Bayan Rasuwar Sheikh Idris Dutsen Tanshi, Allah Ya Ɗauki Rayuwar Jigo a Najeriya
- Allah ya yi wa tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa kuma Seriki Musulumi na Yarbawa, Yekinni Adeojo rasuwa da safiyar Juma'a
- Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi ta'aziyyar wannan rashi tare da addu'ar Allah Ya ba iyalan Alhaji Adeojo hakurin jure kaddarar
- Marigayin dai shi ne Seriki Musulumi na ƙasar Yarbawa kuma babban ɗan kasuwa wanda ya taɓa neman zama gwamnan jihar Oyo
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ibadan, Jihar Oyo - Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa mai kula da shiyyar Kudancin Najeriya, Alhaji Yekini Ayoade Adeojo, ya rasu.
Marigayin ya riga mu gidan gaskiya ne a safiyar ranar Juma’a a garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.

Asali: Facebook
Rahoton jaridar Leadership ya tattaro cewa Alhaji Adeojo sananne ne a fagen siyasa da harkokin kasuwanci, musamman a jihar Oyo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa a siyasar jihar da ƙasa baki ɗaya.
Seriki Musulumi na Yarbawa ya rasu
Shi ke rike da sarautar Seriki Musulumi na Yankin Yarbawa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar PDP a jihar Oyo.
A shekarar 1999, Adeojo ya tsaya takarar gwamna a ƙarƙashin PDP, amma ya sha kaye a hannun marigayi Alhaji Lamidi Adesina na jam’iyyar AD.
Duk da rashin nasarar da ya fuskanta a zaɓen, ya cigaba da zama ɗaya daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP a jihar Oyo.
Baya ga siyasa, marigayin ya kasance mashahurin ɗan kasuwa wanda ya taka rawa kuma ya ba da gudummuwa wajen bunƙasa tattalin arzikin yankinsa.
Har ila yau, yana da babban matsayi a cikin al’umma, inda jama'a ke girmama shi a matsayin jagora mai kishin ci gaban mutanensa.
Alhaji Yekinni Adeojo shi ne mahaifin Hon. Sheriff Aderemi Adeojo, wanda ke rike da mukamin shugaban ƙaramar hukumar Ido a Jihar Oyo.
A rahotanni da suka fito daga iyalansa, za a yi jana’izar marigayin a ranar Juma’a a Ibadan bisa koyarwa addinin Musulunci.

Asali: Facebook
Gwamna Makinde ya yi ta'aziyyar Adeojo
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana jimami kan rasuwar jigo a jam’iyyar PDP kuma Seriki Musulumi na Yankin Yarbawa, Alhaji Yekini Ayoade Adeojo.
Makinde ya yi ta’aziyya ga iyalan marigayin, ya roƙi Allah Ya ba su ƙarfin juriya kan wannan babban rashi. Haka kuma, ya yi ta’aziyya ga jam’iyyar PDP a jihar Oyo, cewar The Nation.
A cikin saƙonsa, gwamnan ya ce:
“Na samu labarin rasuwar ubangidana, Pa Yekini Adeojo. Ina mika ta’aziyyata ga iyalan Alhaji Adeojo, jam’iyyar PDP a Oyo, da kuma daukacin jama’ar jihar bisa wannan babban rashi.
An yi janazar Dutsen Tanshi a Bauchi
A wani labarin, kun ji cewa dubban mutane sun halarci janazar Marigayi Sheikh Idris Dutsen Tanshi, wanda aka yi yau Juma'a a jihar Bauchi.
Hotunan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yada jama'a suka baibaiye filin da aka yi wa malamin sallah kamar yadda addinin musulunci ya tanada.
Tun bayan samun labarin rasuwar malamin, mutane suka fara aika sakon ta'aziyya tare da rokon Allah ya gafarta masa kura-kuransa.
Asali: Legit.ng