Kyawun Alkawari: Barau Ya Raba Miliyoyi fa Iyalan Hausawan da aka Kashe a Edo
- Sanata Barau Jibrin ya cika alkawarin da ya dauka na bai wa iyalan 'yan farauta 16 da aka kashe a Uromi, jihar Edo, tallafin N1m
- Wakilan ofishinsa sun zagaya gida-gida a Bunkure, Rano da Kibiya domin kai kudin a hannun iyalan mamatan kai tsaye
- Barau ya ce taimakon kudin alama ce da ta nuna cewa yana tare da jama’arsa a kowane hali, ciki har da lokacin bakin ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin, ya kaddamar da raba tallafin N1m ga iyalan mafarauta 16 da suka rasa rayukansu a harin Uromi.
Sanatan ya sanar da cewa zai raba tallafin ne a ranar Laraba yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai Bunkure, jihar Kano.

Asali: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka raba tallafin ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafin Sanata Barau na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Barau ya bayyana cewa yana jin zafin abin da ya faru da kuma ya ce zai tsaya tsayin daka domin ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan aika-aika.
Tawaga daga ofishin Sanata Barau karkashin jagorancin Farfesa Muhammad Ibn Abdullah tare da Hon. Yusuf Tumfafi ne suka kai kudin gida-gida.
Barau Jibrin ya cika alkawarin tallafin N1m
Tawagar ta fara ne daga karamar hukumar Bunkure, inda suka gana da iyalan wadanda abin ya shafa.
Daga nan suka zarce zuwa Rano da Kibiya, domin ci gaba da isar da sakon ta’aziyya da kuma kudin tallafi.
A cewar sanarwar, an mika kudin kai tsaye ga matan mamatan, domin a tabbatar da cewa iyalan sun karɓi tallafin ba tare da wata tangarda ba.
Wakilan Barau sun ce hakan ya nuna yadda yake bai wa lamuran jama’a muhimmanci, musamman a lokacin da suka fi bukatar kulawa.

Asali: Facebook
A cewar Barau, raba tallafin alama ce ta cewa gwamnati da wakilan al’umma ba za su bar jama’a su fuskanci irin wannan hali cikin kadaici ba.
Barau ya ce zai tabbatar da adalci
Sanata Barau ya kara da cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin cewa wadanda suka aikata kisan gillar sun fuskanci hukunci.
A cewarsa:
“Za mu tabbatar da cewa an hukunta masu hannu a wannan aika-aika, Insha Allah.”
Ya yi addu’ar Allah ya jiƙan waɗanda suka mutu, ya bai wa iyalansu hakuri da juriya, tare da warkar da waɗanda suka jikkata a harin.
Bayan rabon tallafin, hankulan al'umma za su koma kan ganin matakin da za a dauka kan wadanda aka kama bayan kai harin.
APC ta zargi PDP kan rikicin jihar Edo
A wani makamancin rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar Edo ta zargi PDP ta janyo rikici da tashin hankali.
Shugaban APC na jihar ya ce PDP na son tayar da rikici a Edo domin jawo hankalin shugaban kasa ya sanya dokar ta baci.
A karkashin haka shugaban jam'iyyar ya ce PDP ce ta kitsa kashe Hausawa 16 da ke dawowa gida hutun sallah a yankin Uromi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng