Farashin Man Fetur Zai Kara Araha a Najeriya da Gwamnatin Tinubu Ta Dawo da Tsarinta

Farashin Man Fetur Zai Kara Araha a Najeriya da Gwamnatin Tinubu Ta Dawo da Tsarinta

  • Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa tsarin cinikin ɗanyen mai da Naira na nan daram domin shiri ne na tsawon lokaci
  • Ma'aikatar kudi da tattalin arzikin kasa ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, 9 ga watan Laraba, 2025
  • Wannan mataki dai ya gamu da kalubale a kwanakin baya wanda ta kai har matatar Ɗangote ta daina saida fetur da Naira

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƴan Najeriya na iysa samun sauƙin tsadar man fetur nan ba da jimawa ba yayin da Gwamnatin Tarayya ta dawo da tsarin cinikin ɗanyen mai da Naira.

Gwamnatin Tarayya karƙashin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ta jaddada cewa tsarin sayar da ɗanyen mai da man da aka tace da Naira ya zama 'tsari na kasa'.

Kara karanta wannan

"Mutum 1 ke juya APC," Tsohon mataimakin shugaban PDP ya faɗi shirin da suke yi

Bola Tinubu.
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ci gaba da tsarin sayar da ɗanyen mai ga Dangote a Naira Hoto: @OfficialABAT
Asali: Getty Images

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da ma'aikatar harkokin kudi ta tarayya ta wallafa a shafin X yau Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta maido tsarin ciniki da Naira

Ma'aikatar ta bayyana cewa wannan tsari na ciniki da Naira, wanda Majalisar Zartarwa (FEC) ta amince da shi tun farko, tsari ne da zai ɗauki dogon lokaci ana amfana da shi.

A cewarta, tsarin wata dabara ce da gwamnati ta ɓullo da ita domin amfanin ƙasa, ba wani mataki ne na ɗan lokaci da za a yi ya wuce ba.

Ta ƙara da cewa masu ruwa da tsaki a harkokin mai sun sake haduwa domin jaddada cikakken goyon bayansu da kuma aniyar ci gaba da aiwatar da tsarin cikin nasara.

Manufar tsarin sayar da ɗanyen mai da Naira

Manufar wannan tsari ita ce yin cinikayyar danyen mai da man da aka tace da kuɗin gida Najeriya watau Naira.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki babban mataki da Amura ta kakaba haraji kan Najeriya

An bullo da shi ne domin karfafa tattalin arzikin ƙasa, inganta tace mai a cikin gida, da daidaita kasuwar musayar kuɗi don rage bukatar Dala a harkokin mai.

Ma’aikatar ta bayyana cewa tsarin zai kuma taimaka wajen inganta tsaron makamashi da kuma haɓaka zuba jari a bangaren tace mai a cikin gida.

Dangote da Tinubu.
Gwamnatin Tarayya ta gana da wakilan Ɗangote Hoto: @OfficialABAT, Aliko Ɗangote
Asali: UGC

Sanarwar ta ce:

“Sayar da ɗanyen mai da man da aka tace da Naira ba tsari ne na ɗan lokaci ba, amma tsari ne da gwamnati ta ɓullo da shi domin haɓaka harkokin tace mai a gida, inganta makamashi da rage dogaro da canjin kuɗin waje.
“Kamar yadda aka saba, kwamitin da aka kafa ya fahimci cewa ana iya fuskantar kalubale a lokaci bayan lokaci wajen aiwatar da wannan tsari.
"Amma wadannan matsaloli ana kokarin shawo kansu ta hanyar aikin haɗin gwiwa tsakanin dukkan masu ruwa da tsaki.”

Gwamnati ta gana da wakilan Ɗangote

Sanarwar ta ce jami’an Ma’aikatar Kudi da kwamitin aiwatar da wannan tsari sun gudanar da taro a ranar Talata domin duba ci gaba da kuma shawo kan matsalolin da ke akwai.

Kara karanta wannan

"Najeriya za ta shiga rudani," JNI ta ja kunnen gwamnati kan kisan kiyashi a Filato da Kebbi

Wadanda suka halarci taron sun hada da Ministan Kudi da tattalin arziki watau Wale Edun, wanda shi ne shugaban kwamitin.

A cikin mahalartan, Legit Hausa ta ji cewa akwai sauran shugabannin ƙananan kwamitoci da jami'an kamfanin mai (NNPCL)

Sauran mahalarta taron sun haɗa da shugaban hukumar tattara haraji (FIRS), wakilan matatar Ɗangote da sauran masu ruwa da tsaki.

Fetur zai iya sauka zuwa kasa da N400

A wani rahoton, kun ji cewa ƙungiyar masu matatun man fetur ta Najeriya (CORAN) ta ce akwai yiwuwar farashin litar man fetur ya sauka kasa da N400.

CORAN ta bayyana cewa matukar ana ba su dama suka ci gaba da sayen ɗanyen mai a gida kuma su tace a gida, man fetur zai yi araha sosai a ƙasar nan.

Kungiyar ta kara da cewa daidaita farashin dala zai iya kara sanya farashin man fetur ya karye warwas a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel