"Najeriya za Ta Shiga Rudani," JNI Ta Ja Kunnen Gwamnati kan Kisan Kiyashi a Filato da Kebbi

"Najeriya za Ta Shiga Rudani," JNI Ta Ja Kunnen Gwamnati kan Kisan Kiyashi a Filato da Kebbi

  • Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana damuwa kan kisan kiyashi da ake yi a Filato, wanda ta ke ganin zai zama babbar barazana ga harkar tsaro
  • JNI, ta bakin sakatarenta, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, ta ce akwai alamun Najeriya za ta fada cikin rudani idan aka ci gaba da tafiya haka
  • Kungiyar ta gargadi gwamnatocin tarayya, Filato, Kebbi da Katsina da su gaggauta daukar matakan da za su dawo da zaman lafiya a yankunansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta bayyana damuwarta kan kisan da ta kira da "marar dalili" da ake yi a jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 60 ne suka rasa rayukansu a karamar hukumar Bokkos da ke jihar Filato.

Kara karanta wannan

'Tinubu ba Jonathan ba ne,' APC na ganin za ta dawo mulkin Najeriya a 2027

Filato
JNI ta gargadi gwamnati kan kisan bayin Allah a Filato Hoto: Jama'atu Nasril Islam/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa JNI ta fitar da wata sanarwa daga ofishin sakatarenta, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu, inda ya ce akwai bukatar a shawo kan lamarin ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JNI ta yi gargadin cewa idan akan bar al'amura suka ci gaba a haka, zai iya haifar da rikice-rikice da rashin doka da oda.

JNI ta shiga damuwa kan kashe-kashe a Filato

Peoples Gazette ta ruwaito cewa JNI a karkashin jagorancin Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro da aka sake fuskanta a jihar Filato.

Kungiyar ta bayyana cewa hare-haren sun kasance “abin bakin ciki matuka, musamman ganin yadda zaman lafiya ke ta dawowa a yankin Filato”.

Filato
Gwamna Caleb Muftwang lokacin da ya ziyarci iyalan mutanen Filato da aka kashe Hoto: Caleb Muftwang
Asali: Facebook

A sanarwar, Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya ce:

“Kisan gilla da ake ci gaba da yi a Bokkos abin damuwa ne matuka, kuma muna fargabar cewa idan ba a shawo kan lamarin yadda ya dace ba, hakan na iya jefa kasa cikin rudani.

Kara karanta wannan

Kudin fansa: Hedkwatar tsaro ta fito da bayanin yadda aka ceto Janar Tsiga

Don haka, gwamnati ta tashi tsaye ta dauki matakin gaggawa domin kare rayuka, kasancewar jinƙai da darajar rayuwar dan Adam kamar sun zame tamkar ba su da wani muhimmanci a Najeriya. Wannan kuma yana bata wa kasar mu suna a idon kasashen duniya.
“JNI na jaddada cewa kada a bar miyagu su samu karfin guiwa a kowane irin lamari, kuma dole ne a hukunta masu aikata laifuka yadda doka ta tanada.”

Kungiyar JNI ta yi gargadi kan kisan Kebbi

A wani lamari mai kama da wannan kuma, JNI ta nuna damuwa kan yawaitar kisan da ke faruwa a karamar hukumar Augie da ke jihar Kebbi.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace kimanin mutane 50, ciki har da mata da yara, a karamar hukumar Funtua da ke jihar Katsina.

Sanarwar ta ce:

“Har yaushe ne za a ci gaba da samun irin wadannan hare-hare ba tare da dakile su ba? Lokaci bai yi ba ne da ’yan Najeriya da hukumomin tsaro za su fara daukar matakan rigakafi maimakon jiran abin ya faru kafin su dauki mataki?

Kara karanta wannan

Bayan kashe mutane sama da 50, gwamna ya gano waɗanda ke ɗaukar nauyin ta'adi

“Saboda haka, JNI na kira da gaggawa ga hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen gano masu aikata laifukan da su fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.”

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohin Filato, Kebbi da Katsina da su dauki matakan gaggawa domin dakile yawaitar kashe-kashen da suka addabi al’umma.

'Yan ta'adda sun farmaki jami'in gwamnatin Filato

A wani labarin, kun ji cewa wasu ’yan ta’adda sun kai hari kan ayarin motocin Sakataren gwamnatin jihar Filato, Samuel Jatau, a wani mummunan kwanton ɓauna da suka shirya.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilu, 2025, a ƙaramar hukumar Bokkos da ke fama da hare-haren ’yan bindiga a 'yan kwanakin nan, inda aka kashe mutum 60.

Rahotanni sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun kai harin ne kusa da ƙauyen Hurti, da ke cikin gundumar Monguna, a lokacin da sakataren ke kan hanyarsa ta zuwa wata ziyarar aiki a Bokkos.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng