'A Tabbatar da Adalci Duniya Ta Gani,' Abba Gida Gida kan Kisan Uromi

'A Tabbatar da Adalci Duniya Ta Gani,' Abba Gida Gida kan Kisan Uromi

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gode wa Bola Tinubu da gwamnan Edo kan gaggawar shiga tsakani kan kisan Hausawa
  • Gwamnatin jihar Kano ta bukaci a gurfanar da wadanda ake zargi a fili domin tabbatar da adalci ga iyalan da abin ya shafa
  • An yaba da kokarin gwamnatin Edo wajen tuntubar al’ummar Hausa da kuma alkawarin bayar da diyya ba tare da jinkiri ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT AbujaGwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba da matakan da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo suka dauka kan kisan Edo.

Ya bayyana jin dadi a kan matakan gaggawar da suka yi wajen shiga tsakani bayan kisan gillar da aka yi wa ’yan asalin Kano 16 a garin Uromi da ke Jihar Edo

Kara karanta wannan

A karon farko, gwamna Fubara ya fadi halin da ya shiga bayan dokar ta baci a Ribas

Gwamna
Abba ya yabi gwamnatin Tinubu kan kisan Edo Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Wannan godiya na kunshe ne cikin wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya wallafa a Facebook.

Ya yaba da ziyarar gaggawa da wakilan gwamnatin tarayya da na Jihar Edo suka kai, tana mai cewa hakan alamar nuna damuwa ce ga jama'a Toronke.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya shiga alhinin kisan Hausawa

Jaridar Punch ta ruwaito cewa Gwamna Abba, ya ce ya yi jimami da alhini kan wannan aika-aika, tare da maimaita kiran da ya saba yi na neman adalci.

Ya jaddada muhimmancin aiwatar da sahihin tsari na shari’a, wanda ya haɗa da fito da wadanda ake zargi a fili, domin tabbatar wa da al’umma cewa an ɗauki matakin da ya dace.

Ya ce:

“Mun yaba da matakan da aka ɗauka zuwa yanzu, amma adalci ba wai kawai a fada ba me, sai an nuna an yi shi.
"Mutanen Kano, da ma duk ’yan Najeriya, suna da haƙƙin ganin waɗanda suka aikata wannan kisan ƙare dangi an gurfanar da su a bainar jama'a.”

Kara karanta wannan

Abin da Sarki Sanusi II ya faɗa wa Gwamma Abba bayan ya yi hawan Sallah a Kano

Kano: Abba ya yabi gwamnan jihar Edo

Gwamna Abba ya kuma yaba da yadda gwamna Okpebholo ya tuntubi al’ummar Hausa da ke jihar Edo domin dakile yiwuwar ƙarin rikice-rikice.

Ya jinjinawa ƙudurinsa na taimakawa iyalan da lamarin ya shafa da diyya, tare da jaddada bukatar gudanar da wannan aiki cikin gaggawa da gaskiya.

Gwamna
Gwaman Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Gwamnan na Kano ya kuma nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa umarnin da ya bai wa hukumomin tsaro na kamo wadanda ke da hannu cikin kisan, tare da gurfanar da su ba tare da ɓata lokaci ba.

Ya ce wannan mataki ya nuna cewa gwamnatin tarayya na da cikakken ƙuduri wajen kare rayuka da dukiyoyin ’yan Najeriya.

Kano ta yabi kokarin gwamnatin Edo

A wani ɓangaren kuma, mutanen garin Toranke sun bayyana godiyarsu ga jajircewar da gwamnatin jihar Edo da ta tarayya suka nuna wajen shawo kan lamarin.

Gwamnonin Kano da Edo sun sha alwashin tabbatar da gudanar da shari’a cikin gaskiya da adalci, da kuma ɗaukar matakan hana maimaita rin wannan mummunan al’amari a gaba.

Kara karanta wannan

Bidiyon Abba Kabir ya jagoranci Okpebholo zuwa ga iyalan wadanda suka mutu a Edo

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa za ta ci gaba da bin diddigin lamarin don tabbatar da cewa iyalan waɗanda abin ya shafa sun samu diyya da dukkanin tallafin da ya dace.

An ba gwamnati shawara kan kisan Edo

A tattaunarsa da Legit, tsohon kwamandan Rundunar Hadin Gwiwa (JTF), Dr. Isma’il Tanko Birnin Kudu ya bayyana kisan da aka yi a matsayin mummunan aikin ta'addanci.

Dr. Tanko ya jaddada muhimmancin gabatar da shari'a a fili ga wadanda ke da alhakin kisan mafarautan da ba su ji ba, ba su gani ba.

Ya ce:

"Shari'a ta gaskiya a fili ga wadanda suka aikata kisan Uromi ne kawai zai dakatar da bukatar fansa."

Haka zalika, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, yana mai cewa, wadannan iyalan sun cancanci adalci.

"Gwamnatin Jihar Edo dole ne ta nemi afuwa daga iyalan wadanda aka kashe da kuma daga kungiyar mafarauta ta Najeriya."

Kara karanta wannan

Bayan kisan Hausawa, Gwamna Okpebholo ya dura a Kano, ya gana da Abba Kabir

Gwamnan Edo ya ziyarci jihar Kano

A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi alkawarin biyan diyya ga iyalan mafarauta 16 da wasu ‘yan sa-kai a jiharsa suka hallaka ta hanyar kona su. Rahotanni sun bayyana cewa mafarautan na kan hanyarsu ce daga Fatakwal zuwa Kano domin gudanar da bikin Sallah tare da iyalansu, amma sai 'yan sa kai su ka tare su a Edo.

Wannan al'amari ya tayar da hankulan 'yan Arewa, kuma tuni shugabanni kamar su mataimakin shugaban majalisar dattawa Barau I Jibrin, suka sha alwashin tabbatar da an yi adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.