An Tafi da Limamin da Ya Yi Batanci ga Dr Dutsen Tanshi bayan an so Masa Duka
- Rundunar ’yan sandan Bauchi ta fara bincike kan wani rikici da ya barke a masallacin Galli a Jahun bayan limamin masallacin ya yi wasu kalamai
- An ce limamin, Ahmad Isa Jaja, ya zagi marigayi Malam Idris Abdulazeez Dutsen-Tanshi a hudubarsa ta Juma’a, lamarin da ya fusata mutanen unguwar
- Kwamishinan ’yan sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umurci sashen leken asiri da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin, tare da jan kunnen malamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta bayyana cewa tana gudanar da cikakken bincike kan rikicin da ya barke a masallacin Galli da ke unguwar Jahun a cikin garin Bauchi.
An samu tashin hankali ne bayan limamin masallacin ya yi mummunar magana kan Dr Dutsen Tanshi a hudubar Juma’ar ranar 4 ga Afrilu, 2025.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan lamarin ne a cikin wani sako da rundunar 'yan sandan jihar ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
’Yan sanda sun ce wani mai kishin kasa ne ya kai rahoton cewa limamin masallacin, Ahmad Isa Jaja, ya furta kalaman batanci ga marigayi Malam Idris Dutsen-Tanshi a yayin hudubarsa.
Kalamai sun jawo fushin mabiyan marigayin, suka taru a masallacin domin bayyana bacin ransu kan furucin da limamin ya yi, lamarin da ya janyo dagulewar al’amura.
An tafi da limamin domin tabbatar da tsaro
Kwamishinan ’yan sandan jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, ya aika jami’an kwantar da tarzoma karkashin jagorancin DPO na Dutsen-Tanshi domin shawo kan lamarin.
Jami’an sun yi nasarar shawo kan lamarin cikin kwanciyar hankali ba tare da tashin wata hatsaniya ba.
Tribune ta wallafa cewa an dauki limamin zuwa wani waje domin kare lafiyarsa da kuma tabbatar da doka da oda.
Bayan haka ne CP Sani-Omolori ya umurci sashen leken asiri (SID) da su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin da daukar mataki bisa shari’a.

Asali: Twitter
Kwamishinan 'yan sanda ya gargadi malamai
A cikin sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, kwamishinan ya gargadi malamai.
Ya jaddada bukatar malamai su rika amfani da hudubarsu wajen wanzar da zaman lafiya da hadin kai a cikin al’umma.
A cewarsa:
“Yayin da malamai ke da ‘yancin fadin albarkacin baki, ya kamata su guji amfani da mimbarin addini wajen zagin mutane ko cin mutuncinsu.
"Yin hakan na iya haddasa rikici da rarrabuwar kai a tsakanin jama’a.”
Kwamishinan ya kara da cewa malamai na da muhimmiyar rawa wajen ciyar da al’umma gaba da kuma tabbatar da zaman lafiya, don haka ya kamata su nuna girmamawa ga doka da hukuma.
Rayuwar Dr. Idris Abdulazeez Dutsen-Tanshi a takaice
Dr. Idris Abdulazeez Dutsen-Tanshi, ɗaya ne daga cikin fitattun malamai a jihar Bauchi da ma Arewacin Najeriya gaba ɗaya, kuma ya kasance masani a fannin ilimin addinin Musulunci.
An fi saninsa da karatuttuka masu zurfi da gamsassun hujjoji, wanda hakan ya janyo masa girmamawa da goyon baya daga dubban matasa da magoya baya.
An haife shi a unguwar Dutsen-Tanshi da ke Bauchi, inda ya taso cikin kulawar malamai da masana addini.
Ya yi karatunsa na addini a gida da kuma kasashen waje, inda ya samu shaidar digiri da kuma digirgir (PhD) a ilimin shari’ar Musulunci.
Ya yi fice wajen gabatar da tafsiri, karantarwa, da kuma hudubobi da ke janyo hankalin jama’a bisa tsarin da ya dace da addini da zaman lafiya.
Dr. Idris ya kafa majalisu daban-daban, ciki har da Dutsen Tanshi Majlis, inda ake gudanar da karatu da wa’azi akai-akai.
A matsayinsa na jagora, ya kasance mai tsayawa akan gaskiya da fadakarwa, lamarin da ya sa ya samu karbuwa sosai, amma kuma hakan ya janyo masa sabani da wasu ’yan ra’ayin da ya saba da nasa.

Kara karanta wannan
Hotuna: Yadda musulmi suka yi cikar ƙwari a wurin janazar Sheikh Idris Dutsen Tanshi
Marigayi Dr. Idris ya rasu ne a cikin 2024, kuma ana ci gaba da tunawa da irin gudunmawarsa ga addini da al’umma.
Wasiyoyin Dr. Idris Dutsen Tanshi
A wani rahoton, kun ji cewa a ranar Juma'a aka yi jana'izar Dr Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi a jihar Bauchi.
Malamin da ya shahara da wa'azi ya yi wasiyoyi da dama ciki har da hana masa zaman makoki bayan ya mutu.
Haka zalika marigayin ya yi wasiyar a nisanci yin turereniya wajen daukar gawarsa da kuma shiga makabarta da takalmi yayin birne shi.
Salisu Ibrahim ya fadada wannan labarin.
Asali: Legit.ng