Buhari Ya Fadi Adadin Dukiyarsa kafin Zama Shugaban Ƙasa da bayan Barin Mulki

Buhari Ya Fadi Adadin Dukiyarsa kafin Zama Shugaban Ƙasa da bayan Barin Mulki

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya bar mulki da dukiyar da ya mallaka tun kafin ya zama shugaban kasa ba tare da ƙaruwa ba
  • Buhari ya shawarci shugabanni su mayar da hankali wajen kyautata rayuwar jama'a fiye da neman jin daɗin kansu a lokacin da suke mulki
  • Ya yaba wa gwamnatin Bola Tinubu bisa gyaran gidansa da ke Kaduna, yana mai cewa duk da haka bayyanar gidan bai canza ba a waje
  • Gwamna Hope Uzodinma ya ce Buhari ya taka rawa sosai wajen kafa jam'iyyar APC, yana kuma kira da ci gaba da jagoranci da shawarwari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi magana kan salon shugabanci nagari.

Buhari ya shawarci shugabanni su mayar da hankali wajen kyautata rayuwar jama'a fiye da neman jin daɗin kansu a mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya aiko sako daga Faransa kan mutuwar shugaban MTN na farko

Buhari ya kalubalanci shugabanni kan salon mulki nagari
Muhammadu Buhari shawarci shugabanni kan gudanar da mulki. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Twitter

Buhari ya magantu kan yawan dukiyarsa

Buhari ya bayyana cewa ya bar ofis da yawan dukiyar da ya mallaka tun kafin ya zama shugaban kasa, ba tare da ƙara wani abu ba a rayuwarsa, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake karɓar bakuncin gwamnoni na jam'iyyar APC a gidansa da ke Kaduna, Buhari ya ce shugabanci kalubale ne kuma dama ce ga ci gaban ƙasa.

Ya yaba da ci gaban da kungiyar gwamnonin APC ke samu, yana mai jaddada bukatar su ci gaba da sadaukar da kai wajen ci gaban Najeriya gaba ɗaya.

Buhari ya nuna godiya ga gwamnatin Bola Tinubu saboda gyaran gidansa da ke Kaduna, inda ya ce an inganta ciki sosai duk da waje bai canza ba.

Ya kuma gode wa gwamnoni da suka kai masa ziyara, yana mai cewa wasu daga cikinsu ya yi aiki tare da su, yayin da wasu kuma sabbi ne a gare shi.

Kara karanta wannan

Nada mukamai: Sanata Ndume ya dura kan Tinubu, ya ce bai tsoron me zai biyo baya

Buhari ya yi magana kan yawan dukiyarsa a Najeriya
Buhari ya fayyace yadda dukiyarsa take kafin da kuma bayan ya bar mulki. Hoto: @GarShehu.
Asali: Twitter

Dalilin ziyarar gwamnoni wajen Buhari

A bangarensa, Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, wanda shi ne shugaban gwamnonin APC, ya ce sun kawo ziyara ne domin taya Buhari murnar Sallah da nuna godiya gare shi.

A cewar Uzodinma:

"Yawancinmu muna alfahari da irin rawar da ka taka wajen kafa jam'iyyar APC, wadda har yanzu take jagorantar tafiyarmu.
"Muna matuƙar farin ciki da yadda ka bayyana cewa jam'iyyar APC ita ce jam'iyyarka ta zaɓi, hakan ya ƙara mana ƙwarin gwiwa.
"Ka ci nasara a zabe, ka yi mulki cikin natsuwa, sannan ka mika mulki ga wani shugaban APC cikin mutunci da daraja."

Ya ce gwamnatin Buhari ta tabbatar da ayyukan raya ƙasa, ta hanyar yakar cin hanci, farfaɗo da tattalin arziki da kuma inganta harkokin tsaro.

Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari

Kun ji cewa Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe tare da wasu gwamnoni na APC sun kai ziyara ta musamman ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun ziyarci Buhari yayin da ake rubibin sauya sheka zuwa SDP

Majiyoyi sun nuna cewa ziyarar ta gudana ne karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Gwamnonin APC, Sanata Hope Uzodinma na jihar Imo.

Gwamna Uzodinma ya ce ziyarar na nuni da girmamawa, biyayya da kuma goyon bayan da jam’iyyar ke ci gaba da bai wa tsohon shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.