Dakarun Sojoji Sun Gwabza Fada da 'Yan Boko Haram, an Samu Asarar Rayuka
- Ƴan ta'addan Boko Haram ɗauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan sojoji a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno
- Tsagerun sun kai harin ne kan sojojin rundunar Operation Hadin Kai a ƙauyen Izge da ke cikin dajin Sambisa
- A yayin harin an hallaka aƙalla sojoji guda biyu, yayin da suka samu nasarar hallaka ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari a ƙauyen Izge da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
A ƙalla wani Kyaftin da wani Korporal na rundunar sojoji na daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu a harin.

Asali: Twitter
Ƴan Boko Haram sun farmaki sojoji
Jaridar Vanguard ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na daren ranar Asabar, lokacin da wasu ƴan ta’adda ɗauke da makamai suka kai hari kan sansanin sojoji da ke Izge.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin harin, dakarun sojojin sun hallaka ƴan ta'addan Boko Haram masu yawa.
Wannan harin ya faru ne kasa da makonni biyu bayan da wasu ƴan Boko Haram ɗauke da makamai suka kai hari kan wasu sansanonin sojoji guda biyu a jihar Borno.
Bisa ga bayanan da aka tattara, ƴan ta’addan sun kai harin ne da makaman RPGs, inda suka kai farmaki kan sansanin dakarun Operation Hadin Kai da ke Izge.
Harin ya haifar da musayar wuta mai tsanani ta tsawon sa’o’i, kafin mazauna yankin, tare da tallafin ƴan banga da mafarauta, suka taimaka wajen korar ƴan ta’addan tare da sojoji.
Izge na cikin dajin Sambisa, inda take da nisan kimanin kilomita 20 Kudu maso Yamma da garin Gwoza.
Sanata Ndume ya koka kan hare-haren Boko Haram
Yayin da yake mayar da martani kan harin, Sanata Mohammed Ali Ndume, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Gwoza, ya bayyana matuƙar damuwa da yadda hare-haren Boko Haram ke ci gaba da tsananta a mazaɓarsa.

Asali: Twitter
Ya bayyana cewa ko da yake dakarun sojoji da sauran hukumomin tsaro na ƙoƙarinsu, ya kamata gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan gaggawa domin shawo kan lamarin.
Wani mazaunin Izge ya bayyana cewa:
“Mu al’ummar Izge, mun fuskanci hari daga Boko Haram da misalin karfe 1:00 na dare a lokacin da yawancinmu ke yin barci."
"Abin takaici, wani Kyaftin da Korporal daga cikin jami'an sojoji sun rasu, yayin da aka kashe ƴan ta’addan Boko Haram da dama."
“Ko da yake an hallaka da dama daga cikin ƴan ta’addan, waɗanda suka tsira sun gaggauta ɗauke gawarwakin ƴan uwan na su daga wajen da aka yi artabun."
Gwamnatin Yobe ta musanta batun ƴan Boko Haram
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Yobe ta yi bayani kan rahotannin da ke cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun tunkaro birnin Damaturu.
Gwamnatin ta bayyana rahotannin a matsayin ƙarya wacce babu ƙamshin gaskiya ko kaɗan a cikinta.
Mai ba gwamnan jihar Yobe shawara kan harkokin tsaro ya buƙaci jama'a da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da harkokinsu.
Asali: Legit.ng