Daga karshe Buhari Ya Fadi Wanda Ya Dauki Nauyin Zamanantar Masa da Gida a Kaduna

Daga karshe Buhari Ya Fadi Wanda Ya Dauki Nauyin Zamanantar Masa da Gida a Kaduna

  • Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi maganar gyara masa gidansa na Kaduna yayin ya karɓi baƙuncin gwamnonin APC
  • Buhari ya yi wa gwamnonin na APC nasiha kan muhimmancin ba da fifiko ga jin daɗin mutanen da suke shugabanta a ƙarƙashinsu
  • Shugaban ƙungiyar gwamnonin na APC ya yi godiya ga tsohon shugaban ƙasan kan rawar da ya taka wajen kafa jam'iyya mai-ci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi nasiha ga gwamnonin jam'iyyar APC da suka ziyarce shi a Kaduna.

Muhammadu Buhari ya shawarci gwamnonin da su yi shugabanci wanda zai mayar da hankali kan buƙatun ƴan ƙasa.

Buhari ya gana da gwamnonin APC
Buhari ya sanya labule da gwamnonin APC a Kaduna Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

Mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasan, Garba Shehu ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Buhari ya bayyana cewa shugabanci na ƙunshe da kalubale da dama, amma kuma dama ce da za a iya amfani da ita wajen inganta ci gaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Abin da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ke bukata daga ƴan Arewa

Buhari ya godewa Tinubu kan gyara masa gida

Tsohon shugaban ƙasan ya kuma yi magana kan gyara masa gidansa da gwamnatin mai girma Bola Tinubu ta yi a Kaduna.

Ya godewa gwamnatin Tinubu saboda gyaran da aka yi wa gidansa da ke Kaduna, inda ya bayyana cewa ko da yake wajen gidan bai canza ba, amma an yi masa gagarumin gyara daga ciki.

Tsohon shugaban ya bayyana gamsuwarsa da ci gaban da ake samu ƙarƙashin gwamnonin APC, sannan ya sake jaddada buƙatar jajircewa don cigaban ƙasa baki daya.

Ya ƙara da cewa ya kamata shugabanni su riƙa fifita jin daɗin al’umma fiye da nasu, yana mai ba da misalin kansa inda ya bayyana cewa ya bar ofis da dukiyar da ba ta wuce wadda ya mallaka ba kafin ya zama shugaban ƙasa.

Ya godewa gwamnonin bisa ziyarar da suka kai masa, yana mai cewa ko da ya kasance yana aiki da wasu daga cikinsu a baya, wasu kuwa sababbi ne a gare shi.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya gama magana, ya faɗi matsayarsa kan ficewa daga LP

Gwamnonin jihohin APC sun yabi Buhari

Shugaban ƙungiyar gwamnonin APC kuma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa ziyarar ta su na da nufin taya tsohon shugaban murnar zuwan ƙaramar Sallah.

Muhammadu Buhari
Buhari ga gana da gwamnonin APC Hoto: @GarShehu
Asali: Twitter

Ya ce sun kuma je wajensa ne domin girmama shi bisa irin gagarumin gudunmawar da ya bayar wajen kafa dimokuradiyya a Najeriya da kuma ƙarfafa jam’iyyar APC.

“Da dama daga cikinmu muna alfahari da rawar da ka taka wajen kafa jam’iyyar APC."
“Muna farin ciki kwarai da jin tabbacin da ka bayar kwanan nan cewa har yanzu APC ita ce jam'iyyar ka. Wannan furuci ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar irin haka."
"Maganar da ka yi ta tabbatar da matsayinka a matsayin ginshiƙi a tafiyarmu, kuma ta karfafa gwiwar mambobin jam’iyyar. Shugaban kasa, kai cikakken ɗan Najeriya ne mai kishin ƙasa."

- Gwamna Hope Uzodimma

Gwamnonin APC sun nemi alfarma wajen Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun miƙa ƙoƙon bararsu ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, shugaba a APC ya fadi tagomashin da Arewa ta samu a mulkin Tinubu

Gwamnonin na APC sun buƙaci Buhari da ya yi magana da na kusa da shi saboda ka da su fice daga jam'iyyar.

Sun nemi tsohon shugaban ƙasan da ya lallaɓi wasu daga cikin tsofaffin ministocinsa kan ka da su raba gari da jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng