'Masarauta Ta Girmi Haka': Shehu Sani kan Gayyatar Sarki Sanusi II, Ya Nemo Mafita

'Masarauta Ta Girmi Haka': Shehu Sani kan Gayyatar Sarki Sanusi II, Ya Nemo Mafita

  • Sanata Shehu Sani ya bukaci iyalan masarautar Kano su sasanta tsakaninsu ba tare da shigar da siyasa ko neman taimakon daga waje ba
  • Ya shawarci iyalan su killace kansu a ɗaki su warware matsalarsu da kansu domin hana siyasa amfani da su a wasa
  • Sanatan ya ce amfani da kotu, ‘yan sanda ko karfi ba hanyar warware rikicin gidan sarauta ba ne a cewarsa
  • Ya nuna bakin ciki kan yadda tarihin Kano mai daraja da al’adu ke samun tozarci sakamakon rikicin cikin gida da ya addabi masarautar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Sanata Shehu Sani ya yi magana kan rigimar kan rigimar masarauta da ke faruwa a jihar Kano.

Shehu Sani ya shawarci iyalan gidan sarautar Kano su killace kansu a ɗaki su sasanta tsakaninsu ba tare da shiga siyasa ba.

Kara karanta wannan

'Mene amfanin kwamishinan yan sandan Kano?' An soki gayyatar Sanusi II zuwa Abuja

Shehu Sani ya shawarci sarakuna a Kano kan sasanta kansu
Shehu Sani ya bukaci Sanusi II da Aminu Ado su shiga daki domin sasanta kansu. Hoto: Sanusi II Dynasty, Masarautar Kano.
Asali: Twitter

Tsohon Sanatan ya bayyana haka ne a yammacin yau Lahadi 6 ga watan Afrilun 2025 a shafinsa na X kan rigimar sarauta a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gayyatar Sanusi II da yan sanda suka yi

Hakan na zuwa ne bayan yan sanda sun gayyaci Sarki Muhammadu Sanusi II domin amsa tambayoyi kan rasa rai da aka yi yayin hawan sallah.

Rundunar ta bukaci basaraken ya bayyana a gabanta zuwa ranar Talata 8 ga watan Afrilun 2025.

Sai dai matakin ya samu suka daga ɓangarorin kasar da dama da ake ganin rena masarauta ne hakan.

Shehu Sani ya soki yan sanda bayan gayyatar Sanusi II
Shehu Sani ya bukaci Sanusi II da Aminu Ado su sasanta tsakaninsu. Hoto: Sanusi II Dynasty, Shehu Sani, Masarautar Kano.
Asali: Facebook

Shehu Sani ya soki matakin ƴan sanda

Shehu Sani ya nuna damuwa kan yadda ake zubar da darajar masarautar wanda hakan bai dace ba.

Ya ce ya kamata iyalan su bar kansu a matsayin kayan wasa na siyasa domin warware matsalarsu cikin lumana da fahimta.

Ya kara da cewa amfani da kotu, ‘yan sanda ko karfi ba hanya bace ta samar da zaman lafiya a gidan sarautar Kano.

Kara karanta wannan

'Ba ni ba neman sanata': Gwamna ya ce yana gama wa'adinsa zai yi ritaya a siyasa

A cewarsa, babban birni kamar Kano da ke da tarihi mai daraja da al’adu bai kamata rikici ya bata masa suna ko ya tozarta shi ba.

A cikin rubutunsa, Sanata Shehu Sani ya ce:

“Ina ganin ya kamata iyalan gidan masarautar Kano su killace kansu a ɗaki su zauna su sasanta tsakaninsu.
"Ya kamata su daina barin kansu suna zama kayan wasa a hannun siyasa.
"Amfani da kotu, ‘yan sanda ko amfani da karfi ba hanya bace ta samar da zaman lafiya.
"Babban birni kamar Kano da ke da tarihin girmamawa da al’adu bai kamata a ci gaba da tozarta shi da irin wannan rikici ba.”

Shehu Sani ya shawarci Sanusi II, Aminu Ado

Kun ji cewa Sanata Shehu Sani ya jinjinawa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, bisa janye hawan Sallah, ya ce wannan mataki zai kawo zaman lafiya.

Sani wanda ya yi Sanata tsakanin 2019 da 2023 ya bukaci sarakan biyu su yi amfani da wata mai albarka na Ramadan don sulhu da hadin kai.

Sanata Shehu Sani ya kara da addu’ar Allah ya ba masarautar ikon fahimtar juna da kwanciyar hankali, ya ce hakan zai taimaka wajen ci gaban Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng