An Yi Albishir da Saukar Kudin Sufuri da Kayayyaki bayan Karyewar Farashin Mai
- Farashin gangar danyen mai ya fadi daga $69.90 zuwa $65 a kasuwannin duniya, wanda hakan zai iya haifar da rage farashin mai
- 'Yan kasuwa sun ce idan wannan yanayi ya ci gaba, ana sa ran za a rage kudin sufuri, kayayyaki da sauransu a fadin kasar nan
- Kungiyar OPEC ta amince da kara yawan hakar mai daga watan Mayun 2025, lamarin da zai kara haddasa faduwar farashin mai a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yayin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fadi, akwai yiwuwar farashin fetur zai ragu a Najeriya.
An bayyana cewa lamarin zai saukaka wa ‘yan kasar wajen kashe kudin sufuri, sayen kayayyaki da sauransu.

Asali: Getty Images
Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa gangar danyen mai da ake amfani da shi a matsayin ma’aunin farashin mai a duniya, ya sauka daga $69.90 zuwa $65.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin abubuwan da suka haddasa faduwar farashin har da sanarwar shugaban Amurka Donald Trump kan karin haraji da kuma matakin OPEC na kara yawan man da ake hako wa.
'Yan kasuwa sun fara rage farashin mai
Rahotanni sun tabbatar da cewa farashin fetur a wasu matatun rarraba mai irin su Mainland, A.Y.M da Ever ya ragu zuwa N918 da N919 daga N920 a baya.
Haka kuma, matatun Prudent, Eterna da Soroman sun rage farashin zuwa N912, N897 da N915 daga farashin da suka fi haka a baya.
Wannan sauyi ya nuna yiwuwar rage farashin da masu sayar da fetur ke bukatar yi a matakan tashar man fetur nan ba da jimawa ba.
Rahotanni sun nuna cewa masu sayar da fetur za su iya rage farashin a matakin gidan mai idan wannan yanayi ya dore.

Asali: Getty Images
Ana sa ran rage farashin kaya da sufuri

Kara karanta wannan
An gano dalilin da ya sa farashin abinci ya kara yin kasa warwas a yankunan Arewa
Shugaban kungiyar masu tashoshin man fetur, Billy Gillis-Harry, ya bayyana cewa wannan saukin farashi zai iya haifar da sauki ga ‘yan Najeriya wajen biyan kudin kaya da ayyuka.
A wata hira da aka yi da shi, ya ce:
“Idan wannan sauyi ya dore, babu shakka farashin kayayyaki da sufuri zai sauka, wanda zai amfanar da talakawa matuka.”
Ya kara da cewa hakan zai taimaka wajen rage radadin hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi a kasar.
OPEC za ta kara yawan hako man fetur
Kungiyar OPEC ta sanar da karin yawan hako mai daga kasashe guda takwas da suka hada da Saudiyya, Rasha, Iraki, UAE, Kuwait, Kazakhstan, Aljeriya da Oman.
Bayanai sun tabbatar da cewa hakan zai kara yawan mai da ake hakowa da ganga 411,000 a rana daga Mayun 2025, wanda zai taimaka wajen daidaita farashin mai a duniya.
NNPCL ya kara kudin litar man fetur

Kara karanta wannan
Matashi ya mutu, 1 kuma rai a hannun Allah bayan artabu kan budurwa a bikin sallah
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya kara farashin mai a wasu yankunan kasar nan.
Legit ta rahoto cewa kamfanin NNPCL ya kara kudin fetur ne a wasu gidajen mai a birnin tarayya Abuja da Legas.
Bugu da kari, an samu karin kudin ne 'yan sa'o'i bayan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban NNPCL, Mele Kyari.
Asali: Legit.ng