Wike Ya Fadi Halin da Yake ciki bayan Cewa Ya Yanki Jiki Ya Fadi, An Tafi da Shi Faransa
- Nyesom Wike, ya musanta rade-radin cewa ya yanki jiki ya fadi a gidansa sannan aka garzaya da shi Faransa neman lafiya
- Ministan Abuja ya ce an kirkiri jita jitar domin karkatar da hankulan jama’a daga wasu batutuwa masu muhimmanci a Najeriya
- Wike ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya tare da tabbatar da cewa masu yi masa fatan mutuwa za su riga shi barin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya karyata rahotannin da ke cewa ya yanke jiki ya fadi a Abuja sannan aka tafi da shi Faransa don samun kulawar likitoci.
Wike, wanda ya bayyana hakan a yayin duba wasu ayyukan gine-gine da ke gudana a Abuja, ya ce labarin rashin lafiyarsa karya ce kawai da aka kirkira domin jawo rudani.

Kara karanta wannan
'Mun sha azaba': Janar Tsiga ya magantu, ya fadi dabbobin da suke kwana tare da su

Asali: Facebook
Rahoton Arise News ya nuna cewa Wike ya ce yana cikin koshin lafiya kuma ba shi da wata matsala ta rashin lafiya da za ta sa a garzaya da shi asibiti ko kuma a fitar da shi zuwa wata kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutuwa na kan kowa inji Nyesom Wike
Da yake karin bayani kan batun, Wike ya ce mutane su daina yi wa ‘yan uwansu fata mara kyau, domin babu wanda zai zauna a duniya har abada.
“Duniya ba madauwama ba ce, amma Allah ne kadai ke sanin ranar da kowane mutum zai mutu. Ba wani mutum da zai ce yau ne ko gobe,”
- Nyesom Wike
Punch ta wallafa cewa Wike ya kara da cewa yana cikin koshin lafiya fiye da wasu daga cikin wadanda suka yada wannan jita-jita, yana mai cewa:
“Kamar yadda kuke gani, na ma fi wasu daga cikinsu lafiya. Kuma zan halarci jana'izarsu,”

Kara karanta wannan
Mutane sun mutu da wasu jirage suka gamu da hatsari ana cikin shagalin sallah a Najeriya
Wike: Ana son rudar mutane kan mutuwa ta
Ministan ya yi zargin cewa an kirkiri jita-jitar ne domin karkatar da hankalin jama’a daga wani bayani da tsohon shugaban ma’aikatan jihar Ribas ya yi.
Tsohon shugaban ma'aikatan ya ce an tada bama-bamai a ginin Majalisar Dokokin Jihar Ribas da kuma hare-hare kan kadarorin gwamnati a lokacin Simi Fubara.
“An kirkiri labarin rashin lafiya ta ne don kawar da hankali daga wannan batu.
"Sun yada jita-jitar cewa an tafi da ni kasashen waje neman lafiya, amma babu wani lokaci da hakan ta faru,”
Ya ce duk wanda ke bin labarai zai tabbatar da cewa a kwanakin baya ya halarci bukukuwan Sallah tare da shugaba Bola Tinubu da kuma wasu manyan mutane a Abuja.
'Jita-jita ba za ta hana mu aiki ba,' - Wike
Wike ya bayyana cewa yana da cikakken kwarin gwiwa a kan aikin da yake yi, kuma ba zai bar wadannan jita-jita su hana shi mayar da hankali kan ayyukansa ba.
A cewarsa:
“Mun saba da irin wadannan sharrin siyasa, kuma ba za su hana mu yin aikin da aka dauke mu yi ba. Mun san cewa akwai mutanen da ba sa kaunarmu, amma ba abin da za su iya yi,”

Asali: Twitter
Bala Lau ya yi ta'aziyyar Dutsen Tanshi
A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci a jihar Bauchi, Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi ya rasu.
Mutane da dama a ciki har da manyan malamai a Najeriya sun fara ta'aziyyar rasuwar malamain saboda gudumawar da ya bayar.
Shugaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya mika sakon ta'aziyya ga dalibai da iyalan Sheikh Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng