An Fayyace Shirin Peter Obi na 'Hadewa' da El Rufai a Jam'iyyar SDP

An Fayyace Shirin Peter Obi na 'Hadewa' da El Rufai a Jam'iyyar SDP

  • Na kusa da Peter Obi wanda ya yi takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Yunusa Tanko, ya yi magana kan shirinsa na komawa SDP
  • Yunusa Tanko ya bayyana cewa har yanzu Peter Obi cikakken mamba ne a jam'iyyar LP wacce ya yi takara a cikinta a 2023
  • Shugaban na ƙungiyar Obidients ya bayyana cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan bai koma SDP kamar yadda ake rayawa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban riƙon ƙwarya na ƙungiyar Obidient Movement Worldwide, Yunusa Tanko, ya yi maganan kan batun komawar Peter Obi jam'iyyar SDP.

Yunusa Tanko ya bayyana cewa har yanzu Peter Obi ɗan jam’iyyar LP ne, daga nan har zuwa wani lokaci da za a iya samun wani sabon ci gaba.

Peter Obi bai fice daga LP ba
Peter Obi bai koma SDP ba Hoto: @Peterobi
Asali: Facebook

Yunusa Tanko ya bayyana hakan ne yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Morning Brief' a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

2027: SDP ta waiwayi manyan ƴan adawa, Atiku, Obi da Kwankwaso, ta mika masu buƙata 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene shirin Peter Obi kan komawa SDP?

Jigon na LP wanda ya kasance cikin masu yaɗa manufofin takarar Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya ce tsohon gwamnan na jihar Anambra bai koma jam’iyyar SDP ba.

Yunusa Tanko ya bayyana hakan ne a matsayin martani ga iƙirarin da ɗan takarar shugaban ƙasa na SDP a 2023, Adewole Adebayo, ya yi cewa Peter Obi da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, sun fara tattaunawa don shiga SDP.

Kafin Adewole ya yi wannan magana, sakataren SDP na ƙasa, Olu Agunloye, ya ce wasu daga cikin tawagar Obi suna tattaunawa da jam’iyyar ta SDP gabanin zaɓe mai zuwa.

"Abin da na sani shi ne, mai girma Peter Obi har yanzu ɗan jam’iyyar LP ne. Haka zai ci gaba da kasancewa har sai idan wani sabon lamari ya bayyana."

- Yunusa Tanko

Yunusa Tanko ya ƙara da cewa shugabannin jam’iyyar LP za su fito da matsayarsu a fili cikin ƴan kwanaki masu zuwa, musamman dangane da hukuncin Kotun Koli da ya tuɓe Julius Abure daga matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Kara karanta wannan

Ta tabbata Atiku Abubakar ya fice daga jam'iyyar PDP? An samu bayanai

"Yanzu da nake magana da ku, akwai yiwuwar a gudanar da taron shugabannin jam’iyyar cikin wannan mako domin bayyana matsaya mai muhimmanci ga kowa, wadda za ta yi daidai da hukuncin da Kotun Koli ta yanke. Wannan zai kawo ƙarshen cece-kuce da ke faruwa yanzu."

- Yunusa Tanko

Peter Obi
Har yanzu Peter Obi dan jam'iyyar LP ne Hoto: @Peterobi
Asali: Twitter

Ƴan adawa sun kafa haɗaka

Yayin da ake shirin zaɓen shekarar 2027, tattaunawa kan haɗakar jam’iyyun adawa ta yi nisa domin kawar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

A ranar Alhamis, 20 ga watan Maris, 2025, manyan ƴan adawa irin su Atiku, Peter Obi, tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da wasu ƴan siyasa sun sanar da kafa haɗakar neman raba Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC da mulki.

Ƴan adawan sun zargi Shugaba Tinubu da gazawa wajen tafiyar da tattalin arzikin ƙasa yadda ya dace, hauhawar farashin kaya da matsanancin tsadar rayuwa.

Wannan haɗakar na fatan samun nasara ne ta hanyar dogaro da yawan ƙuri’un da Atiku da Obi suka samu a zaɓen 2023.

Kara karanta wannan

Kisan 'yan Arewa a Edo: Rundunar sojoji ta bayyana yadda aka warware matsalar

Peter Obi ya tsoma baki kan gayyatar Sanusi II

A wani labarin kuma, kun ji cewa Peter Obi ya yi magana kan janye gayyatar da ƴan sanda suka yi wa Muhammadu Sanusi zuwa Abuja.

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan ya bayyana cewa ya ji matuƙar daɗi kan janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16.

Ya kuma ce matakin ya nuna cewa mahukunta na amfani da basira wajen warware matsalolin da suka shafi rashin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel