Daga karshe Nuhu Ribadu Ya Fadi Kudin Fansan da Gwamnati Ta Taba Biya
- Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya nuna damuwa kan kuɗaɗen fansa da ake biyan ƴan bindiga
- Nuhu Ribadu ya gargaɗi iyalan mutanen da suka tsinci kansu a hannun ƴan bindiga kan su daina ba da kuɗaɗen fansa
- Mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaron ya bayyana cewa ba ƴan bindiga kuɗi, yana jawowa su ƙara ƙarfin aikata ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya yi magana kan biyan ƴan bindiga kuɗin fansa.
Nuhu Ribadu ya yi gargaɗi ga iyalan mutanen da ƴan bindiga suka sace kan cewa su daina biyan kuɗin fansa.

Asali: Facebook
Nuhu Ribadu ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar wasu daga cikin mutanen da aka ceto a ranar Talata, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me Nuhu Ribadu ya ce kan biyan kuɗin fansa
Mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaron ya bayyana cewa an ceto mutanen ne sakamakon ayyukan sojoji, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
An karɓi mutanen da aka ceto ne a cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
“Don Allah ku daina ba wa waɗannan mutanen kuɗi, wannan shi ne abu mafi wahala da muke fuskanta."
"Da yawa daga cikin mutanen nan da aka sace, iyalansu sun bai wa masu garkuwa da su kuɗi, amma hakan bai kai ga sakin su ba. Mu jami’an tsaro ne dai muka ceto su."
“Ba kuɗin da ake bayarwa ne ke sanyawa a sake su ba. Waɗannan mutane, yadda ake ci gaba da ba su kudi, haka suke ƙara samun ƙarfi da haddasa matsala gare mu."
"Ba mu taɓa ba kowa ko sisi ba, kuma ba ma so mutane su riƙa badawa."

Kara karanta wannan
Babban basaraken Igbo ya gargadi 'yan Arewa kan kisan mafarauta a Edo? An ji gaskiya
- Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu ya faɗi illar biyan kuɗin fansa

Asali: Facebook
A cewar Nuhu Ribadu, ƴan Najeriya na taimakawa ayyukan masu garkuwa da mutane a faɗin ƙasar nan idan suka ci gaba da biyan kuɗin fansa.
“Dukkan manufar su ita ce su samu kuɗi, kuma idan aka ci gaba da ba su, tamkar an ce musu su ci gaba da yin hakan ne."
"Muna roƙon jama’armu, ƙasar nan gaba ɗaya, don Allah a daina biyan wannan kuɗi. Ku ba mu dama mu yi aikinmu. Za mu yi shi yadda ya dace."
- Nuhu Ribadu
Nuhu Ribadu ya danganta nasarar ceto waɗanda aka sace da ƙoƙarin da jaruman dakarun sojojin Najeriya da sauran hukumomin tsaro suka yi.
Ribadu ya yi magana kan kashe-kashe a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa Nuhu Ribadu wanda yake ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, ya yi tofin Allah tsine kan hare-haren ƴan bindiga a.jihar Plateau.
Nuhu Ribadu ya yi Allah wadai kan hare-haren da ƴan bindiga suka kai a ƙaramar hukumar Bokkos, waɗanda suka jawo asarar rayukan mutane masu yawa.
Mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa gwamnati ba za ta lamunci irin wannan ta'addancin ba.
Asali: Legit.ng