Abubuwa 5 da za a Tuna Sheikh Idris Dutsen Tanshi da Su bayan Mutuwarsa

Abubuwa 5 da za a Tuna Sheikh Idris Dutsen Tanshi da Su bayan Mutuwarsa

  • Marigayi Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi ya yi gwagwarmaya wajen jaddada abubuwa da dama da ba za a manta da shi ba
  • Ya kasance cikin malaman addinin da suka fafata da 'yan ta'addar Boko Haram, har ya yi mukabala da Muhammad Yusuf
  • Ya kasance mutum mai tsayawa kan gaskiya, lamarin da ya jawo masa sabani da gwamnatoci har ya yi hijira a 2024

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Sheikh Dr Idris Abdul'azeez Dutsen Tanshi malami ne da ya shahara a Najeriya da kuma wasu sassan duniya saboda tsayuwar dakansa.

Malamin ya yi gwagwarmaya a fagen ilimi da wa'azi, tare da fuskantar kalubale iri-iri a rayuwarsa.

Dr Idris
Dr Idris Dutsen Tanshi ya rasu bayan ya sha gwagwarmaya a harkar malanta. Hoto: Dusten Tanshi Majlis Bauchi
Asali: Facebook

A wannan rahoton, mun tattaro muku wasu abubuwa 5 da za su sanya a rika tunawa da shi bayan rasuwarsa.

Kara karanta wannan

Bayan jana'izar Dr Idris, wani limami ya ja sallar Juma'a a masallacin Dutsen Tanshi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwagwarmayar Abdulaziz Idris Dutsen Tanshi

1. Yawan fadakarwa kan Tauhidi

Sheikh Dr Idris Abdulazeez ya shahara sosai da wa’azin tauhidi, wanda ya sa wasu ke kiransa da "Dr Tauhid."

Marigayin ya kasance yana kira ga mutane su bauta wa Allah Shi kaɗai ba tare da haɗa wani da Shi ba.

Sheikh Lawal Shuaibu Triumph ya bayyana cewa shagala da kira zuwa ga tauhidi ne ya sa wasu ke ganin wa’azin Sheikh Dr Idris yana da zafi.

A cikin wani bidiyo da aka wallafa a Facebook, ya ce:

"Duk mai kira zuwa tauhidi, dole a ga yana da tsanani a magana."

2. Fafatawa da 'yan Boko Haram

A lokacin da kungiyar Boko Haram ta fara tashe, Dr Idris ya kasance cikin malaman da suka bijire wa akidarsu.

Sheikh Dutsen Tanshi ya fafata da jagoran kungiyar a lokacin, Muhammad Yusuf, a wata mukabala da suka yi.

Kara karanta wannan

Yadda Dutsen Tanshi ya dawo Najeriya daga Indiya duk da tsananin rashin lafiya

Mukabalar ta nuna irin munanan ayyukan da kungiyar ke aikatawa, wanda hakan ya zama wata shaida da ke nisantar da Dr Idris daga zargin goyon bayan ta’addanci.

3. Maganar ceton Annabi (SAW)

Sheikh Idris Dusten Tanshi ya sha nanata cewa a ganinsa ceton Annabi (SAW) ya fi ceton kowa a ranar alkiyama.

A wani bidiyonsa da aka wallafa a X, ya ce:

“Ko da mahaifiyata za ta yi ceto, na fi son ceton Annabi (SAW).”

Ya tabbatar da cewa Annabi (SAW) zai yi ceto ga al’ummarsa a ranar Lahira, kuma hakan ne ya sa yake dagewa wajen bin sunnah.

A bangaren neman taimako a duniya, malamin ya ce bai neman taimakon kowa sai Allah, sai dai an yi wa wannan zancen mummanar fahimta.

4. Sabani da gwamnoni da gudun hijira

Sheikh Idris ya sha samun sabani da gwamnonin jihar Bauchi da kuma wasu shugabanni a Najeriya.

Kara karanta wannan

'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi

A wata hira da ya yi da DW Hausa, ya bayyana yadda ‘yan siyasa ke juya wa malamai baya idan sun samu mulki bayan neman addu’a daga gare su.

A cewarsa, akwai wani gwamna da ya roƙi addu’arsa kafin zaɓe, amma bayan nasara sai ya jefa shi a kurkuku a Abuja.

A shekarar 2024, sakamakon sabani da gwamnatin Bauchi, Sheikh Dr Idris ya yi hijira zuwa wata ƙasa a Afrika kafin daga bisani ya dawo Najeriya.

5. Gwagwarmayar malanta a Najeriya

Sheikh Idris Abdulazeez ya kasance malami mai tsayawa kan abin da ya yi imani da shi ko da kowa zai juya masa baya.

A wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, Dr Jalo Jalingo ya bayyana shi a matsayin mutum wanda ba ya tsoron fadin gaskiya, komai dacinta.

Rayuwarsa ta kasance cike da gwagwarmaya, kuma mutane za su ci gaba da tunawa da shi saboda irin kokarinsa wajen yada tauhidi da kare addini.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Idris Dutsen Tanshi ya fada kan rashin lafiya da mutuwa kafin ya Cika

A ranar Juma'a, 4 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana'iza tare da birne Dr Idris Dutsen Tanshi a jihar Bauchi.

Dr Jalo
Dr Jalo ya yi ta'aziyyar rasuwar Dr Idris Dutsen Tanshi. Hoto: Ibrahim Jalo Jalingo
Asali: Depositphotos

Legit ta tattauna da Khadija Dahiru

Wata dalibar ilimi a jihar Bauchi, Khadija Dahiru da aka fi san da Ummu Shaikhil Islam ta bayyana wa Legit cewa akwai abubuwa da dama da za su tuna da malamin da su.

Ummu Shaikhil Islam ta ce:

"Abin da muka sani a kan shi ya rayu ne a kan sadaukarwa game da addini. Ba shi da nuku-nuku ko fuska biyu.
"Abin da zan rika tunawa da shi, shi ne tun da nake a masallacin shi nake sallar Idi. Mun ji kaikayi a ran mu da ba shi ya mana sallar Idi bana ba.
"Duk lokacin da Idi ya zo, zan rika tuna wa da shi. Mutum ne mai yawan kyauta, kyauta kuma sosai."

Wasiyoyin Dr Dutsen Tanshi guda 5

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Allah ya karbi rayuwar malamin Musulunci, Idris Dutsen Tanshi

A wani rahoton, kun ji cewa Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi ya bar wasu wasiyoyi kafin rasuwarsa.

Daga cikin abubuwan da malamin ya yi wasiya da su akwai nisantar masa zaman makoki bayan ya mutu.

Haka zalika Dr Idris ya yi wasiya da kada a yi turereniya wajen daukar gawarsa kuma kada a shiga makabarta da takalmi yayin birne shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng