Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Nasara

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Bindiga, Sun Samu Gagarumar Nasara

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka tsagerun ƴan bindiga a jihar Taraba da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Haziƙan sojojin sun hallaka miyagun ƴan bindigan ne a wani samame na musamman da suka kai musu a ƙaramar hukumar Karim Lamido
  • Dakarun sojojin sun lalata sansanoni masu yawa na ƴan bindigan tare da ƙwato makamai masu tarin yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Taraba - Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Lafiya Jama'a sun samu nasara kan ƴan bindiga a jihar Taraba.

Dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka ƴan bindiga uku, rushe sansanoninsu da dama, tare da ƙwato makamai a wani samame da suka kai musu.

Dakarun sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Taraba
Dakarun sojoji sun kashe 'yan bindiga a Taraba Hoto: @ZagazolaMakama
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka ragargaji ƴan bindiga a Taraba

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi kwanton bauna, sun hallaka 'yan kasar waje da dan sanda

Dakarun sojojin sun kai samamen ne na musamman a ranar 5 ga watan Afrilu, 2025 a ƙaramar hukumar Karim Lamido ta jihar Taraba.

Aikin ya mayar da hankali kan maɓoyar da ake zargin ƴan bindiga na ɓuya, inda dakarun suka kutsa zuwa ƙauyen Achalle suka tsaftace yankin gaba ɗaya kafin su ci gaba da matsawa zuwa ƙauyen Chibi.

Da suka isa Chibi, dakarun sun ci karo da ƴan ta’addan, waɗanda suka fara tserewa bayan da suka hango sojoji na ƙaratowa.

A fafatawar da ta biyo baya, an hallaka ƴan ta’adda uku, sannan an rusa sansanonin da suka gina.

Dakarun sun kuma ƙwato babura guda biyu, gidan harsashi guda ɗaya na bindigar AK-47, da harsasai guda 13 na musamman masu kaurin 7.62mm na musamman a wajen da aka yi artabun.

Bugu da ƙari, dakarun sun gudanar da cikakken sintiri a yankin Dutsen Zaki da Achalle, inda suka rushe sansanonin ƴan ta’adda fiye da 70 a cikin makonnin baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya fusata kan kashe kashe a Plateau, ya dauki muhimmin alkawari

Ba a ga wani motsin dan Adam ba a wannan sabon sintirin, alamar cewa nasarorin baya sun yi tasiri sosai.

Sojoji sun samu yabo

Yayin da yake jinjinawa dakarun bisa juriya da nasarar da suka samu, kwamandan 6 Brigade na sojojin Najeriya, Birgediya Janar Kingsley Chidiebere Uwa, ya sake tabbatarwa da mutanen Taraba cewa ba za a bar wata mafakar ƴan ta’adda ko masu aikata laifi a jihar ba.

Ya buƙaci al’umma da su kasance masu lura da bin doka, tare da ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum ba tare da tsoro ko fargaba ba.

Janar Uwa ya kuma ƙarfafa gwiwar jama’a da su ci gaba da samar da sahihan bayanai da suka dace cikin lokaci ga hukumomin tsaro.

Ya bayyana cewa irin wannan haɗin gwiwar na da matuƙar muhimmanci wajen tallafawa ayyukan tsaro da tabbatar da zaman lafiya da tsaron al’umma.

Ƴan bindiga sun hallaka ƴan China

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Jami'an tsaro sun cafke mai safarar kayayyaki ga rikakkun 'yan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu miyagun ƴan bindiga sun kai harin kwanton ɓauna kan ƴan ƙasar China a jihar Abia.

Ƴan bindigan sun hallaka ƴan ƙasar mutum biyu tare da wani jami'in ɗan sanda wanda yake yi musu rakiya.

Rundunar ƴan sandan wacce ta tabbatar da aukuwar harin ta ce lamarin ga auku ne lokacin da suke hanyar zuwa wurin da kamfaninsu ke aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng