Yadda Dutsen Tanshi Ya Dawo Najeriya daga Indiya duk da Tsananin Rashin Lafiya
- Marigayi Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya ƙi zaman jinya a Indiya, yana mai cewa zai fi so ya rasu tare da Musulmai a Najeriya
- Wani dan siyasa a jihar Bauchi ya ce a shekarar 2019, Dr Idris ya bayyana burinsa na cigaba da samun ladan sallah ta hanyar gina masallatai
- Biyo bayan sanar da rasuwarsa a daren ranar Juma'a, al'ummar Musulmi a fadin Najeriya na cigaba da masa addu'ar samun rahama
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi - Wani dan siyasa a jihar Bauchi, Musa Azare ya fadi halin da Dr Idris Dutsen Tanshi ya shiga lokacin da rashin lafiyarsa ya yi tsanani.
A ranar Litinin, 31 ga watan Maris Musa Azare ya nemi makusancin marigayi Sheikh Dr Idris Abdul'azeez domin aika gaisuwa da addu'ar samun lafiya.

Kara karanta wannan
Hotuna: Yadda musulmi suka yi cikar ƙwari a wurin janazar Sheikh Idris Dutsen Tanshi

Asali: Facebook
A sakon da ya wallafa a Facebook, mutumin ya shaida masa cewa jikin Sheikh Dutsen Tanshi ya tsananta, yana bukatar addu’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutumin ya ƙara da cewa a lokacin da Sheikh Idris ya je asibiti a ƙasar Indiya, likitoci sun bukace shi da ya ci gaba da zama a can don ci gaba da shan magunguna da shirin tiyata.
Malaman asibitin sun nemi ya sha magani ta yadda zai samu lafiyar yi masa aiki a can.
Dalilin kin zaman Idris Dutsen Tanshi a Indiya
Sheikh Idris Abdul'aziz ya bayyana cewa likitocin da ke duba shi a Indiya sun bukaci da ya zauna saboda duba lafiyarsa da kuma ci gaba da shan wasu magunguna kafin ayi masa tiyata.
Sai dai Shehin ya ƙi amincewa, yana mai cewa zai fi so ya koma gida Najeriya, domin idan mutuwa ta zo, ta riske shi a cikin iyalai da ‘yan uwa Musulmai.

Kara karanta wannan
'An yi babban rashi,' Atiku ya yi magana da jin labarin rasuwar Sheikh Dutsen Tanshi
A cewarsa, idan ya warke, zai koma domin yin tiyata. Idan kuma mutuwa ta riske shi kafin ya sake tafiya, to ya fi son ya mutu a cikin Musulmai a Najeriya.
Wannan ne ya sa ya koma gida Najeriya kuma Allah ya karbi rayuwarsa a daren Juma'a, 3 ga Maris a jihar Bauchi.
Yadda Idris Dutsen Tanshi ya gina masallatai
A shekarar 2019, yayin ziyarar da Musa Azare ya kai masa a gidansa, Dr Idris ya bayyana cewa yana son ko bayan ya mutu, Allah Ya cigaba da ba shi ladan sallah kamar yana raye.
Musa Azare ya bayyana cewa Dr Idris ya ce:
“Wannan ne dalilin da ya sa duk lokacin da na samu dama, sai na gina masallaci.”
Ya ƙara da cewa ya gina masallatai sama da 10 a cikin garin Bauchi da kewaye domin ci gaba da samun ladan ibada bayan ransa.

Kara karanta wannan
Abubuwan da Idris Dutsen Tanshi ya fada kan rashin lafiya da mutuwa kafin ya Cika

Asali: Twitter
Sheikh Bala Lau ya yi ta'aziyyar Dr Idris
A wani rahoton, kun ji cewa manyan malaman Najeriya na cigaba da alhinin rasuwar Sheikh Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.
Shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewa rashin Dr Idris Dutsen Tanshi rashi ne ga al'ummar Musulmi.
Haka zalika Sheikh Bala Lau ya bayyana cewa mutuwa rigar kowa ce, saboda haka ya ba iyalai da daliban malamin hakurin rashin.
Asali: Legit.ng