Jerin Shugabannin Kamfanin NNPCL tun daga Kafuwarsa da Jihohinsu
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Bashir Bayo Ojulari a matsayin sabon shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL).
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Bashir Bayo Ojulari ne domin ya maye gurbin Mele Kolo Kyari wanda aka sallama daga muƙaminsa.

Asali: Twitter
Hadimin shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanar da hakan a shafinsa na X.
Mutanen da suka shugabanci NNPCL
Kafin Mele Kyari mutane daban-daban daga sassan Najeriya sun jagoranci kamfanin NNPCL.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune ta yi duba kan cikakken jerin tsofaffin shugabannin kamfanin NNPCL.
Ga jerinsu a nan ƙasa:
1. Cif R.A. Marinho (Yuli 1977 – Afirilu 1980)
An haifi Cif Marinho a ranar 30 ga watan Disamba, 1934, a Ijebu-Ode, jihar Ogun. Ya girma a unguwar "Brazilian Quarters" na tsibirin Legas kuma ya halarci kwalejin St. Gregory, Obalende, Legas.
A lokacin shugabancinsa, an ƙirƙiro da muhimman tsare-tsare a masana'antar man fetur ta Najeriya, inda yawan haƙar mai ya ƙaru daga ganguna 50,000 a kowace rana zuwa sama da ganga miliyan 2.5 lokacin da ya yi ritaya.
2. Odoliyi Lolomari (Afirilu 1980 – Agusta 1981)
An Cif Odoliyi Lolomari a ranar 16 ga watan Disamba, 1933, a garin Abonnema, jihar Rivers.
Cif Lolomari ya riƙe muƙamin shugaban NNPC kuma wakilin Najeriya a hukumar OPEC.
Ya rasu a ranar 1 ga watan Satumba, 2021, yana da shekaru 87.
3. Cif Lawrence Amu (Oktoba 1980 – Nuwamba 1985)
An haifi Cif Lawrence Amu a ranar 23 ga watan Disamba, 1933, a Ojokoro, jihar Legas.
An naɗa shi shugaban NNPC a watan Agusta 1981. Ya rasu yana da shekaru 65 a ranar 26 ga Agusta, 2019.
4. Dr. Aret Adams (Nuwamba 1985 – Afirilu 1990)
An haifi Dr. Aret Adams a ranar 27 ga wataɓ Fabrairu, 1938, a Auchi, jihar Edo.

Kara karanta wannan
"Mutane sun manta": Tinubu ya faɗi aikin da Sheikh Dutsen Tanshi ya yi wa Najeriya
Ya yi aiki da kamfanin Shell-BP daga 1964 zuwa 1974 kafin ya shiga NNOC, wanda daga baya ya zama NNPC.
An naɗa shi a matsayin shugaban kamfanin NNPC a shekarar 1985, kuma ya riƙe mukamin har zuwa 1990.
Ya rasu a ranar 7 ga Agusta, 2002, yana da shekaru 64.
5. Dr. Thomas John (Afirilu 1990 – Yuni 1992)
Dr. Thomas John shi ne mutum na biyar da ya shugabanci NNPC bayan Dr. Aret Adams. Haifaffen jihar Cross Rivers ne.
Ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.
6. Cif Edmund Daukoru (Yuni 1992 – Oktoba 1993)
An haifi Cif Edmund Daukoru a ranar 13 ga watan Oktoba, 1943, a jihar Bayelsa mai arziƙin mai.
Ya fara aiki da kamfanin Shell International Petroleum Company a 1970, inda ya zama babban jami'in bincike kafin daga baya ya zama babban manajan harkokin bincike a Najeriya.
A shekarar 1992, aka naɗa shi shugaban NNPC.
7. Cif Chamberlain Oyibo (Nuwamba 1993 – Agusta 1995)
An haifi Cif Chamberlain Oyibo a shekarar 1941 a jihar Rivers da ke yankin Kudu maso Kudu.
Ya shugabanci kamfanin NNPC na tsawon shekaru biyu kafin ya yi ritaya a shekarar 1995.
8. Alhaji Dalhatu Bayero (Agusta 1995 – Mayu 1999)
An haifi Alhaji Dalhatu Bayero a ranar 16 ga watan Nuwamba, 1922, a jihar Kano. Ya riƙe muƙamin shugaban NNPC daga 1995 zuwa 1999.
Alhaji Dalhatu Bayero ƙani ne ga tsohon Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero.
9. Jackson Gaius-Obaseki (Mayu 1999 – Nuwamba 2003)
Jackson Gaius-Obaseki ɗan asalin jihar Edo ne a yankin Kudu maso Kudu. Ya karanci Geology a jami'ar Ibadan.
Ya fara aiki a NNPC a shekarar 1972, inda ya ci gaba da samun matsayi har aka naɗa shi a matsayin shugaba a shekarar 1999.
10. Funsho Kupolokun (Nuwamba 2003 – Satumba 2007)
An haifi Funsho Kupolokun a shekarar 1947 a jihar Ogun. Ya samu digiri a fannin Injiniya daga jami'ar Legas a 1971.
Daga 1973 zuwa 1974, ya samu horo a kamfanin man fetur na Algeria, inda ya yi aiki a filin hakar mai na Hassa-Messand.
Daga baya, ya fara aiki a NNPC kuma ya riƙe muƙamai daban-daban.
11. Abubakar Lawal Yar’Adua (Satumba 2007 – Janairu 2009)
An haifi Abubakar Lawal Yar'adua a watan Yuli 1949 a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma.
Abubakar Lawal Yar'adua ya shugabanci kamfanin NNPC a lokacin mulkin marigayi Umaru Musa Yar'adua.
A lokacin shugabancinsa, ya jajirce wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.
12. Dr. Mohammed Sanusi Barkindo (Janairu 2009 – Afirilu 2010)

Asali: Getty Images
An haifi Dr. Mohammed Sanusi Barkindo a ranar 20 ga watan Afirilu, 1959, a birnin Yola, jihar Adamawa.
Ya kasance sakatare-janar na hukumar OPEC a 2006. Ya shugabanci NNPC daga 2009 zuwa 2010. Ya rasu a ranar 5 ga watan Yuli, 2022.
13. Alhaji Shehu Ladan (Afirilu 2010 – Mayu 2010)
An haifi Alhaji Shehu Ladan a ranar 21 ga watan Satumba, 1952, a jihar Kaduna.
Shehu Ladan lauya ne kuma ƙwararre a harkokin gudanar da albarkatun man fetur da iskar gas a Kaduna.
Ya rike muƙamin shugaban kamfanin NNPC a shekarar 2010. Ya rasu a ranar 4 ga watan Oktoba, 2011, yana da shekaru 59.
14. Austen Oniwon (Mayu 2010 – Yuni 2012)
An haifi Austen Oniwon wanda ɗan asalin jihar Kogi ne a ranar 1 ga watan Afirilu, 1951.
A shekarar 2012 Goodluck Jonathan ya fatattaki Austen Oniwon wanda ya yi karatu a jami'o'in Oxford Harvard.
15. Andrew Yakubu (Yuni 2012 – Agusta 2014)
An haifi Andrewa Yakubu wanda ɗan asalin Zangon Kataf ne a jihar Kaduna a ranar 10 ga watan Satumba, 1955.
Ya riƙe muƙamin shugaban kamfanin NNPC daga 2012 zuwa 2014, bayan da Shugaba Goodluck Ebele Jonathan ya naɗa shi a shekarar 2012.
16. Dr. Joseph Thlama Dawha (Agusta 2014 – Agusta 2015)
Dr. Joseph Thlama Dawha ɗan asalin garin Biu ne a ihar Borno, a yankin Arewa maso Gabas.
Shugaba Goodluck Jonathan ne ya nada shi a matsayin shugaban kamfanin NNPC daga Agusta 2014 zuwa Agusta 2015.
17. Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu (Agusta 2015 – Yuli 2016)
An haifi Dr. Emmanuel Ibe Kachikwu wanda ɗan asalin jihat Delta ne a ranar 18 ga Disamba, 1956.
Ya rike muƙamin shugaban kamfanin NNPC sannan daga baya aka naɗa shi da ministan harkokin man fetur.
18. Dr. Maikanti Baru (Yuli 2016 – Yuli 2019)
An haife shi a watan Yuli, 1959. Asalinsa ɗan garin Jama’are ne a jihar Bauchi a yankin Arewa maso Gabas, amma ya taso a Jos, jihar Plateau.
Dr. Maikanti Baru shi ne mutum 18 da ya rike muƙamin shugaban kamfanin NNPC.
Ya yi aiki daga watan Yuli 2016 zuwa Yuli 2019. Ya rasu a ranar 29 ga Mayu, 2020, yana da shekaru 61.
19. Mele Kolo Kyari (Yuli 2019 – Afirilu 2025)

Asali: Facebook
Mele Kyari asalinsa ɗan birnin Maiduguri ne a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.
Shi ne shugaban NNPC na farko bayan an canza shi zuwa kamfani mai zaman kansa wato NNPCL.
20. Bayo Ojulari (Afirilu 2025 – yau )

Asali: Facebook
Bayo Ojulari haifaffen jihar Kwara ne a yankin Arewa ta Tsakiya.
Kafin naɗinsa a 2025, Ojulari tsohon babban jami’i ne a kamfanin Shell kafin ya zama shugaban kamfanin NNPCL.
Dalilin Tinubu na korar Mele Kyari a NNPCL
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu jami'ai a fadar shugaban ƙasa sun bayyana dalilin sauke Mele Kyari daga shugabancin kamfanin NNPCL.
Jami'an sun bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ɗauki matakin ne domin yana son sababbin jini su jagoranci kamfanin.
Sun nuna cewa wasu daga cikin shugabannin na NNPCL sun fara zama ɓangaren matsalar da ake son warwarewa maimakon su zama mafita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng