda cewa “Alhaji Sanusi” maimakon “Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II”
  • Mai magana da yawun kungiyar, Nura Ali ya ce hakan raini ne da cin mutunci ga matsayin Sarautar Kano da tarihinta a Arewacin Najeriya
  • Kungiyar ta kuma gargadi ’yan sanda da ka da su bari siyasa ta rinjaye aikinta na kare rayuka da dukiyoyi tare da mutunta shugabannin gargajiya
  • Kungiyar ta bukaci daukacin shugabannin gwamnati da al’umma su fifita zaman lafiya da sulhu don kaucewa rikici da rikitarwa a jihar Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Wata kungiya mai rajin kare muradun al’umma mai suna CCKCSG ta bukaci ’yan sanda su nemi afuwar Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Kungiyar ta ce ya kamata rundunar ta nemi yafiya saboda kiran basaraken da “Alhaji Sanusi” a wata takardar da hukumar ta fitar.

Kara karanta wannan

Kano: Buba Galadima ya yi maganar yiwuwar sake sauke Sanusi II da maido shi

An caccaki ƴan sanda kan kiran Sanusi II da 'Alhaji'
Kungiya ta bukaci yan sanda su nemi afuwar Sanusi II bayan kiransa da 'Alhaji'. Hoto: Sanusi II Dynasty, Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

An soki yan sanda kan kaskantar da Sanusi II

Mai magana da yawun kungiyar, Nura Ali bayyana hakan a taron manema labarai a Kano inda ya ce hakan cin mutunci ne da raini, cewar Daily Nigerian.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kiran Sarkin Kano da “Alhaji Sanusi” ba kuskure ba ne, illa wata manufa ce ta raina sarki da kuma mutuncin al’adun Kano.

Ya ce:

“Abin takaici ne yadda aka raina Sarkin Kano ta hanyar kiransa da ‘Alhaji Sanusi’ a wata takarda ta hukumomin tsaro suka fitar.
“Wannan ba kuskure bane, wata manufa ce ta nuna raini da rashin girmamawa ga tarihinmu da al’adunmu na gargajiya.
“Sarki Muhammadu Sanusi II, shi ne sarkin Kano na 16 kuma jagoran al’adunmu, wanda taken sarautarsa ke dauke da tarihin mutanenmu da burinsu.
“Cire masa wannan take a wata takarda ta hukuma yana nuna rashin mutunta masarautar Kano da kuma al’adun Arewacin Najeriya.
“Don haka muna bukatar ’yan sanda su ba da hakuri cikin gaggawa tare da yin alkawarin kiransa da “Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi II” a gaba."

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tsoma baki a rikicin sarautar Kano bayan janye gayyatar Sanusi II

An bukaci yan sanda sun ba Sanusi II hakuri
Kungiya ta nemi yan sanda su nemi yafiyar Sanusi II bayan kiransa da sunan 'Alhaji'. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi.
Asali: Twitter

Kungiya ta shawarci hukumar yan sanda

Kungiyar ta kuma bukaci Sufeto Janar na ’yan sanda, Hukumar Kula da Ayyukan ’yan sanda da sauran hukumomi su tabbatar da adalci da gaskiya.

Ta ce dole ne ’yan sanda su kaucewa shisshigi na siyasa, su mayar da hankali kan kare rayuka da dukiyoyi ba tare da nuna bangaranci ba.

Kungiyar ta bukaci a girmama sarakunan gargajiya yadda ya dace domin su na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya a cikin al’umma.

Kungiyar ta yi gargadin cewa bai kamata rundunar ’yan sanda ta dauki wani mataki da zai nuna karancin tunani ko wulakanci ga al’adun Kano ba.

Sanusi II ya yi sababbin nade-nade

Kun ji cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi sababbin nade-nade a masarauta, ciki har da ɗansa Adam Lamido Sanusi (Ashraf).

A wata sanarwa da masarautar ta fitar, ta bayyana cewa an nada Ashraf Sanusi a matsayin sabon Tafidan Kano.

Nade-naden sun hada da Munir Sanusi Bayero daga Wamban Kano zuwa Galadiman Kano, Kabiru Tijjani Hashim daga Turakin Kano zuwa Wambai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.