'Yan Bindiga Sun Yi Kwanton Bauna, Sun Hallaka 'Yan Kasar Waje da Dan Sanda
- Wasu miyagun ƴan bindiga ɗauke da makamai sun farmaki tawagar wasu ƴan ƙasar China a jihar Abia da ke Kudancin Najeriya
- Miyagun sun farmaki mutanen ne lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin da kamfaninsu ke yin aiki
- Ƴan bindigan sun hallaka ƴan ƙasar China mutum biyu tare da wani jami'in ɗan sanda wanda ke yi musu rakiya
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Abia - Ƴan bindiga sun kashe wasu ƴan ƙasar China guda biyu da wani ɗan sanda a jihar Abia.
Rundunar ƴan sandan jihar Abia wacce ta tabbatar da harin, ta ce an kashe mutanen ne a wani harin kwanton ɓauna da ƴan bindiga suka kai musu a Uturu, ƙaramar hukumar Isuikwuato.

Asali: Twitter
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Abia, Maureen Chinaka, ta fitar a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka kashe ƴan China
Ta bayyana cewa an kai wa waɗanda lamarin ya shafa harin ne da yammacin ranar Juma’a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin da kamfanin ke aiki a Agukwu-Amaya da ke cikin ƙauyen Ndundu.
Sanarwar ta ce an kashe manajan kamfanin, Mista Quan, da abokin aikinsa Mista Cai, tare da Insfekta Audu Saidu, ɗaya daga cikin jami’an tsaron da ke musu rakiya.
Hakazalika ƴan bindigan sun yi awon gaba da bindigar Insfekta Audu Saidu bayan sun kashe shi.
Ƴan sanda sun kai ɗauki
Ta ce bayan samun rahoton, jami’an ƴan sanda, sojoji da sauran hukumomin tsaro sun ƙaddamar aikin haɗin gwiwa.
"Bayan samun rahoton, jami’an rundunar ƴan sandan jihar Abia tare da hadin gwiwar sojoji da sauran hukumomi suka fara gudanar da bincike da aikin ceto."
"Sakamakon haka, an ceto ƴan ƙasar China guda uku ba tare da rauni ba, yayin da ɗaya daga cikinsu ya samu rauni. Insfekta Uba Ahmed da aka ceto, ya samu raunin harbin bindiga a ƙafarsa."

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Jami'an tsaro sun cafke mai safarar kayayyaki ga rikakkun 'yan ta'adda
- Maureen Chinaka
Kakakin ƴan sandan ta ce an garzaya jami'in ɗan sandan tare da sauran ƴan ƙasar wajen da suka jikkata zuwa asibitin tarayya (FMC) inda ake kula da su.
Ta kuma ƙara da cewa wata tawaga ta musamman karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan ƴan sanda mai kula da ayyuka ta ziyarci wurin da lamarin ya faru a ranar Asabar.
"Ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin ƴan sanda, sojoji da mazauna yankin, an kuma ceto Insfekta Ijeagwa Friday ba tare da ko ƙwarzane ba."
- Maureen Chinaka

Asali: Twitter
Ta ce bincike na ci gaba da gudana kuma ana kokarin gano wadanda suka aikata laifin domin a gurfanar da su a gaban kuliya.
Chinaka ta bayyana cewa kwamishinan ƴan sandan jihar Abia, Danladi Isa, ya tabbatarwa da al’umma cewa za a hukunta masu laifin.
An cafke mai safarar kayayyaki ga ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an tsaro sun samu nasarar cafke wani mai safarar kayayyaki ga ƴan bindiga a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi awon gaba da matafiya a kan hanya, 'yan sanda sun dauki mataki
Jami'an tsaron na rundunar Askarawan Zamfara sun cafke wanda ake zargin ne lokacin da yake ƙoƙari kai kayan sanyi ga ƴan bindiga a cikin daji.
Wanda ake zargin mai suna Ashiru Jijji ya amsa cewa zai kai kayayyakin ne ga wasu riƙaƙƙun ƴan bindiga masu suna Ali da Inuwa.
Asali: Legit.ng