Kwana Ya Kare: Shugaban Jam'iyyar APC Ya Rasu cikin Wani Yanayin Ban Al'ajabi

Kwana Ya Kare: Shugaban Jam'iyyar APC Ya Rasu cikin Wani Yanayin Ban Al'ajabi

  • An shiga jimami da ban al'ajabi a jihar Kogi bayan rasuwar shugaban jam'iyyar APC na shiyyar Kogi ta Gabas
  • Suleiman Omika Mohammed ya rasu ne lokacin da yake cikin hutawa a gidansa da ke birnin Lokoja, babban birnin jihar
  • Mataimakin gwamnan Kogi, Joel Salifu ya yi ta'aziyya kan wannan babban rashin da APC ta yi na ɗaya daga cikin shugabanninta

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - Shugaban jam’iyyar APC na shiyyar Kogi ta Gabas, Suleiman Omika Mohammed, ya rasu yana da shekara 45.

An ruwaito cewa Omika Mohammed, wanda ya maye gurbin Nasir Agbodu a matsayin shugaban jam'iyyar ƴan watanni da suka gabata, ya rasu cikin yanayin ban al'ajabi.

Shugaban APC a Kogi ya rasu
Shugaban APC a shiyyar Kogi ta Gabas ya rasu Hoto: Idris HK
Asali: Facebook

Jam'iyyar APC ta yi babban rashi a Kogi

Tashar Channels tv ta ce shugaban APC na jihar Kogi, Abdullahi Bello, ne ya tabbatar da rasuwarsa ta wayar tarho.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, mai magana da yawun APC ya rasu a ƙasar waje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, mataimakin gwamnan jihar, Joel Oyibo, ne ya sanar da shi wannan mummunan labari, a lokacin da yake a birnin Legas don yin ta’aziyya ga shugaban APC na jihar Legas da ya rasa matarsa.

A cewar ƴan uwansa, marigayin yana hutawa ne a gidansa da ke Lokoja, babban birnin jihar, lokacin da ya fara kururuwar neman agaji yana cewa yana jin karfin jikinsa na raguwa, sai ya faɗi nan take ya rasu.

Mataimakin gwamna ya yi ta'aziyya

A gefe guda kuma, mataimakin gwamnan jihar Kogi, Joel Salifu, ya bayyana matukar alhini da baƙin ciki kan rasuwar bazata ta Suleiman Omika Mohammed.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na mataimakin gwamnan, Unubi Emmanuel, ya fitar, inda ya ce mataimakin gwamnan ya bayyana mutuwar a matsayin abin firgici da girgiza zuciya.

Shugaban APC a Kogi ya rasu
Alhaji Suleiman Omika Mohammed ya rasu yana da shekara 45 Hoto: Idris HK
Asali: Facebook

Sanarwar ta bayyana marigayin Omika Mohammed a matsayin mutum mai halin kirki wanda ya yi wa jam’iyyar hidima da gaskiya kuma ya taka rawar gani wajen nasarar APC a yankin, yana mai cewa rashinsa zai bar babban gibi a cikin jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

Mataimakin gwamnan ya yi addu'ar Allah da Ya ji kansa, Ya gafarta masa, kuma Ya ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashi da ba za a iya maye gurbinsa ba.

Marigayi Omika Mohammed, wanda aka riga aka binne bisa tanadin shari'ar Musulunci, an haife shi ne a ranar 1 ga watan Oktoba, 1980 a garin Oduh, ƙaramar hukumar Dekina, jihar Kogi.

Marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya da ƴaƴa shida.

Kakakin jam'iyyar APC a Ogun ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa mai magana da yawun bakin jam'iyyar APC mai mulki a jihar Ogun, Alhaji Abdulraheem Tunde Oladunjoye, ya koma ga mahaliccinsa.

Marigayin wanda ya kasance mai ba gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, shawara kan harkokin yaɗa labarai, ya rasu ne ƙasar waje.

Alhaji Abɗulraheem ya yi bankwana da duniya ne bayan ya yi fama da jinyar rashin lafiya wacce ba a bayyana ko wace iri ba ce.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng