Nuhu Ribadu Ya Fadi Hanyar kawo Karshen Kisan Gilla a Jihar Filato
- Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar Filato
- Hare-haren da aka kai a ƙaramar hukumar Bokkos sun haifar da asarar rayuka da dama, an kashe akalla mutum 50, yayin da ake neman gawarwaki
- A lokacin ziyarar da ya kai a Jos, Ribadu ya yi kira da a samar da haɗin kai tsakanin al’umma da gwamnati wajen kawo ƙarshen rikice-rikicen
- Ya ƙara da cewa lokaci ya yi da al’umma za su ɗauki matakin kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakaninsu, ta yadda za a samu sauki daga matsalar tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga suka kai a jihar Filato.
Yayin da ya yi kakkausar sukar, Nuhu Ribadu ya kara da cewa gwamnati ba za ta lamunci kisan gillar da ake yi wa bayin Allah a jihar ba.

Asali: Facebook
Jaridar The Nation ta wallafa cewa Mashawarcin shugaban ƙasa ya bayyana haka ne a lokacin da ya ziyarci dakarun operation Fansan Yamma a Jos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Harin Filato ya kashe mutum 50
Hare-haren sun afku ne a makon da ya gabata a wasu kauyuka a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bokkos, inda aka kashe akalla mutane 50, kamar yadda rahotanni suka nuna.
A lokacin da ya kai ziyararsa hedkwatar rundunar Operation Safe Haven a Jos, Ribadu ya bayyana cewa:
"Muna fuskantar mawuyacin lokaci, amma hakan ba zai dawwama ba."
Ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin al’umma da gwamnati wajen kawo karshen kashe kashen da sauran matsalolin tsaro.
Filato: Nuhu Ribadu ya nemi hadin kai
Ribadu ya kuma yi kira ga al’ummomi da su ɗauki matakin kawar da matsalar da kansu ta hanyar taka wa rashin jituwar da ke tsakaninsu burki don samun sauki.

Asali: Facebook
Mashawarcin shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ‘yan bindiga suke ci gaba da kai wa yankin.
Ribadu ya ce duk da dakarun tsaro na yin dukkanin abin da ya dace, hadin kan jama'a babban sinadari ne da zai taimaka wajen dawo da zaman lafiya a yankunansu.
JNI ta yi gargadi kan kisan Filato
A baya, kun samu labarin cewa kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana damuwarta kan kisan da ake yi a jihar Filato, wanda ke ci gaba da jawo zaman tsoro a Bokkos da kewaye.
Rahotanni sun nuna cewa akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu a ƙaramar hukumar Bokkos, jihar Filato, sakamakon hare-haren da ‘yan bindiga suka kai garuruwa da dama.
Sanarwa da aka fitar daga ofishin sakataren JNI, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, kungiyar ta yi gargadi ga gwamnatin jihar Filato da ta ɗauki matakan gaggawa don magance rikicin.
Asali: Legit.ng