Shugaban 'Yan Sanda Ya Janye Gayyatar Sanusi II zuwa Abuja, Ya ba da Sabon Umarni
- Sufeto-Janar na ƴan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II
- Shugaban ƴan sandan ya ce an janye gayyatar da aka yi wa Sanusi II zuwa Abuja ne bayan masu ruwa da tsaki sun shiga cikin lamarin
- Sai dai, Kayode Egbetokun ya umarci wata tawaga ta musamman da taje Kano domin samo bayanai wajen Sanusi II kan abubuwan da suka faru wajen bikin Sallah
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya ba da sabon umarni kan gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II zuwa Abuja.
IGP Kayode Egbetokun ya janye gayyatar da aka yi wa Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan
'Mene amfanin kwamishinan yan sandan Kano?' An soki gayyatar Sanusi II zuwa Abuja

Asali: Facebook
Kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X a ranar Lahadi, 6 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda za su ƙarbi bayanan Sanusi II
Olumiyiwa Adejobi ya ce shugaban ƴan sandan ya umarci jami'an sashen binciken sirri na rundunar da su tafi Kano domin ƙarɓar bayanan Sarkin kan abubuwan da suka faru.
Shugaban ƴan sandan ya ce an janye gayyatar ne sakamakon shigowar wasu manyan masu ruwa da tsaki a ƙasar nan a cikin lamarin.
Hakazalika, Sufeto-Janar na ƴan sandan ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka na cikin kudurin rundunar ƴan sanda na tabbatar da cewa ayyukanta ba a siyasantar da su ba, ko a fassara su bisa kuskure.

Asali: Twitter
Meyasa aka janye gayyatar Sanusi II
"Rundunar ƴan sandan Najeriya ta janye gayyatar da ta yi wa Alhaji Aminu Sanusi dangane da abin da ya faru a jihar Kano lokacin bikin Sallah a ranar 30 ga Maris, 2025."
"An fara aikewa da wannan gayyata ne domin ba da dama ga Alhaji Sanusi ya bayyana yadda abubuwa suka faru waɗanda suka janyo karya doka da oda a jihar."
"Sai dai, bisa shawarar da aka samu daga masu ruwa da tsaki da kuma bisa ƙudirin Sufeto-Janar na ƴan sanda na tabbatar da cewa ba a siyasantar da ayyukan ƴan sanda ba, ko a fassara su ta hanyar da ba ta dace ba, Sufeto-Janar ya bayar da umarnin a janye gayyatar."
"A madadin haka, jami’an sashen binciken sirri na rundunar ƴan sanda sun samu umarni daga Sufeto-Janar da su tafi Kano domin karɓar bayanai daga Alhaji Sanusi."
- ACP Olumuyiwa Adejobi
Shehu Sani ya magantu kan gayyatar Sanusi II
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi magana kan gayyatar da ƴan sanda suka yi wa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Shehu Sani ya bayyana cewa yin amfana da ƴan sanda ko kotun ba shi ba ne abin da ya dace wajen warware matsalar rikicin sarautar Kano.
Ya buƙaci iyalan da lamarin ya shafa da su killace kansu a wani waje domin su shawo kan matsalar rikicin wanda ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
Asali: Legit.ng