"Ba Za Mu Iya ba": Gwamnatin Sokoto Ta Aika da Gargadi kan Rashin Tsaro

"Ba Za Mu Iya ba": Gwamnatin Sokoto Ta Aika da Gargadi kan Rashin Tsaro

  • Gwamnatin jihar Sokoto ba ta ji daɗin kalaman da wasu mutane ke yi ba kan matsalar rashin tsaron da ta addabi al'umma
  • Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro ya fitar da sanarwa, ya gargaɗi jama'a su guji yin kalaman da kawo cikas ga ƙoƙarin gwamnati
  • Kanal Ahmed Usman (mai ritaya) ya bayyana cewa gwamnatin jihar na bakin ƙoƙarin wajen ganin an samu tsaro a Sokoto

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnatin Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta yi gargaɗi ga mutanen jihar kan matsalar rashin tsaro.

Gwamnatin Sokoto ta gargaɗi jama'a da su guji yin kalaman da za su iya kawo cikas a ƙoƙarinta na kawo ƙarshen rashin tsaro a faɗin jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu
Gwamnatin Sokoto ta yi gargadi kan rashin tsaro Hoto: @ahmedaliyuskt
Asali: Facebook

Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara na musamman kan harkokin tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ne ya yi wannan gargaɗin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun tunkaro birnin Damaturu? Gwamnati ta yi bayani

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa gwamnatin Sokoto yin gargaɗin?

Gargaɗin ya biyo bayan wasu kalamai da aka danganta da wani Basharu Altine Guyawa, wanda ya yi ƙoƙarin nuna cewa gwamnatin jihar ba ta sauke nauyin da ke kanta a ɓangaren tsaro.

Sanarwar ta bayyana cewa irin waɗannan kalamai na iya ragewa jama’a ƙwarin gwiwar fahimtar irin ƙoƙarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi domin shawo kan matsalolin tsaro da suka addabi jihar, rahoton Tribune ga tabbatar.

“Kamar yadda gwamna ke yawan faɗi, batun tsaro lamari ne da ya shafi kowa da kowa. Gwamnati ita kaɗai ba za ta iya samar da tsaro ba tare da goyon baya da haɗin kan al’umma ba."
"Saboda haka, ya kamata jama’armu su guji yaɗa bayanai masu tayar da hankali da siyasantar da batun tsaro, maimakon haka su marawa gwamnati baya wajen samo mafita ta dindindin kan ƙalubalen tsaro da muke fuskanta."
"Gwamnati ba za ta yarda da wani yunƙuri daga kowane mutum ko ƙungiya ba da nufin kawo cikas ga ƙoƙarinta ko ɗauke mata hankali wajen shawo kan wannan matsala."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kashe kashe a Plateau, ya dauki muhimmin alkawari

- Kanal Ahmed Usman

Gwamnati na ƙoƙari kan samar da tsaro

A cewar sanarwar, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro na aiki tuƙuru domin dawo da zaman lafiya, musamman a yankin Gabashin jihar wanda ke fama da matsalolin tsaro.

Gwamna Ahmed Aliyu
Gwamnatin Sokoto ta ja kunnen jama'a kan rashin tsaro Hoto: @ahmedaliyuskt
Asali: Twitter
“Kwanan nan gwamnati ta taimaka wajen gudanar da wani atisayen haɗin gwiwa a yankin, wanda ya samu gagarumar nasara, inda aka lalata mafakar wasu ƴan bindiga da dama, sannan aka kashe wasu daga cikinsu."
"Haka kuma, an ceto mutane da dama da aka yi garkuwa da su a yayin wannan atisaye."
"Abin mamaki, Guyawa wanda shine shugaban ƙungiyar Movement for Social Justice in Nigeria ya bayar da lambar yabo ta ƙwarewa ga Gwamna Ahmed Aliyu a watan Fabrairu domin girmamawa da yabawa bisa ƙoƙarin gwamnati wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Sokoto."
“A lokacin gabatar da lambar yabon a gidan gwamnati da ke Sokoto, Guyawa da kansa ya tabbatar cewa gwamnatin jihar ta samar da dukkanin kayan aikin da suka dace, kuma hakan na haifar da sakamako mai kyau a yaƙin da ake da ƴan bindiga."

Kara karanta wannan

Kisan 'yan Arewa a Edo: Rundunar sojoji ta bayyana yadda aka warware matsalar

- Kanal Ahmed Usman

Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makaman sun kai harin ta'addanci a kan bayin Allah a jihar Sokoto.

Ƴan bindigan ƙarƙashin jagorancin hatsabibin nan Bello Turji, sun hallaka mutum 11 a harin da suka kai a garin Lugu da ke ƙaramar hukumar Isa.

Mutanen da Bello Turji da mutanensa suka kashe dai, manoma waɗanda suka fita wajen neman na abincinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng