'Ƴan Ta'addan Lakurawa Sun Farmaki Jami'an Tsaro a Kebbi, an Rasa Rayuka
- Jami'an tsaro na ƴan sa-kai sun rasa rayukansu a wani kwanton ɓauna da suna shiryawa ƴan ta'addan Lakurawa a Kebbi
- Ƴan ta'addan na Lakurawa sun hallaka ƴan sa-kan ne a ranar Lahadi a ƙauyen Morai da ke ƙaramar hukumar Augie
- Jami'an na ƴan sa-kai sun yi yunƙurin ƙwato shanun da ƴan ta'addan suka sace ne bayan sun kawo farmaki a ƙauyen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Ƴan ta’addan ƙungiyar Lakurawa sun kashe mutane 13 daga cikin ƴan sa-kai a jihar Kebbi.
Ƴan Lakurawan sun kashe ƴan sa-kan ne a wani hari da da suka kai a ƙauyen Morai da ke ƙaramar hukumar Augie a jihar Kebbi a ranar Lahadi.

Asali: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ƴan sa-kan guda 13 sun rasa rayukansu ne lokacin da suka yi yunƙurin daƙile harin da ƴan ta’addan suka kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sa-kan sun yi ƙoƙarin hana ƴan ta'addan tafiya da shanun da suka sace ne bayan sun farmaki ƙauyen.
Yadda ƴan Lakurawa suka kashe ƴan sa-kai
Tashar Channels tv ta ce wani mazaunin yankin, Malam Ibrahim Augie, ya bayyana cewa ƴan sa-kai da dama ne suka fito domin daƙile harin da ƴan ta’addan suka kai bayan samun labarin zuwansu.
Ya ƙara da cewa kafin su kai ga yin wani abu, ƴan ta’addan sun riga sun kewaye su, sannan suka kashe 13 daga cikinsu.
"Ƴan sa-kai sun ɓoye domin kai wa ƴan ta’addan farmaki da kuma ƙwato shanun da aka sace, amma abin takaici shi ne, ba su sani ba cewa sun riga sun hango su. Sai suka buɗe musu wuta, suka kashe su."
"Babban abin takaicin shi ne ba su sani ba cewa ƴan ta'addan sun riga da sun kewaye su."
"Suna motsawa domin tare hanyar ƴan ta’addan, sai kawai maharan suka buɗe musu wuta, inda nan take suka hallaka aƙalla mutane 13. Ƙauyen da abin ya faru yana da nisan kimanin kilomita uku kacal daga ƙauyenmu."
- Malam Ibrahim Augie
Ya zuwa yanzu, an samo gawarwaki guda shida daga cikin waɗanda aka kashe, kuma an riga an yi musu jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Bayanai sun ce ana kuma ci gaba da bincike don gano sauran gawarwakin da suka ɓace cikin daji.

Asali: Twitter
Me ƴan sanda suka ce kan harin Lakurawan?
Kokarin jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, bai yi nasara ba har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, domin ba a samu wayarsa ba.
Wannan hari na baya-bayan nan ya sake tayar da hankali a tsakanin al’ummomin jihar Kebbi, musamman a yankunan karkara da ke fama da matsalar ƴan bindiga da ƴan ta’adda.
Ƴan ta'adda sun farmaki sakataren gwamnatin Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan ta'adda sun kai farmaki kan sakataren gwamnatin jihar Plateau, Samuel Jatau.
Ƴan ta'addan sun farmaki ayarin motocin sakataren gwamnatin ne lokacin da yake kan hanyar zuwa ƙaramar hukumar Bokkos.
Samuel Jatau ya samu ya tsallake rijiya da baya a harin bayan jami'an tsaron da ke tare da shi sun buɗewa ƴan ta'addan wuta.
Asali: Legit.ng