Atiku da Shugaban SDP Sun Ziyarci Aisha Buhari bayan an Mata Rashi
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai ziyarar ta’aziyya ga Aisha Buhari bisa rasuwar dan uwanta, Yusuf Usman Halilu
- Shugaban jam’iyyar SDP na kasa, Shehu Musa Gabam, ya bi sahun Atiku Abubakar wajen yin ta’aziyya da addu’a ga marigayin
- Biyo bayan bayyanar labarin, jama’a sun bayyana matakin da Atiku ya dauka a matsayin mai kyau da nuna shugabanci mai cike da karamci da fahimta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Adamawa - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci Hajiya Aisha Muhammadu Buhari domin yin ta’aziyya kan rasuwar dan uwanta, Yusuf Usman Halilu.
Atiku ya bayyana cewa ya samu tarba daga Musa Halilu, Dujuman Adamawa, ya yi addu’ar Allah gafarta wa marigayin, Ya ba shi Aljannah Firdaus.

Kara karanta wannan
An bayyana shirin Atiku da Obi na haduwa da El Rufa'i a SDP domin kifar da Tinubu

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanan da Atiku Abubakar ya yi ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam’iyyar SDP na kasa ma ya kai ziyarar, yana mai addu’ar Allah ji kan mamacin, ya kuma ba iyalansa hakuri da juriya.
Atiku ya yi wa dan uwan Aisha Buhari addu’a
A cikin sakonsa na ta’aziyya ga tsohuwar matar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana cewa:
“Na kai ziyarar ta’aziyya ga Hajiya Aisha Buhari bisa rasuwar dan uwanta Yusuf Usman Halilu.
"Na yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya kuma azurta shi da Aljannah Firdaus.”
Shehu Gabam ya bi sahun ta’aziyyar Atiku
Shugaban jam’iyyar SDP, Shehu Musa Gabam ya kasance cikin manyan 'yan siyasa da suka ziyarci Aisha Buhari.
Shehu Musa Gabam ya wallafa a Facebook cewa:
“Na kai ziyarar ta’aziyya ga Hajiya Aisha Muhammadu Buhari bisa rasuwar dan uwanta. Allah ya azurta shi da Aljannah Firdaus, ya kuma ba danginsa juriya.”
Gabam ya yi nuni da cewa lokaci ne da ake bukatar juna sosai, yana mai jaddada bukatar a ci gaba da nuna tausayi da kulawa ga juna a cikin al’umma.

Asali: Facebook
Jama’a sun yi wa Aisha Buhari ta'aziyya
Biyo bayan bayyanar labarin, al'umma da dama sun yi addu'a ga marigayin tare da yaba wa Atiku Abubakar kan ziyarar.
Dung Zang Nyam ya ce:
“Allah ya karbi addu’arku, ya jikan Yusuf Usman Halilu. Wannan ziyarar alama ce ta shugabanci, tausayi da hadin kai da muke bukata a wannan lokaci.”
A daya bangaren, Maina Mohammed Adam ya ce:
“Mataki ne mai cike da tunani. Allah ya jikan marigayin, ya kuma saka da alheri ga wadanda suka jajanta.”
Muhammad Al-khamis Idris ya bayyana cewa:
“Wannan shugaba ne da ke nuna tausayi da sanin darajar kowa. Allah ya gafarta wa marigayin, ya saka maka da alheri.”
'Atiku da Obi na shirin sauya sheka' - SDP

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a SDP, Adewole Adebayo ya ce akwai alamar Atiku Abubakar da Peter Obi za su sauya sheka.
Adewole Adebayo ya ce idan Atiku da Obi suka shiga tafiyarsu yana da tabbas cewa za su kayar da Bola Tinubu a 2027.
Jigon na jam'iyyar ya tabbatar da cewa kofar su a bude take wajen karbar 'yan siyasa domin gina tafiyar ceto Najeriya daga halin da take ciki.
Asali: Legit.ng