Abubuwan da Idris Dutsen Tanshi Ya Fada kan Rashin Lafiya da Mutuwa kafin ya Cika
- Sheikh Idris Abdulaziz ya bayyana cewa rashin lafiyarsa ko komawarsa ga Mahalicci ba zai hana ci gaba da yada da’awar gaskiya ba
- Dutsen Tanshi ya ƙara da tunatar da jama'a cewa dukkanin ɗan Adam zai koma ga Allah Sarki (SWT), domin babu wanda zai dawwama
- Malamin ya nanata cewa ba zai taɓa koyar da ƙarya ba, ko ya goyi bayanta, ko ya yada ta, ko kuma ya faɗe ta da gangan ga al'ummar Musulmi ba
- Ya amince cewa ɗan Adam mai kuskure ne, amma kuskurensa ba yana nufin yana yada ƙarya ba ne, sai dai saboda rauninsa irin na ɗan Adam
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Bauchi – Fitaccen malamin addinin Musulunci, wanda ya rasu a daren Juma’a, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, ya taba magana kan masu yada jita-jita game da rashin lafiyarsa kafin rasuwarsa.
Ya bayyana cewa rashin lafiyarsa, ko ma komawarsa ga Mahalicci, ba zai hana ci gaba da yaduwar da’awa ta gaskiya da tunatar da al’umma abubuwan da addini ya yi umarni da su ba.

Asali: Facebook
A wani bidiyo da Sani Abdullahi Mu’az ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Dutsen Tanshi ya dauki alkawari cewa ba zai taɓa koyar da karya ko yada abin da Allah ya hana ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kowa zai koma ga Mahalicci" Dutsen Tanshi
Marigayi Sheikh Dutsen Tanshi ya yi gargadi ga masu murna da jinyarsa a lokacin da ba shi da lafiya, inda ya bayyana cewa babu wata halitta da za ta dawwama a doron ƙasa.
Ya ce:
"Amma don motar gawa ta wuce kai dariya, to gobe kai za a ɗauka, ko ba ka gane ba ne? Kar ka yi farin ciki da rashin lafiyar Idrisu. Manzon Allah (SAW) ya yi rashin lafiya, ya kuma rasu. Ko ba haka ba ne? To wa zai yi saura?"
"Mun zo zama ne? Wallahi ba wanda ya zo zama. Lokaci kawai ake jira. Kowa idan lokacinsa ya yi, zai tafi."
Dutsen Tanshi: "Dan Adam mai kuskure ne"
A cikin daya daga cikin karatunsa, Sheikh Dutsen Tanshi ya bayyana yakinin cewa za a ci gaba da da’awar gaskiya har bayan rasuwarsa, kuma masu karɓar gaskiya za su ci gaba da karɓarta.

Asali: Facebook
Ya jaddada cewa:
"Mun ɗauki alkawarin cewa za mu gaya wa mutum gaskiya, ko waye kuwa — tsakaninmu da mutum gaskiya. Kuma duk abin da zai fito daga bakina, wallahi iya imani na, gaskiya ne."
"Idan kuma an samu kuskure, dan Adam dai mai kuskure ne. Amma ni ba zan ganganta yin karya ba, ba zan ganganta faɗin karya ba, ba zan ganganta goyon bayan karya ba."
Ya ƙara da cewa:
"Dama dan Adam mai rauni ne. Saboda haka, idan ya yi kuskure, wannan ba yana nufin yana da niyyar faɗin karya ba ne."

Kara karanta wannan
'Yadda watsi da shirin Sardauna ke jawo asarar rayukan Hausawa,' Yan kasuwa kan kisan Edo
Abubuwan da Dutsen Tanshi ya ginu a kai
A baya, mun wallafa cewa a daren Alhamis, 3 ga watan Afrilu, Allah ya karɓi rayuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, lamarin da ya girgiza musulmi.
Marigayin ya shahara wajen yaɗa ilimin Tauhidi da wa’azin gaskiya, kuma yana daga cikin malaman da suka kafa tarihi a fagen faɗakar da al’umma ta hanyar karatu da huduba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng