Amnesty Int'l Ta Fadi Yadda 'Yan Sanda Suka Lallasa Masu Zanga Zanga

Amnesty Int'l Ta Fadi Yadda 'Yan Sanda Suka Lallasa Masu Zanga Zanga

  • Ƙungiyar Amnesty Int'l ta bayyana damuwarta game da yadda jami’an tsaro suka tarwatsa masu zanga-zanga a biranen Abuja da Fatakwal
  • Masu zanga-zangar ƙungiyar sun fito tituna a Abuja, Legas da sauran manyan birane, duk da gargaɗin da rundunar ‘yan sanda ta bayar
  • Amnesty ta ce a Fatakwal, masu zanga-zanga da 'yan jarida sun sha duka daga jami'an tsaro bayan an wulla masu borkonon tsohuwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta duniya, Amnesty Int'l, ta bayyana damuwarta kan yadda jami’an tsaro ke kai hari ga masu zanga-zanga a biranen Abuja da Fatakwal.

Masu zanga-zanga da ke ƙarƙashin ƙungiyar Take It Back Movement sun fito a tituna na birnin tarayya Abuja, Legas da wasu manyan birane a faɗin ƙasar nan domin bayyana ƙorafe-ƙorafensu.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Matasa sun bijirewa ƴan sanda, sun mamaye titunan Abuja da wasu jihohi

Kola Sulaimon
Amnesty da fusata da cin zarafin masu zanga-zanga Hoto: Kola Sulaimon
Asali: Getty Images

A sakon da ta wallafa a shafin X, Amnesty int'l ta ce har yanzu zanga-zangar na gudana, duk da gargaɗin da rundunar ‘yan sanda ta bayar sau da dama dangane fitowar matasan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasan kasar nan na gudanar da zanga-zangar kan zargin take haƙƙin bil’adama da kuma amfani da dokar laifukan intanet wajen tauye haƙƙin jama’a.

Zanga-zanga: Amnesty Int'l ta soki 'yan sanda

Jaridar Daily Trust ta rawaito kungiyar ta bayyana matuƙar damuwa da yadda jami’an tsaro ke cin zarafin masu zanga-zanga, inda ta bayyana hakan a matsayin take haƙƙin ɗan adam.

Ya ce:

“Amnesty na matuƙar damuwa da hare-haren da jami’an tsaro suka kai wa masu zanga-zanga a Abuja da Fatakwal.
“A Fatakwal, masu zanga-zanga da ‘yan jarida an yi musu duka. A Damaturu, jihar Yobe, an kama matasa huɗu da ba bisa ƙa’ida ba. Wadannan munanan ayyuka ba za a yarda da su ba, dole ne a gudanar da bincike kai tsaye.”

Kara karanta wannan

Matasa sun rikita Abuja da zanga zanga, an fara harba barkonon tsohuwa

'Yan sanda sun gargadi masu zanga-zanga

Rundunar ‘yan sanda ta ƙasa ta fitar da sanarwa tana gargaɗi kan gudanar da zanga-zangar, ta buƙaci masu shirya taron da su dakatar da shirye-shiryen, tana mai cewa lokacin bai dace ba.

‘Yan sanda sun ce zanga-zangar na da wata wata mummunar manufa, musamman duba da cewa ranar da aka tsara gudanar da ita ta yi dai-dai da ranar yan sanda ta kasa.

Zanga
Wasu masu zanga-zanga a Najeriya Hoto: @PstDayoEkong
Asali: Twitter

Sai dai masu zanga-zangar sun ƙi bin gargaɗin, suka fito kwansu da kwarkwatarsu zuwa manyan tituna a sassan ƙasar domin miƙa buƙatunsu.

A jihar Ribas, masu shirya zanga-zangar da suka hallara a Filin Isaac Boro da ke Fatakwal sun sha borkonon tsohuwa daga jami’an tsaro, wanda suka tarwatsa taron.

An rikita Abuja da zanga-zanga

A baya, kun samu labarin cewa a safiyar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025, jama’a a Najeriya suka fito tituna don gudanar da zanga-zanga a manyan biranen ƙasar, ciki har da Abuja da Lagos.

Kara karanta wannan

'A dawo mana da Fubara': Zanga zangar adawa da Tinubu ta barke a Rivers

Zanga-zangar, wacce kungiyar Take-It-Back Movement ta shirya, na da nufin jawo hankalin gwamnati kan halin matsin rayuwa da kuma zargin danniya da ake yi wa 'yan kasa.

A babban birnin tarayya Abuja, an ga tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Omoyele Sowore, tare da lauya mai fafutuka, Deji Adeyanju, suna jagorantar masu zanga-zangar a yankin Maitama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.