Abin da Mazauna Kano Ke Cewa da ’Yan Sanda Suka Gayyaci Sanusi II zuwa Abuja
- Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II zai gana da Sufeto Janar na ‘yan sanda a Abuja ranar Talata
- An gayyaci Sanusi ne kan wani al’amari da ya faru a lokacin bukukuwan Sallah a Kano
- Wasu mazauna Kano sun soki wannan gayyata, suna cewa yana da nufin tayar da rikici a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu mazauna Kano sun yi magana kan gayyatar Sarki Sanusi II da yan sanda suka yi zuwa birnin Abuja.
Wasu daga cikinsu sun nuna rashin jin dadinsu kan wannan gayyata, suna ganin wata dabara ce ta kifar da Sarki Sanusi II daga sarauta.

Asali: Facebook
Takardar gayyatar Sarki Sanusi II zuwa Abuja
Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, zai gana da Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, a babban hedkwatar ‘yan sanda dake Abuja ranar Talata, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An gayyaci Sanusi ne ta wasika da aka rubuta a ranar 4 ga watan Afrilu, wadda Kwamishinan ‘yan sanda (Ayyuka), Olajide Ibitoye, ya sanya wa hannu.
A cewar wasikar, an bukaci Sanusi da ya bayyana a hedkwatar sashin leken asirin ‘yan sanda dake Abuja karfe goma na safe.

Asali: UGC
An rasa rai yayin bikin sallah a Kano
Rahotanni sun ce gayyatar na da nasaba da wani lamari da ya faru a lokacin Sallah a Kano, kodayake ‘yan sanda ba su bayyana cikakken bayani ba.
Majiyoyi daban-daban sun tabbatar da cewa hakan yana da alaka da jerin gwanon motoci da aka yi duk da haramta shi daga wajen ‘yan sanda.
An samu rikici da asarar rai sakamakon wannan jerin gwanon da aka gudanar, wanda hakan ya kara tayar da hankali a Kano.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta kama wani Usman Sagiru a ranar 30 ga watan Maris, 2025, bisa zargin kashe wani da hari kan ‘yan sintiri.

Kara karanta wannan
Galadima: Aminu Ado na karbar ta'aziyya a fadarsa, sarakuna, 'yan siyasa na tururuwa
Martanin wasu yan Kano kan gayyatar Sanusi II
Mafi yawan wadanda suka yi magana kan lamarin sun bayyana rashin jin kan abin da suka kira wani shiri na lalata zaman lafiyar Kano.
Suka ce hakan wani shiri ne na neman hanyar sanya dokar ta-baci a jihar kamar yadda aka yi a Rivers da ke Kudancin Najeriya.
Wani mazaunin Kano da ya bukaci boye sunansa ya ce:
“Muna gargadi kan wadannan dabaru na haddasa rikici a Kano domin a samu damar sanya dokar ta baci.”
Har ila yau, wani ya bayyana cewa:
“Abin da ya faru ranar Sallah ba hawa ba ne, sai dai tafiyar Sarkin daga masallaci zuwa fadarsa.”
Mazauna Kano sun yi kira ga ‘yan sanda da kada su lalata zaman lafiya da ke Kano da wata hujja maras karfi da za ta tayar da hankali.
Sanusi II ya yabawa Abba Kabir Yusuf
Kun ji cewa Mai Martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaba da yake zuba wa a Kano.
Sanusi II ya ce ƙoƙarin da gwamnan ke yi na inganta harkokin ilimi, kiwon lafiya noma da tsaro a jihar Kano ya cancanci a jinjina masa.
Gwamna Abba Kabir ya jaddada godiya ga mai martaba sarkin bisa jagorancin da yake yi da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a Kano.
Asali: Legit.ng